Ga mazaje masu kyautar ’yan wuta
Editan Aminiya, ka ba ni dama in mika sakona ga mazaje masu kyautar ’yan wuta ga budurwarsu. A gaskiya lamarin wasu maza na da ban mamaki, musamman ga mazaje da suke wa mata kyauta a lokacin da suke son junan su, daga baya kuma idan wata matsala ta shiga tsakaninsu, sai su rufe idanunsu su […]
Editan Aminiya, ka ba ni dama in mika sakona ga mazaje masu kyautar ’yan wuta ga budurwarsu. A gaskiya lamarin wasu maza na da ban mamaki, musamman ga mazaje da suke wa mata kyauta a lokacin da suke son junan su, daga baya kuma idan wata matsala ta shiga tsakaninsu, sai su rufe idanunsu su ce sai an biya su, duk abin da suka bai wa budurwar. Ina kira ga masu irin wannan dabi’ar da su yi kokari su daina. Idan ka ga ba za ka dauki kyauta ka bai wa budurwa don Allah ba, kuma don soyayyar da ke tsakanin ku ba, a ganina ka huta da kyautar. Ko kuma ku yi yarjejeniya akan idan wata matsala ta shiga tsakaninku za ta biya ka. Daga Sayyada Fatima 08133751208.
Ga Sarkin Minna Bahago
Assalamu alaikum. Edita don Alllah ka ba ni dama in mika sakon taya murna ga sarkinmu mai adalci, Alhaji Dokta Umar Faruk Bahago, kan cikarsa shekara 25 a karagar mulkin Minna. Allah Ya ja zamanin sarki. Daga Maman Innawuro, Tunga Minna 07030891275.