Ga mujirimai (2)
Daga cikin alamomin mujirimai akwai bijire wa addinin Allah, ba su koyonsa kuma ba su aiki da shi. “Kuma wane ne ya fi zalunci bisa ga wanda aka tunatar da ayoyin Ubangijinsa, sa’annan ya bijire daga barinsu? Lallai Mu Masu yin azabar ramuwa ne ga masu laifi (mujirimai).” (As-Sajadah:22). Kuma daga alamomin mujirimai akwai cewa […]
Daga cikin alamomin mujirimai akwai bijire wa addinin Allah, ba su koyonsa kuma ba su aiki da shi. “Kuma wane ne ya fi zalunci bisa ga wanda aka tunatar da ayoyin Ubangijinsa, sa’annan ya bijire daga barinsu? Lallai Mu Masu yin azabar ramuwa ne ga masu laifi (mujirimai).” (As-Sajadah:22).
Kuma daga alamomin mujirimai akwai cewa lallai su suna batar da mabiyansu, sukan bi duk hanyar da ta saukaka domin batar da mutane da kawar da su daga hanyar gaskiya. Sai batattun sun zo Ranar kiyama suna jingina bacewarsu zuwa ga mujiriman. Alkur’ani ya nuna mana halin ’yan wuta bayan an kikkifa su a cikinta alhali suna husuma a cikinta suna furuci kan bacewarsu: “Rantsuwa da Allah! Lallai ne mun kasance hakika a cikin bata bayyananniya. A lokacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu. Kuma babu abin da ya batar da mu face mujirimai. Saboda haka ba mu da wandansu maceta. Kuma ba mu da aboki, masoyi.” (As-Shu’ara: 97-101).
Huduba ta Biyu:
Amma karshen mujirimai a duniya su jira kamun Allah gare su, saboda fadinSa Madaukaki: “Lallai Mu Masu yin azabar ramuwa ne ga masu laifi (mujirimai).” (As-Sajadah:22).
Akwai waki’o’in da suka faru da suke mana nuni kan faduwar mujirimai da makomarsu da ukubar Allah gare su a nan gidan duniya. Amma sakamakonsu a Lahira yana daga cikin jinsin aiki. Sai Allah Ya yi wa mujirimai irin mu’amalar da suka yi ga mutane a duniya ta hanyar hana su zaman lafiya. “Kuma a ranar da Sa’a ke tsayuwa, mujirimai na rantsuwa ba su zauna (a duniya) ba, face awa daya.” (Ar-Rum:55). Saboda dadin mujirimancinsu ya tafi, sai ya zamo duniya dadai a wurinsu ba ta kasance ba, face awa daya a cikin yini. Kaiton awar mujirimi da dagawarsa ina ma zai fahimci haka. Da sannu zai mance girman kai da girman mukami da daukakar da yake jin yana da su, zai ga rayuwa gaba daya ba ta zamo ba face awa daya, kamar ni’imar duniya ba ta taba samuwa gare shi ba, kuma bai gan ta ba!
Sa’annan za a tashi mujirimai Ranar kiyama suna masu jin kishin ruwa. “Kuma Muna kora mujirimai zuwa Jahannama gargadawa.” (Maryam:86). Wato suna masu jin kishin ruwa, kaskanci da rashin girma za su same su. Shin ina girma da jabbaranci da mutakabbirancinsu suke? “Kuma kana ga mujirimai a ranar nan suna wadanda aka yi wa cirri daidai a cikin maruruwa. Rigunansu daga farar wuta ne, kuma wuta ta rufe fuskokinsu.” (Ibrahim:49). Kuma “A ranar da Sa’a ke tsayuwa mujirimai za su kasa magana.” (Ar-Rum:12). Ma’ana za su cire tsammani daga rahamar Allah da ni’imarSa kamar yadda suka hana su ga muminai. Kuma Allah Ya sake cewa: “A ranar da Sa’a ke tsayuwa a ranar mutane ke rarraba.” (Ar-Rum:14).
Kuma za a iya gane mujirimai da alamominsu: “Za a iya sanin mujirimai da alamarsu, saboda haka sai a kama kwarkwadarsu da sawayensu.” (Ar-Rahman: 41). Zabaniyarwa azaba za su kama gashin keyarsu da sawayensu su kakkarya kasusuwan gadon bayansu su jefa su a cikin wuta. “A ranar da ake hurawa a cikin kaho, kuma Muna tara mujirimai a ranar nan, suna masu jajayen idanu. Suna boye magana a tsakaninsu, (suna ce wa juna) “Ba ku zauna ba a (cikin duniya) face kwana goma. Mu ne mafi sani ga abin da suke fada a sa’ad da mafificinsu ga hanya ke cewa, “Ba ku zauna ba face yini guda.” (daha:102-104).
Za ka ga firgitarsu da tsoronsu a Ranar kiyama lokacin da suka ga littafinsu yana dauke da mujirimancinsu. “Kuma aka aza littafin ayyuka, sai ka ga mujirimai suna masu jin tsoro daga abin da ke cikinsa, kuma suna cewa, “Kaitonmu! Me ya samu wannan littafi, ba ya barin karama kuma ba ya barin babba face ya kididdige ta?” (Kahfi:49).
Kunya za ta kama su rika sunkuyar da kawunansu Ranar kiyama: “Kuma da ka gani a lokacin da masu laifi suke masu sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, “Ya Ubangijinmu! Mun gani kuma mun ji, to, Ka mayar da mu (duniya) mu aikata aiki na kwarai. Lallai mu masu yakini ne.” (As-Sajadah:12).
Kuma za a tabbatar wa mujirimai laifuffukansu, suna ganin an rubuta mujirimnacinsu a cikin littafinsu, sai su yi kokarin neman fansa daga azaba da duk abin da suka mallaka, sai su gabatar da mafi girman abin da suka mallaka domin fansar kawunansu: “Mujirimi na gurin da zai iya yin fansa, da azabar ranar na da ’ya’yansa. Da matarsa da dan uwansa. Da danginsa, masu tattara shi. Da wanda ke cikin duniya duka gaba daya, sa’an nan fansar ta tserar da shi.” (Ma’arij: 11-14).
Kuma ba za a karbi hakan daga gare su ba, kuma zabaniyoyin azaba za su kifa fuskokinsu su ja su a cikin Jahannama: “Lallai ne mujirimai suna cikin bata da hauka. Ranar da za a ja su a cikin wuta a kan fuskokinsu. “Ku dandani shafar wuta.” (kamar: 47- 48). Mazauninsunna karshe zai kasance a cikin wutar Jahannama: “Lallai mujirimai madawwama ne a cikin azabar Jahannama. Ba a saukakar da ita (azabar) daga gare su, alhali kuwa su a cikinta masu kasa magana ne. Kuma ba mu zalunce su ba, amma su ne suka kasance azzalumai. Kuma suka yi kira, “Ya Maliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana (mu huta da azaba. Maliku) ya ce: “Lallai ku mazauna ne. Lallai ne, hakika, Mun je muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku masu ki ga gaskiyar ne.” (Zukhruf: 74-78).
Ku yi salati – Allah Ya yi muku rahma – a bisa Annabin Rahma, ni’ima marar yankewa Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wa sallam). Ya Allah Ka kara tsira a bisa Annabi Muhammad da iyalan Annabi Muhammad, kamar yadda Ka yi tsira a bisa Annabi Ibrahim da iyalan Annabi Ibrahim, Lallai ne Kai ne Abin godewa Mai grima. Ka yi aminci a bisa Annabi Muhammad da iyalan Annabi Muhammad kamar yadda Ka yi aminci a bisa Annabi Ibrahim da iyalan Annabi Ibrahim. Lallai ne Kai ne Abin godewa Mai girma.