Ga wasu dalilan da suka sa aka dage zaben gobe Asabar
Kamar yadda aka tsara, da a ce ba a dage ranar zabe ba, da idan Allah Ya kai mu gobe Asabar, 14 ga watan nan na Fabrairu za a gudanar da zaben Shugaban kasa da na Majalisun Tarayya. Sai dai abin ba haka zai kasance ba, domin kuwa Shugaban Hukumar Zabe (INEC), Farfesa Attahiru Jega […]
Kamar yadda aka tsara, da a ce ba a dage ranar zabe ba, da idan Allah Ya kai mu gobe Asabar, 14 ga watan nan na Fabrairu za a gudanar da zaben Shugaban kasa da na Majalisun Tarayya. Sai dai abin ba haka zai kasance ba, domin kuwa Shugaban Hukumar Zabe (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya shiga kafafen watsa labarai, ya sanar da cewa lallai hukumar tasa ba za ta iya gudanar da shi ba kamar yadda aka tsara, saboda wai hukumomin tsaro sun ce ba za su iya bayar da tsaro ga al’ummar kasa ba a wannan rana. Abin tambaya, anya kuwa wannan shi ne dalili na gaskiya da ya sanya aka dauki wannan gurgun mataki?
Koma dai ba wannan ne dalili na kashin gaskiya ba, hukuma dai abin da ta ce ke nan. Hukumomin tsaro sun ce akwai barazana mai karfi daga ’yan kungiyar Boko Haram, don haka a ranar da za a gudanar da zabe ma, za su zafafa kai masu hare-hare, domin ganin an magance matsalarsu gaba daya. Hatta bayan dage zaben, an jiwo mai ba Shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro, Kanar Sambo Dasuki ya fito ya shelanta wa duniya cewa za su magance matsalar Boko Haram nan da makonni shida, wanda haka zai ba da cikakkar damar gudanar da zabubbuka cikin sauki.
Shin anya kuwa wannan dalili zai karbu ga al’umar kasa, wadanda sun dade da shiryawa domin kada kuri’insu? Wasu da dama sun shirya iyalansa, sun kashe kudi sun tafi garuruwansu na asali, domin kada kuri’unsu. Haka ma, kafin dage zaben, Attahiru Jega ya fito ya sanar da cewa sun shirya tsaf, domin gudanar da zaben. Hatta Ministan Al’amuran kasashen Waje na Amurka, John Kerry, da ya ziyarci Njeriya kwanakin baya, Shugaban kasa da kansa ya shaida masa cewa lallai za a gudanar da zaben kamar yadda aka shirya. Wadannan dalili ke tabbatar da cewa akwai wasu boyayyun dalilai da suka sanya aka dage zaben. Idan haka ne, wadanne dalilai ne da suka bambanta da wanda gwamnati ta bayar, da suka sanya aka dage zabe? Bari mu duba tare da lalabawa mu gani, ko za mu iya samar da wasu dalilan.
Wani babban dalili da ake ganin cewa shi ya haddasa aka dage zaben, shi ne yadda jam’iyyar da ke kan mulki ta shiga firgici a sakamakon yadda ta ga mutane sun kaurace mata. Jam’iyyar ta yi tsoron za ta fadi zabe, wanda dalili ke nan ya sanya suka nemi a dage zaben domin su sake shiri. Biri ya yi kama da mutum, domin kuwa ko a lokacin da jam’iyya mai mulki ke yawon yakin neman zabe, kusan duk jihar da suka je ba su samu goyon bayan mutane da yawa. Hasali ma, wasu jihohin, inda jam’iyyar ce ke mulki, har ihu ake masu, tare da jifa, kamar jihohin Katsina da Bauchi. Ba haka ba ma, hatta Jihar Bayelsa, mahaifar Shugaban kasa, an samu rahoton da ke nuna yadda al’ummarsa suka yi masa bore, a lokacin da ya daga hannun dan takararsu na gwamnan jihar.
Wani dalili da ya sanya aka dage zaben nan, kamar yadda wata majiya kwakkwara ta sanar da ni, yana da nasaba da kulumboto da camfi. Ma’ana, jam’iyya mai mulki wai ta camfa ranar 14-Fabrairu-2015 saboda wani boka ya gaya masu cewa, madamar aka yi zabe a wannan rana, to akwai yiwuwar a kada gwamnatin da ke kan mulki, saboda rana ce da taurarin sa’a suka dace da taurarin Janar Muhammad Buhari.
A lokacin da bokan nan yake bayyana masu dalla-dalla na wannan kulumboto, ya ce haruffan da suka rubuta sunan ‘Muhammadu Buhari’ guda 14 ne, wannan na nufin ranar 14 ga wata (1-M, 2-U, 3-H, 4-A, 5-M, 6-M, 7-A, 8-D, 9-B, 10-U, 11-H, 12-A, 13-R, 14-I). Haka kuma, watan Fabrairu, shi ne wata na biyu a shekara, wannan na nufin idan Buhari ya ci zabe, zai hau karagar mulki sau biyu ke nan, domin kuwa ya taba yi a 1984 zuwa 1985. Haka kuma, bokan ya nuna masu cewa, kamar yadda yake a tsarinsu, ranar 14 ga watan Fabrairu, rana ce ta masoya, rana ce ta nuna kauna. Don haka, irin yadda Buhari ke da masoya da yawa a Najeriya, za su iya nuna masa kauna a wannan rana ta 14 ga wata, su zabe shi a matsayin Shugaban kasa. Ya kuma kara nuna cewa, a tsarin shugabannin da suka mulki Najeriya, Jonathan ne shugaba na 14 (1-balewa, 2-Ironsi, 3-Gowon 4-Murtala 5-Obasanjo, 6-Shagari, 7-Buhari 8-Babangida, 9-Shonekan 10-Abacha, 11-Abdulsalam, 12-Obasanjo, 13-Umaru, 14-Jonathan), don haka, ga shi kuma ana cikin shekara ta 2015. Bokan ya ce idan aka sake aka yi zaben a wannan rana, to, 15 na nufin, Jonathan zai kare mulkinsa a matsayin Shugaban kasar Najeriya na 14; sabon shugaba na 15 zai hau. Wannan dalili ne ya sa wai bokan ya ce a zakuda da ranar zaben, domin kauce wa wannan camfi.
Wani dalili kuma da ya sanya aka dage zaben shi ne, akwai wasu Janar-Janar da hamshakan sojoji masu ci a yanzu da wadanda suka bar mulki da ba su son ganin cewa Janar Buhari ya hau mulkin Najeriya. Majiya ta sanar da ni cewa irin wadannan sojoji da wasu hamshakan ’yan kasuwa da wasu manyan ma’aikatan gwamnati da suka yi wandaka da dukiyar kasa, su ne ba su son ganin Janar Buhari ya dare mulki, saboda zai taka musu burki, zai hana satar dukiyar kasa, zai hana almundahana da babakere. Wasu ma na ganin cewa zai kama su ya kulle ne, musamman ma wasu tsofaffin sojoji da suka yi masa juyin mulki, suka kulle shi. An ce suna tunanin har gobe Janar Buhari na kullace da yadda aka garkame shi a jarun tsawon shekaru biyu, aka hana shi ganawa da iyalinsa, mahaifiyarsa na gargarar mutuwa, ya nemi a bar shi ya gana da ita, amma aka hana har ta mutu. Sannan kuma yana kullace da yadda aka shiga gidansa aka yi masa kaca-kaca da kayansa, aka dauke masa muhimman takardu da sauransu. Irin wadannan sojoji, suna tsoron idan ya hau mulki, zai yi masu ramuwar gayya, wacce ta fi gayya ciwo. Shi ya sanya a yanzu da suke da dama, suke yin kutu-kutun kada ya kai ga mulki.
Ko hakarsu za ta cin ma ruwa? Lokaci ne kadai zai nuna, domin kuwa an sanya 28 ga watan Maris da 11 ga watan Afirilun bana a matsayin sababbin ranakun zabe.
Allah dai muke roko Ya zaba mana shugbanni nakwarai, masu kaunar talakawa, Ya kawo mana lafiya da zaman lafiya a kasarmu da al’umma baki daya!