Gaba ke haifar da banga a siyasar Arewa – dansudu

Alhaji Ado Shu’abu  dansudu, Shugaban kungiyar Hadin kan Mutanen Arewa ( Arewa United Consultatibe Forum), kuma mataimakin shugaban kungiyar ci gaban matasa ta kasa, kana  mai fashin baki ne siyasar Najeriya, ya shaida wa Aminiya alfanun siyasar ubangida da sababin bangar siyasa da illolinta. Aminiya: Yawancin mutane kan soki Salon tsarin siyasar ubangida ko ya […]

Gaba ke haifar da banga a siyasar Arewa – dansudu
Gaba ke haifar da banga a siyasar Arewa – dansudu

Alhaji Ado Shu’abu  dansudu, Shugaban kungiyar Hadin kan Mutanen Arewa ( Arewa United Consultatibe Forum), kuma mataimakin shugaban kungiyar ci gaban matasa ta kasa, kana  mai fashin baki ne siyasar Najeriya, ya shaida wa Aminiya alfanun siyasar ubangida da sababin bangar siyasa da illolinta.

Aminiya: Yawancin mutane kan soki Salon tsarin siyasar ubangida ko ya abin yake ne?
Ado dansudu: Siyasar ubangida ta dogara ne da hallarcin da kuma jajircewar ubangidan, idan ubangidan nagari to tsarin siyasa ce mafi  kyau da amfani, saboda shi ubangidan za ka ga idan mutumin kirki ne yana da jama’a da yawa a karkashinsa kuma kokarinsa ya ga ana tafiya da kowa a siyasance, za ka ga mafi akasarin mutanen da ke amfana da siyasar ubangida ba ‘ya’yan wane da wane ba ne; ba kuma kowa ne yasan da zaman su ba, cancantar su  ce take sa shi ubangidansu ya tsaya musu, ya fito da su har su samu karbuwa, su kuma yi wa jama’a  aiki.  Alal misali in ka dubi irin salon siyasa a nan Kudu maso Yamma za ka ga irin ta ce Ahmad Bola Tinunbu ja-gaban Bargu yake yi in ka lura za ka ga shi ya dauko tsohon Gwamnan Legas Fashola, ya fito da shi tun ba wanda yasan shi, domin shi yasan gogagge ne; kuma ya cancanta.Kuma ya taka rawar gani.  
Sannan haka ta kasance a karo na biyu in ka lura shi ma gwamnan mai ci  yanzu cancantarsa ce ta sa Ahmad Bola Tinunbu ya fito da shi. Domin manyan ’yan siyasa ne kawai suka san da zamansa. Sha’awar Bola Tinunbu ne a matsayinsa na ubangida, kuma shugaba shi ne ya jajirce don ganin kowane bangare na Kudu maso Yamma an dama da shi a siyasance, ba wai a bar  mutum guda yayi ta mulki kamar  tsarin sarautar gargajiya.  In ka lura wasu sassan Arewacin kasar nan Gabas da Yamma da Arewa ta tsakiya za ka ga wani tun da aka kafa siyasar yana nan akan mukami ya ki ya sauka ya ba wani ya dana, bayan kuwa akwai wadanda suka fi shi cancanta,  amma saboda tsarin siyarsar kudi kuma yana da su ya kankame ko’ina shi kadai.  Amma a nan Kudu maso Yamma karkashin Bola Tinunbu  ba wani dan majalisar dattawa ko na wakilai da ya yi fiye da sau daya ko sau biyu; da ka yi na biyu za a ce ka ba wani shi ma ya gwada tasa bajintar.  
Haka ya dinga kewayawa ba wai sai dan wane da wane ba: A’a cancanta ake dubawa kawai .  Haka ma babu wani gwamna a karkashin tafiyar Bola Tinunbu  da ya zama sanata, ka yi gwamna sannan ka zo ka yi sanata, ai ba kai kadai ne ba; kuma ba wani sanata da ya taba zama gwamna ko mataimakin gwamna da ya zama gwamna sai dai wani ya yi. To ka ga tsari ne da zai ba kowa hakkinsa, kuma a dama da kowa, ba sai wane da wane ba. Ya kamata mu ma a Arewa mu yi koyi da wannan, domin haka ban ga dalilin sukar salon siyasar ubangida ba, saboda tsarin siyasa ne da ba zai bar mutum daya ya yi ta yi tamkar gado ba.
Aminiya: Kana nufin sauran sassan kasar nan su yi koyi da irin salon siyasar Kudu maso Yammaci ke nan?
Ado dansudu: kwarai kuwa! Domin wannan kyakkyawan tsari ne da ya kamata mu ma a Arewa mu yi koyi, kuma kamata ya yi mu yaba wa shi Ahmad Bola Tinunbu; mu kuma jinjina masa bisa gwagwarmayar da ya yi na tabbatar sauyi a kasar nan. Domin kuwa yana cikin wadanda suka zage damtse, har mulki ya koma Arewa. Don haka wajibi ne duk  wani dan jami’iyyar  APC ya yi masa  biyyaya, ya kuma bi jami’iyya sau da kafa.
Aminiya:  Me kake ganin yana kawo matsalar bangar siyasa a Arewacin kasar nan?
Ado dansudu: A Arewa wadansu kafafen yada labarai, musanman gidajen rediyo suke ingiza bangar siyasa, a inda za ka ga mutum ya zo ya sayi fili yana fada wa wani maganganu da zage-zage sai ka ga shi ma wancan ya zo ya  maida martini, to hakan ke kawo siyasar gaba. Kuma duk sa’adda wani shugaba ya je ya zagi abokin karawarsa, to kamar ya ce magoya bayansa su yi fada da na wanccan ke nan. Mu a nan da zarar wani ya fada wa wani babba kakkausar magana yanzu ka ga an taka masa burki. ’Yan Arewa ya kamata  mu zama masu da’a da biyayya da girmama na gaba, saboda rikon da addinin da aka san mu da shi, amma akasin haka yake faruwa, sai ka ga wannan ya je gidan rediyo ya zagi wanccan, wanccan ma ya je ya maida martani ai ka ga wannan ya saba wa addinan mu.  A Arewa ne ko da kansila ka tsaya wa mutum ya ci tun ba a je ko’ina ba, sai ka ga ya fara gaba da kai. Da wuya ka ga wani yana tare da ubangidansa  na siyasa,  to ka ga akwai matsala don tafiyar da mulki ba hadin kai ba zai yiwu ba.
Wajibi ne mu dawo daga rakiyar  siyasar gaba, domin ita ke janyo bangar siyasa, ita bangar siyasa ba talaka kawai ke yinta ba, don akwai ‘yan bangar siyasa a kansiloli da shugabanin kananan hukumomi da ‘yan majalisun jihohi da na tarayya, domin duk mutumin da zai kawo matsala ya tayar da hankalin jama’a ya zama dan bangar siyasa. Zage-zage da kazafi da karairayi da cin mutuncin jama’a ba su ne siyasa ba. Wani lokaci na je Sakwato, na ga wani sanata ya taho anyi masa jerin gwanon motoci ga jiniya na tash.
Kai ko da gidan kansila ka wuce za ka ga mutane sun yi dandazo  sun zo maula, amma a nan Kudu sai ka ga sanata ya wuce a motar sa ba ko wanda ya san da shi; kowa ya sa harkokinsa  a gaba ba ruwan kowa da shi. Saboda haka ya kamata mu ma ‘yan Arewa mu yi koyi da wannan.