Gaba ta kare, Dbanj da Don Jazzy sun sasanta

A duniyar mawakan zamani na Kudancin Najeriya, babu wanda ya yi tsammanin Dbanj da Don Jazzy za su kara shan inuwa daya, tun bayan da suka farrake a bara, lokacin da suke gudanar da sana’arsu a kamfani daya mai suna ‘Mo-Hitts Records.’Mawakan biyu, sun bar masoyansu cikin mamaki, inda a makon jiya aka gan su […]

Gaba ta kare, Dbanj da Don Jazzy sun sasanta

Don Jazzy a hagu tare da DBanj suna rera waka tare.A duniyar mawakan zamani na Kudancin Najeriya, babu wanda ya yi tsammanin Dbanj da Don Jazzy za su kara shan inuwa daya, tun bayan da suka farrake a bara, lokacin da suke gudanar da sana’arsu a kamfani daya mai suna ‘Mo-Hitts Records.’
Mawakan biyu, sun bar masoyansu cikin mamaki, inda a makon jiya aka gan su tare suna rera waka, a yayin bikin auren kanwar Dbanj, mai suna Taiwo, wacce aka daura aurenta da Dotun, mai aiki a gidan rediyon Cool FM. An yi shagalin bikin ne a birnin Ikko.
Abin da masoyansu ke tambaya shi ne, shin wannan sasanci da suka yi, zai dore ne ta yadda za su dawo da kamfaninsu na baya ko kuwa dai za su ci gaba da kasancewa masu cin gashin kansu a farrake? Lokaci ne zai nuna haka, domin kuwa babu dayansu da ya amince ya yi wa ’yan jarida karin bayani, bayan da aka kammala bikin.