Gaba tsakanin ’ya’yan PDP ba za ta haifar mata da da mai ido ba a Keffi – Babayo
daya daga cikin ’yan takaran Shugaban Jam’iyyar PDP a karamar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa Alhaji Aliyu Babayo, ya bukaci ’ya’yan jam’iyyar su mance da bambance-bambancen da ke tsakaninsu su hada kai don gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar a karamar hukumar da za a gudanar kwanan nan cikin lumana da kwanciyar hankali. Alhaji Aliyu Babayo […]
daya daga cikin ’yan takaran Shugaban Jam’iyyar PDP a karamar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa Alhaji Aliyu Babayo, ya bukaci ’ya’yan jam’iyyar su mance da bambance-bambancen da ke tsakaninsu su hada kai don gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar a karamar hukumar da za a gudanar kwanan nan cikin lumana da kwanciyar hankali.
Alhaji Aliyu Babayo ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke zantawa da wakilinmu a Keffi, inda ya ce sai hakan ta samu kafin su iya kwato ragamar mulki daga Jam’iyyar APC a karamar hukumar su kuma dawo da martabar jam’iyyar a ciki da wajen jihar.
Ya ce “Ina jan hankalin ’yan uwana da ke neman shugabancin jam’iyyarmu ta PDP a wannan karamar hukuma cewa kada su manta cewa duk da cewa muna neman kujera daya ce, dole ne mu hada kai domin a samu damar gudanar da zaben cikin lumana, saboda ta haka ne kawai za mu dawo da martabar jam’iyyarmu a karamar Hukumar Keffi da jihar nan baki daya sannan mu kwato mulki daga hannun APC.”
Alhaji Aliyu Babayo ya kuma bukaci takwarorinsa ’yan takaran su tabbatar sun tallafa wa duk wanda ya samu nasara a zaben, inda ya ce sauran jam’iyyu sun zuba ido su ga faduwar jam’iyyar.
Kimanin ’yan takara biyar ne suka nuna sha’awarsu ta nema kujerar shugaban jam’iyyar a karamar hukumar.