Gabobin da za ki fesa turare
Mutane da yawa kan kasa tantancen wuraren da ya kamata su rika fesa turare don ya dade, wanda jim kadan bayan sun fesa turare sai a nemi kamshinsa a rasa. Hakan ne ya sa za a ga mutane na yawan fesa turare a-kai-a-kai.A wannan makon na yi miki guzurin wuraren da za ki fesa turare […]
Mutane da yawa kan kasa tantancen wuraren da ya kamata su rika fesa turare don ya dade, wanda jim kadan bayan sun fesa turare sai a nemi kamshinsa a rasa. Hakan ne ya sa za a ga mutane na yawan fesa turare a-kai-a-kai.
A wannan makon na yi miki guzurin wuraren da za ki fesa turare don kamshinsa ya dade.
Akwai wadansu gabobi a jikin mutum da ake kira ‘pulse points’, wadannan gabobi suna da jijiyoyin jini, wanda a lokacin da jini yake zagayawa sukan dauki dumi su kuma fitar da kamshin turaren.
Wadannan gabobi sun hada da: zakaran wuya da wuyan hannu da bayan kunne da cikin gwiwar hannu da kuma kafa. Idan kika fesa turare a wadannan gabobi duminsu zai dumama shi, kamshinsa zai rika tashi.
A yayin fesa turare: Ki rika hankali da idanunki domin zai iya lahanta miki shi. Kada ki fesa a wurin da yake da rauni. Kada ki hadiye shi zai iya cutar da ke.