Gabon: Janar Brice Nguema zai karɓi rantsuwa a Kotun Koli

Ƙungiyar ƙasashen Afirka ta dakatar da Gabon saboda juyin mulki da sojoji suka yi wa Shugaba Ali Bongo

Gabon: Janar Brice Nguema zai karɓi rantsuwa a Kotun Koli

Janar Brice Oligui Nguema Gabon, Kwamandan Rundunar Tsaron Shugaban Kasar Gabon, ya yi wa uban gidansa, Shugaba Ali Bongo Odimba, juyin mulki ranar Laraba, 30 ga Agusta, 2023.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun sanar da shirinsu na ranstar da shugaban mulkin soji a daidai lokacin da Ƙungiyar Gamayyar Ƙasashen Afirka (AU) ta dakatar da ƙasarsu daga cikinta.

Majalisar Tsaron Ƙungiyar AU ta sanar da haka ne a taron gaggawa da majalisar tsaro da harkokin siyasarta ta gudanar ranar Alhamis a kan hamɓararwar da sojoji suka yi wa Shugaba Ali Bongo Odimba.

A ranar masu juyin mulkin sun sanar cewa za a rantsar da Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya jagoranci juyin mulkin a matsayin shugaban ƙasa na riƙon ƙwarya a babbar kotun ƙasar.

Sanarwar sojojin ta ce a ranar Litinin za a rantsar da Janar Brice Oligui Nguema, tare da alkawarin mutunta dukkan nauyin da ya rataya a wuyan gwamnatin ƙasar a cikin gida da ƙetare.

Amma Majalisar Tsaron AU ta ce “Mun dakatar da Gabon daga ɗaukacin harkokin AU, har sai an dawo da halattacciyar gwamnati da kuma kundin tsarin mulkin ƙasar.”

Juyin mulkin Gabon shi ne na farko a yankin Tsakiyar Afirka, a ’yan shekarun nan, kuma ya zo ne sa’o’i kaɗan bayan Shugaba Bongo ya lashe zaɓe domin yin tazarce.

‘Yan adawa na zargin an sanar da Bongo a matsayin wanda ya yi nasara ne tun kafin a kammala ƙidaya ƙuri’u, don haka suka buƙaci sojojin da su ƙarashe ƙirgen ƙuri’un.

Sai dai tun da farko sojojin, ƙarƙashin jagorancin Janar Brice Nguema, sun soke zaɓen sun kuma jingine kundin tsarin mulki tare da soke duk masu riƙe da muƙaman siyasa a ƙasar.

Sojojin rundunar tsaron fadar shugaban ƙasar da suka hamɓarar da Shugaba Bongo sun suka soke zaɓensa mai cike da ruɗani, suka kuma tsare shi da iyalansa.

An kifar da gwamnati a Gabon ne mako biyar daidai bayan sojojin da ke tsaron shugaban ƙasa a Jamhuriyar Nijar sun yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja