Gabza ake ba mu a sansanoninmu — ’Yan gudun hijira

’Yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya kore su daga garuruwansu a sassan Jihar Borno sun koka da irin abincin da suka ce gwamnati tana ba su a matsugunin ’yan gudun hijira a jihar. Mutanen, wandanda suka hada da maza da mata da kuma tsofaffi da kananan yara, sun ce mafi akasarin abincin da […]

Gabza ake ba mu a sansanoninmu — ’Yan gudun hijira
Gabza ake ba mu a sansanoninmu — ’Yan gudun hijira

Yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya kore su daga garuruwansu a sassan Jihar Borno sun koka da irin abincin da suka ce gwamnati tana ba su a matsugunin ’yan gudun hijira a jihar.

Mutanen, wandanda suka hada da maza da mata da kuma tsofaffi da kananan yara, sun ce mafi akasarin abincin da suke ci a sasanonin yana da karancin inganci, domin babu isasshen man girki da kuma sinadaran dadada abinci.
A jihar Borno akwai wurare 22 inda gwamnati ta ajiye ’yan gudun hijiran, wadanda rikicin ya tilasta wa ficewa daga garuruwansu.
Da wakilinmu ya yi tattaki zuwa wasu daga cikin sansanonin da ke cikin garin Maiduguri, ’yan gudun hijirar sun yi matukar korafi a kan yadda ake ciyar da su.
A sansanin da ake kira Bakassi, mutanen sun gaya wa Aminiya cewa ba su cika cin abincin da ake ba su ba, wanda suka ce ya hada da dafa-dukan shinkafa da kunu da kuma tuwo.
Wata ma’aikaciyar karamar Hukumar Mungono, Hajja Waziri, wacce take cikin daruruwan mutanen da ke ajiye a wurin, ta zargi masu kula da su da girka abinci mara dadi.
“Duk da cewa azumi ake yi, kunu kawai ake ba mu a lokacin shan ruwa, sannan shi kansa kunun ba suga a ciki kuma ba dadi; sannan ba ko mahadi, kamar kosai,” inji ta. Matar, wacce ke tare da ’ya’yanta guda bakwai da kuma mijinta, ta kara da cewa: “Mukan karbi kunun ne lokacin da ba mu da kudi ko kuma don mu ba yaranmu. Amma akasarin lokaci, mukan saya mu girka abin da za mu ci ne da kanmu.
“I dan dafa-dukan shinkafa suka dafa, sukan zuba manja kalilan a ciki; wani lokacin ma ba ko gishiri. Babban fatanmu kawai a samu zaman lafiya mu koma gida,” cewar Hajja.
Shi ma wani magidanci, Taju Saleh, wanda ya gudo daga Mungono da matarsa daya da ’yaya uku, ya koka da irin abincin na ’yan gudun hijira a nan Bakassin.
“Abinci ba dadi sannan kuma ba shi da yawa. A wasu lokutan ma ba kowa kan samu ba, sai a ce ya kare. Duk da rashin dadinsa, ya zame min dole in ci ni da iyalina, saboda ba ni da wata hanyar samun kudin shiga. A baya nakan yi sana’ar kabu-kabu ne a Mungono amma yanzu ba halin yin hakan,” inji shi.
Wakilinmu ya hadu da Saleh ne da yamma bayan ya karbo kunun buda-baki da aka raba a sansanin, inda ya yi tsokaci kamar haka dangane da kunun: “Wannan ma yana da dan haske a kan na wasu lokutan da za ka gan shi baki kirin.”
Wadansu da suka karbo kunun sun nuna wa wakilinmu abin da suka ce dawa ce wacce ba ta niku ba a cikinsa sannan kuma sun ce tsalala yake.
Wani ma’aikacin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce akan ba su tuwo da bakar miya mara dadi. “Da yawanmu ba ma cin wannan tuwon saboda ba shi da dadi,” inji shi.
Abacha Zarime shi ma yana zaune a Bakassi. Ya ce ba su taba cin nama ko kifi ba tunda suka shiga sansanin.
Ciyaman din ’yan gudun hijirar na garin Mungono, Alhaji Abacha Baichu, ya tabbatar da korafe-korafe a kan abincin nasu, amma ya alakanta haka da yawan mutane.
“Ka san an ce in dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Abu kadan da za ka dafa a gida ya yi dadi, in aka ce za a ba mutane da yawa ba lallai ne ya yi dadi ko ya ishe su ba,”
Ya ce: “Saboda yawan mutane wurin dafa abincin ma an raba shi har gida tara. Tabbas dadi da yawan abincin ba zai yi kamar na gida ba. Amma mun gode wa Allah tun da ana kawo mana.”
Ya ce sama da mutane 10,000 ke zaune a wurin, wadanda suka hada da ’yan kananan hukumomin Mungono da Guzamala da Nganzai, yana mai cewa karamar Hukumar Mungono kawai tana da sama da kashi uku bisa hudu na adadin.
Alhaji Baichu ya kara da cewa akan samu mutum 40 cikin daki guda a gidajen sansanin.
Da Aminiya ta ziyarci wani sansanin da ke makarantar Ali Mungono Teachers College a washegarin ranar Alhamis ta makon jiya, a cikin birnin Maidugurin, jami’an tsaro ba su bar wakilinmu ya shiga ciki ba saboda jami’in hukumar tallafin gaggawa ta NEMA wanda zai ba da izini a shiga ba ya nan. Sai dai an lura cewa ’yan gudun hijirar da suka hada da ’yan kananan hukumomin Baga da Gamboru Ngala, na fitowa daga sassanin gab da Magariba domin sayen abin buda baki.
Wani dan gudun hijarar mai sana’ar saida turare dan asalin garin Baga, Alhaji Ari Maiturare Baga, ya sanar wa Aminiya cewa ana fama da karancin abinci a cikin sansanin. Mutumin da ya ce yana tare da matarsa da ’ya’ya bakwai a wurin kulawar, ya soki inganci abincin da kuma wadatarsa. “Tun da aka fara azumi, yau kwana tara, ni da iyalina ba mu samu karbar abincin da suke rabawa ba saboda ba ya isa,” inji Alhaji Ari.
Shi ma wani mazaunin wurin daga garin Gamboru Ngala, kokawa ya yi dangane da karancin abincin, yana mai cewa da kyar yakan samu ya karba, shi da matansa biyu da ’ya’ya hudu.
Muhammad Mustafa ya zargi jami’ai da kwauron abincin. “Jiya ma farar shinkafa kawai na samu ba miya. Sai da muka sayo mai na N10 da ya ji na N10 muka zuba a ciki muka ci,” inji shi.
Ya kuma kara da cewa yawanci mazauna sansanin ba su samun abin sa wa a baka ko da sun kai azumi. “Kunun da suke yi ba ya isa.”
A wani sansanin a Dalori, wanda jami’ai suka ce yana dauke da sama da mutum 16,000, mafiya yawan ’yan gudun hijirar sun ce ana ba su abinci isasshe, sai dai wasu tsofaffi a wurin sun koka da cewa ba a sa musu nama ko kifi a, sannan sun ce ana ba su kunu ba mahadi kamar kosai ko alale.
Da Aminiya ta tuntubi shugaban NEMA na sansanin, Bashir Idris Garga, ya ce a wasu lokutan ana ba ’yan gudun hijirar kifi, saboda tsananin yawansu. Ya kuma kara da cewa akan raba musu kunu da kosai, sabanin yadda mutanen suka fada.
Sai dai ya ce tsare-tsaren da hukumar take aiwatarwa da hadin gwiwar takwararta ta jiha (SEMA) za su inganta abubuwan da ake ba ’yan gudun hijirar.
A baya, gwamnatin ta Borno ta ce tana kashe Naira miliyan 600 a duk wata domin ciyar da ’yan gudun hijarar jihar.
A ranar Asabar da ta gabata ce Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima, ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya ta karbe kuluwa da ’yan gudun hijirar jihar.
Gwamnan, wanda ya yi magana ta bakin mai ba shi shawara ta musamman a harkar watsa labarai, Malam Isa Gusau, ya ce sabon tsarin ya fara ne makonni kalilan bayan sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi mulki.