Gada-gadar gudun gada

Masu karakaina da sagaraftu a tituna kasar Haurobiya, musamman masu jele a babban falalen titin Harubja zuwa birnin Dabo, sun sha cin karo da masu walagigi da watangaririyar gada-gadar gudun gada. Ba wasu ba ne ke ranta a na kolo illa masu jan linzamin ababen hawa, musamman ’yan kungiyar NATUWO, wato masu laluben na-tuwo da […]

Gada-gadar gudun gada
Gada-gadar gudun gada

Masu karakaina da sagaraftu a tituna kasar Haurobiya, musamman masu jele a babban falalen titin Harubja zuwa birnin Dabo, sun sha cin karo da masu walagigi da watangaririyar gada-gadar gudun gada. Ba wasu ba ne ke ranta a na kolo illa masu jan linzamin ababen hawa, musamman ’yan kungiyar NATUWO, wato masu laluben na-tuwo da na-koko a jikin kurkurido da shorido-shorido. Ayyukan da masu jan linzamina babewn hawa ke tsuwurwurtawa sau tari da dama sukan haifar asarar rayukan al’umma da dukiyoyi, al’amuran da suka ta’azzara a ‘’yan kwanakin nan.
Al’amarin masu gada-gadar gudun gada bai taba dugunzuma ni ba, kamar ranar da muka ci karo da dankwara, wanda ya yi wa kurkuridon mu shan kai a kan gadar farko ta shiga birnin Lawurje. Karon battar mu da dankwara a birnin Lawurje ta sanya kurkuridon mu kirar bagobirar motoci ta kuje, har ta kai ga ’yar kurkurar dankwara ta zaftare mana kwalliyar gaba. Wannan lamari na aukuwa, sai akwai wani bakanike ya rankayo da gudu, inda ya dan yi mana ’yan gyare-gyare, sannan ya bukaci mu shiga cikin farfafjiyar gyaran ababen hawa da ke gaban gadar shiga birnin Lawurje. Wannan lamari dai ya auku ne a farkon watan Farin-birin, amma ba zan iya fasko hakikanin ranar ba. Kuma Malam Ahmadu ga Masallaci da Nagujungu (ba mai shanyin ’yan gayu ba) na Kamfanin buga amintattun jaridun kasar Haurobiya su ne shaidata.
Muna shiga farfajiyar kanikawa, sai jami’in kanikanci ya yanke mana makudan Hauron da za a kasha wajen sayen kayan gyara da lika su a jikin Bagobirar motoci. Ni kuwa da jin wannan batu sai na bijiro da shawarar cewa, tunda dankwara ne musababbin wannan hadari, lallai ya kamata nya biya kudin gyara tun kafin mu kirawo mai taku da kulki hular dakon giwa bugu da kari. Shi kuwa gogan naku (dankwara) sai ya ce ai ko karfanfana ba shi da ita. Da jin ya furta wadannn kalamai, sai na lallaba na wafce takardun kurkuridon sa, inda muka yi ta cacar baki, har dai masu hankali a kwanyarsu suka yi mana masalaha, inda aka yanke cewa, ya biya rabin kudin gyara mu ma mai jan linzamin kurkuridon mu ya biya rabi. Don haka muka rankaya zuwa birnin Dabo, inda aka karkare wannan batu.
’Yan makaranta, masu koyon wtsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, ya kamata ku fasko cewa,Hanr mota kwazazzabai, jami’an tsaro na karbar ’yan kwabbbai; jiga-jigan jan jama’a a jibga-jibgan ababen hawa na gudun wuce sa’a, tamkar gada (dabba) a cikin daji.’ Kuma akwai ma gadojin da ba su da makarai, ta yadda idan mutum bai yi sa’a ba, kurkuridon san a iya yin alkafura cikin koramar karkashin gada. Wasu ababen hawa kuwa, musamman manya da kananan gwajin kwanji suke yi, tamkar dai karo da karo sai rago, ta yadda idan aka yi taho-mu-gama mai jan linzamikan salwantar ko ya kassara rayuwar dimbin mutane da lodin kayan su.
Kuma wani abin takaicin shi ne, wanda duk ya yi dare a kan babbban falalen titin Haurubja zuwa birnin Dabo, da zarar ya bar kwaryar masarautar birnin Lawurje, tabbas akan smau iyalan Da’u fataken talatainin dare, wadanda ke kassara rayuwar al’umma su kwace musu kayan su. Hasalima wadannan miyagu an san matsugunnin su, musamman tsakanin MARKEKE da KUNKUMEMEN gari, amma da zarar ka fara isa kwaryar masarautar birnin DABO, inda ba a dabo, Gwamna Gandun Aiki, ya sanya jami’an tsaro su yi dako a kan hanya, wato abin da Gwamna Malam Nasara el-Rusau ya kamata ya kwatanta a kan iyakokin kananan hukumomin da ke kewaye da Jihar Bayan-kada.
Titin Haurubja ya ci rayukan manya da jiga-jigan jagorancin al’umma, har ma a kwananan nan ya cinye rayuwar ministan kwadagon Haurobiya. Duk da cewa muna nuna alhini da ya yi wa Gwamnatin Baban-burin-huriyya ta’aziyya, muna kuma yin kira da karajin babbar murya kan lallai hukumomi a Haurobiya ya bijiro da wani babban dandazon da cincirindon masu ruwa da tsaki, don shawo kan matsalolin da suka hada da gada-gadar gudun gada da iyalan Da’u da ke yi mana SAMAR-SARMA DIF-DIF, wato irin takun dodannin nan a cikin talatainin dare. Idan kuwa bah aka niu sai in koma birnin mutanen can masu Inda-inda, wato Jihar Ni-na-ja, tun da a can idan za a gaishe da Babban mutum mai rawani, sai a ce BAGADOJI. Kun ga ke idan a masarautar Bahagon Babban mutum mai rawani BABU-GADOJI, to wa zai yi musu “gada-gadar gudun gada?’ Watakila ma ko gada ta cikin daji ba za a samu ba.
Kwananan nan masu CAbIN ZABARIN BABURIDO suka haifar da matsalolin da suka salwantar da rayuka da dukiyo a biranen Haurubja da Ikko ikon Allah. Wannan ma wata matsalar ce da masu fuka-fukin tashi mutanen Mista Darlong ke fama da ita, musamman idan ba a samar musu abin yi ba, a kantunan Dong Fong na mutanen Mao Zedong, ta yadda mutanen Mista Gizagong za su daina yin dirshan da kashe fatari a cikin Kangong.
Batu na ingarman kwangiri, tsilli-tsillin matsalolin da ke addabar al’umma a titunan Haurobiyawa, hukuma na da laifi, gama-garin al’umma kuwa su suka fi tafka ta’asa a kwanon tasar su. Domin kamata ya yi Hukuma ta sanya jami’an Rawar dandi da sassarfa a titi ko Rodi da sasssaben titi su rika gudanar da ayyukan su har cikin talatainin dare, inda za su rika cafke masu “Gada-gadar gudun gada; kuma akwai bukatar gwamnatin Tarairayar Haurobiyawa ta toshe kwazazzaban tituna, sannan ta hana jami’an tsaro karbar ’yan kwabbai. Su kuwa gama-garin al’ummasu rika kai rahoton batagarin da ke karakaina a garuruwan su, muisamman a wannan lokaci da ake fama da matsalolin haramtas bobo da kwambon bokoko, gha kuma satar nagge da karsana da bujimi
Sakon makaranta: Ta’aziyya

Salam. Da fatan mai girma Malam Dodo yana cikin koshin lafiya. Allah ya sa haka amin. Ina mai bayyana alhini na wajen bayyana wa shagabanni da sauran dalibai masu daukar darasi a Farfajiyar Amitattaciyar jaridar Haurobiya, cewa, a makon da ya arce, Shagaban dalibai Dodanni na kasa “Bashir Ya’u” (Uncle Bash) ya zamo maraya, don kuwa ya rasa mai saya masa alawa, da mazarkwaila. (mahaifinsa).
A madadin dalibai na Jihar Da fullo-ke-damawa muna masa ta’aziya da fatan Rabbi ya sa can ta fi nan. Ga mai son yi masa ta’aziyar yana iya latsa 07037133338.
Daga Sabiu Uba New Nig. Yola Shagaban daliban Jihar Da-fullo-ke-damawa 07032385544. [email protected].
Muna rokon Mai-duka  Mai-kowa, Mai komai ya yi masa rahama. Allah Ya kyauta karshen mu. Amin summa amin. – Malam Dodo.