Gadar Charanchi ta ci matafiya 23
Manajan Daraktan Hukumar Kula da Hanyoyin Tarayya (FERMA) Mista Gabriel Amuchi ya bayyana kudirin hukumar na hanzarta gyara gadar da ta karye kuma ta ci mutum 23 a ranar Litinin da ta gabata a kauyen ’Yanranda da ke karamar Hukumar Batsari da ke Jihar Katsina.Mista Amuchi, wanda ya yi magana tab akin Ko’odinetan Shiyya na […]

Manajan Daraktan Hukumar Kula da Hanyoyin Tarayya (FERMA) Mista Gabriel Amuchi ya bayyana kudirin hukumar na hanzarta gyara gadar da ta karye kuma ta ci mutum 23 a ranar Litinin da ta gabata a kauyen ’Yanranda da ke karamar Hukumar Batsari da ke Jihar Katsina.
Mista Amuchi, wanda ya yi magana tab akin Ko’odinetan Shiyya na hukumar mai kula da Arewa maso Yamma, Mista Michael Akeyo a Katsina a shekaranjiya Laraba, ya ce “An gina gadar ce a 1990, kuma ruwa ya karya ta ce sakamakon ambaliya, kuma irin haka kan faru a kowace shekara 25.”
Ya ce ya je wurin da lamarin ya faru ne bisa umarnin Manajan Daraktan domin duba halin da ake ciki, ya ce shirye-shirye sun yi nisa a gefen hukumar domin sake gyara gadar.
Manajan Daraktan ya shawarci masu motoci da ke bin hanyar su rika taka-tsantsan tare da kiyaye uamarnin ’yan sanda da jami’an hukumar kiyaye hadari ta kasa da suke wurare da dama domin kula da direbobin.
Mista Amuchi ya ce ofishin FERMA na Katsina ya samar wa masu motoci wasu hanyoyin bi zuwalokacin da za a kammala gyarar gadar da ta karye.
A ranar Litinin da ta gabata ce wasu motoci biyu ciki har da wata bas dauki da fasinjoji 24 suka fada cikin gadar da ta karye, inda mutum 23 suka mutu, biyar kuma suka ji rauni.
Aminiya wadda ziyyarci wurin ta samu labarin cewa an gano gawarwaki 15, zuwa ranar Talata, inda kuma ake ci gaba da neman sauran. An gano gawarwaki 11 a kauyen Ajiwa da ke karamar Hukuma batagarawa, yayin da aka gano hudu a karamar Hukumar Rimi.
Bas din mai lamba dA 328 KZR tana kan hanyarta ta zuwa Kano ne daga Katsina, kuma Aminiya ta samu labarin cewa mazauna kauyen ’Yanranda sun yi kokarin tsayar da direban bas din amma bai tsaya ba sakamakon mugun gudun da yake yi, inda yana zuwa ya fada a gadar. Ita kuma daya motar kirar kanta Mistubishi dauke da mutum uku ta fada a gadar ce da misalin karfe 5;00 na asuba, sai dai an ceto dukkan fasinjojinta da rai. Direban kanta ya ce ya ki tsayawa ne saboda ya dauka ’yan fashi ne suke tare shi.