Gadar Gwange: Kasuwar da ta zama maboyar ’yan ta’adda

Babbar  Gadar Gwange wacce take Kasuwar  Gamboru, a Unguwar Kwastam a birnin Maiduguri, gada ce da ta kai kimanin shekara 40. Jama’a suna harkar kasuwanci a cikinta. Gadar ta yi kaurin suna a da can wajen aikata miyagun laifuffuka, a wasu lokutan har da kisa a jefa gawar cikin ruwan kasar gadar, ta yadda  iyalan […]

Gadar Gwange: Kasuwar da ta zama maboyar ’yan ta’adda

Gadar Gwange wadda ta zama mavoyar ’yan ta’adda a baya

Babbar  Gadar Gwange wacce take Kasuwar  Gamboru, a Unguwar Kwastam a birnin Maiduguri, gada ce da ta kai kimanin shekara 40. Jama’a suna harkar kasuwanci a cikinta. Gadar ta yi kaurin suna a da can wajen aikata miyagun laifuffuka, a wasu lokutan har da kisa a jefa gawar cikin ruwan kasar gadar, ta yadda  iyalan wadanda aka kashe ba za su ji labarin dan uwansu ba.                                                                                                                                                 Da rikicin Boko Haram ya fara kazancewa, mabiya kungiyar Boko Haram sun rika farautar mutane suna kashe su suna jefa  su a karkashin gadar, kafin sojoji su karbe iko da karkashin gadar, inda harkokin kasuwanci suka koma  yadda suka kamata.                                                                                                                                              Wakilinmu ya ziyarci karkashin gadar inda ya zanta da wadansu dattawa da wadannan abubuwa suka faru a kan idonsu shekaru da dama da suka gabata.

Malam Bulama Ibrahim, shi ne Shugaban Kungiyar Kananan ’Yan Kasuwa na Kasuwar Gamboru (Kasuwa), ya shaida wa Aminiya cewa “Wannan gada ta haura shekara 40, don mu ma mun tashi ne muka ga wannan gada. A wancan lokacin daji ne har da namun daji a cikinta. Bayan da mutane suka fara yawaita ne sai kisan kai ya yi yawa a kasar gadar. Idan mutane sun biyo ta wurin, mutanen da ba a san ko su wane ne ba sai su kama mutum su yanka shi ko su kashe shi su jefa gawar a ruwa ya tafi da shi. A lokacin muna tsammanin suna cire wasu abubuwa ne a jikin gawar don su yi tsaface-tsafacensu, har muna kwana a cikin zullumi mu tashi da shi domin muna jin tsoron kada wani dan uwa ko danka ya bi wannan wuri, ga shi kuma dole ne sai an bi ta wurin domin gada ce wacce ta hade Unguwar Gwange da Babbar Kasuwar Maiduguri da ake kira Monday Market.”
Ya kara da cewa “A daya bangaren kuma ta nufi hanyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da ita kanta Jami’ar Maiduguri a hanyar zuwa kananan hukumomin Konduga da Bama da Gwoza da kuma iyakar kasar nan da kasar Kamaru.  Gadar ta kuma  hade da hanyar zuwa Garejin Muna da kananan hukumomin Mafa da Dikwa da garin Gamboru-Ngala wanda ya yi iyaka da kasashen Kamaru da Chadi. Kuma ita ce hanyar shiga cikin gari, sannan a Kasuwar Gamboru ne muke sayar da kayan marmari da ake sarowa daga wurare masu nisa zuwa nan, inda mutanen gari suke zuwa su saya ko su sara. To ka ga dole sai an bi ta wannan wuri domin Shatale-tale ne da ya kasa hanyoyin kashi 4, kuma kowane sai an bi shi, to dalilin da ya sa ake yawan kashe mutane ke nan a karkashin gadar.”

“Su kuma masu kashe mutanen muna tsammanin su cewa ba su da aikin yi ne ko ba su da wani jari mai karfi na yin kasuwanci,” inji shi.

Ya ce suna kuma zargin suna da iyayen gida da suke aiko su don samar musu da sassan jikin mutane don tsaface-tsaface.

“To amma daga baya abin ya yi sauki kwarai da gaske, kafin zuwan rikicin Boko Haram. Zuwan kungiyar Boko Haram kuma sai abin ya sake tashi kamar an fama gyambo, shi ke nan sai wurin ya ci gaba da zama maboya ko matattarar Boko Haram inda suke kamo mutane su kashe su cikin sauki, kuma sun kashe mutane da dama, saboda a karkashin gadar akwai lunguna da mutum zai iya cuya ya aikata laifi, jami’an tsaro su biyo shi ya bace musu ya shige karkashin gadar ya boye ba su ganshi ba. To haka Boko Haram suka yi ta cin karensu babu babbaka a karkashin gadar, inda a baya sai da muka yi ta neman wurin da za mu iya tsayawa mu ci gaba da gudanar da kasuwanci domin Allah ne kawai Ya kare mu daga shiga hannun wadannan miyagun mutane, kafin daga sojoji su shawo kan lamarin, su kwace wurin mu samu sauki mu dawo harkokinmu,” inji shi.

A karhe ya ce, “Ina rokon gwamnati ta zo ta gyara karkashin gadar gudun kada a sake komawa gidan jiya, wato ta gyara ta gina shaguna ta dada kakkafa kananan masana’antu don samar wa matasa aikin yi, domin karkashin gadar ba karamin wuri ba ne.’’

wani dattijo mai suna Yahaya Ahmadu, mai shagon sayar da kayayyakin masarufi a karkashin ya ce “Gaskiya a da muna cikin fargaba da tashin hankali kan yadda kashe-kashen mutane ya yi yawa a wannan wuri tun kafin bayyanar Boko Haram da lokacin Boko Haram, a takaice a rikicin Boko Haram mun dandana kudarmu mu masu neman abinci a wannan wuri, domin a wannan shatale-talen gada ne rikincin Boko Haram ya fara tashi kasancewar ’yan kungiyar Boko Haram sun dauko majinyaci su za su kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri sai jami’an tsaro suka tarwatsa su suka harbe na harbewa, inda su kuma suka harzuka har abin ya yi kamari ya kai ga Boko Haram sun kori jami’an tsaro a wurin ya zama Cibiyar Makasa na Boko Haram.  Duk inda suka kai hari suka kashe mutane to za su dawo nan, su boye makamansu kafin su koma Unguwar Bulabulin-Ngarnam. Yawancinmu masu karamin karfi ne muna neman abinci a nan, akwai masu sayar da danyen kifi da kayan gwari da abinci da masu kira da jima da sauransu.”

Ya ce an kashe wadansu abokan kasuwacinsu, domin a wuri ne na ba-ta-kashi a tsakanin jami’an tsaro da ’yan Boko Haram, saboda kasar gadar tana da girma da fadin da za a iya yin komai. Ya ce, “Ba karamin gumurzu aka yi ba saboda  haka muna zuwa kasuwar ce kawai da nufin ko a dauki ranmu ko mu tsira. Shi ya sa koyaushe cikin shirin yin gudu muke. Daga karfe 10 na safe zuwa karfe 12 na rana akalla za mu yi gudun fitar rai sau 3, mu gudu mu dawo-mu gudu mu dawo. Kuma ko da mutum zai wuce kasar gadar zai wuce ne cikin fargaba, saboda ta iya yiwuwa a turaka karkashin gadar a yi maka yankan rago babu wanda ya sani, kuma ba za mu san inda aka jefa gawar ba. Idan lokacin akwai ruwa sai su jefa gawar ruwa ya tafi da ita bayan sun cire abin da za su cire, to amma lokacin Boko Haram idan sun kashe suna haka rami su binne na binnewa, wani lokacin kuma ba sa binnewa sai su bari su yi ta wari. Babu shakka wurin nan a da an mayar da shi matattarar kashe mutane, amma yanzu alhamdulillahi.”

Ya yaba wa ’yan kato-da-gora da ya ce sun taimaka wajen fitar da ’yan Boko Haram daga cikin gari, “Wannan gada da wannan kasuwa tamu ta Gamboru karkashin gada da ke Kwastam, ba mu da wata matsala duk wanda ka gani to yana neman halaliyarsa ce, sannan ita kanta karkashin gadar ta zamo matattarr shara sai Baban Bola ko wadansu almajirai za a ga suna bi suna tsince wasu abubuwan amfani, kuma jami’an tsaro sun yi wa wurin kawanya. Mun so mu rika noma a wurin amma jami’an tsaro sun hana shi ne muke rokon gwamnati ta yi wa Allah ta gyara wannan wuri ko dai ta gina shaguna ta sanya haya ko kuma ta kafa kananan masana’antu don inganta tattalin arzikin jihar da samar wa matasa aikin yi don magance zaman kashe wando.”