Gadin dabbobi
Wani ne matarsa za ta aikin Hajji, dayake tana kiwon dabbobi sai ta ce wa mijinta: “Bala, ka kula da dabbobina.” Haka ta yi ta fada masa a kullum, har dai ta shiga jirgi. Kafin su tashi ta sake lekowa ta jirgi ta ce masa: “Bala, na fa gaya maka ka kula mini da […]
Wani ne matarsa za ta aikin Hajji, dayake tana kiwon dabbobi sai ta ce wa mijinta: “Bala, ka kula da dabbobina.” Haka ta yi ta fada masa a kullum, har dai ta shiga jirgi. Kafin su tashi ta sake lekowa ta jirgi ta ce masa: “Bala, na fa gaya maka ka kula mini da dabbobina.” Ashe wani attajiri ya ga abin da matar nan ta yi, ya kuwa ji haushi sai ya biya wa mijin nan kujera, shi ma ya tafi Makka. A can sai matar nan ta ga mijinta wurin jifar Shaidan sai take cewa: “Kai, lallai kamar ta yi yawa, ga wani kamar Bala.” Bayan wani lokaci sai ta sake ganinsa, sai ta ce masa: “Wai ko Bala ne?” Ya ce shi ne. Ta ce: “Wa ya kawo ka nan kuma ina dabbobina?” Ya ce mata: “Dabbobin banza, su mutu mana don kaniyarsu!”
Daga Anisa Daura, 07038591359