Gadon “a ware” na ’yan Biyafura
A ware, wadansu ne kalmomin da ke fitowa daga bakunan wasu ‘yan Najeriya marasa kishin kasa a halin yanzu. Su dai manufarsu da kokarinsu duk ya ta’alaka a kan ganin sun yi nasara raba kasar nan. Wadannan ba wasu ba ne illa wasu jama’ar yankin Ibo da ke a sashen Kudu maso gabashin kasar nan. […]
A ware, wadansu ne kalmomin da ke fitowa daga bakunan wasu ‘yan Najeriya marasa kishin kasa a halin yanzu. Su dai manufarsu da kokarinsu duk ya ta’alaka a kan ganin sun yi nasara raba kasar nan. Wadannan ba wasu ba ne illa wasu jama’ar yankin Ibo da ke a sashen Kudu maso gabashin kasar nan.
Wannan fafutukarsu ta gado, asalinta ta faro ne tun a shekarar 1966, inda shugabaninsu (‘yan tawayen) Ironsi da Ojuku suka kaddamar da juyin mulki na farko a kasar nan, tare da taimakon wasu tsirarrun sojoji, don kawai kin jinin yankin Arewa. Kodayake shi Ojukku bai shiga cikin sojojin juyin mulkin ba, amma Ironsi ya nada shi Gwamnan Lardin Kudu maso Gabas (yankin Ibo), a cikin dan lokacin da ya yi a kan karagar mulkin kasa, watau watanni shidda da suka yi bayan hambarar da gwamnatin su Firayiminista Abubakar Tafawa balewa da Firimiya Sa Ahmadu Bello.
Bayan ture gwamnatinsu, tare da kashe Ironsi ne, sai Ojuku ya kafa wata kungiya mai suna Biyafara, wai ita kungiya ce mai fafutikar kare hakkin Ibo. Ba komai ne ya sa suka sabbaba wannan kungiya ba, illa ganin sun kasa mallake dukkan mukaman gwannatin tarayya ga kuma bincike da ya nuna yankin kasar su yana cike da arzikin man fetur.
A hankali ganin kungiyar ta samu karbuwa daga dangi, ’yan uwa da jama’arsa na yankinsu, ga kuma tallafi da goyon bayan da wasu daga cikin manyan kasashen duniya irin su Isra’ila da Faransa da sauransu da dama suke ba su;sai ya ga ba abin da ya rage musu illa su yi azamar fito da gundarin manufar tasu a fili; watau ‘A ware’, don haka, nan da nan sai ya kaddamar da kasar Biyafara ma dungun ta ‘yan a ware’.
Ita dai wannan manufar tasu ce ta haddasa yakin basasa na farko a kasar nan, wanda ya gudana a cikin shekaru uku (1967-1970),ya kuma lakume rayukan al’ummar kasa da dama, musamman jama’arsu ta Ibo. Sai da suka ga ba sarki sai Allah sa’annan suka mika wuya ga sojojin gwamnatin tarayyar kafin yakin ya lafa.
Tun daga lokacin ne suka riki kowace ranar 30 ga watan Mayu 30-5 a matsayin ranar tunawa da fafutukar kafa kasar Biyafara. Suna raya ranar suna kara wa gurinsu na kafa kasar su karfi da azama. Ko a cikin wannan shekarar ma(2017) sai da Khalifan su Ojukku, watau Nnamdi Kanu ya sake jaddada manufarsu ta ‘A ware,’ inda ya tsaya kai da fata wai sai an raba kasar nan.
Yanzu kam ta bayyana a fili cewar ashe ma duk abun barazana ce, da kuma rainin hankali irin na jama’ar Ibo. Domin ai da matasan yankin Arewa suka ce eh sun jaddada ‘A ware’ din, kuma har sun yanke ranar 1-10-2017 ta zama ranar ‘A ware,’, watau kowane Ibo ya bar yankin Arewa, suma jama’armu da ke can su dawo gida. Sai ga shi tun ba a kai ko’ina ba, dattawansu sun fara kokarin ganin an janye waccan maganar.
To ai kai ma daga jin Ibo yanzu ya ce ‘A ware’ kai ka san ba gaskiya ba ce, domin yadda jama’ar Ibo ke cin karensu babu babbaka a Arewaci, mu Hausa-Fulani ba mu da wannan gatan a yankinsu, domin ko rantsuwa na yi ba kaffara; ba wa ni Bahaushe a kasar Ibo da ya samu dama da martabar shuka jarin da ya kai na miliyan 10 a yankin Ibo, amma su fa? Kamfanoni da kasuwanci iri-iri duk sun samu damar kafa abinsu, duk da sarautu da mukamai ba wanda ba a ba su a yankin mu na Arewa, baya ga unguwanni da majami’u da aka yarje musu su kafa, kuma su zauna cikin lumana.
Yau ka leka kasashen Ibo ka ga yadda Bahaushe ke rayuwa cikin kunci da hantara da tsangwama da kyaradukyimasaakeyi. Dukda da aikingwamnati ne yakaidanyakenArewakasar Ibo to saiyagwammacekidi da karatu, sabili da masauki ma sai ya yi masa wuya, balle muhallin zama. Haka ma ko a kasuwanni Bahaushe bai yi mukamin da zai samu rumfa a cikin kasuwannin su ba, sai dai a bayan kasuwa.
To amma shi ne yau Ibo zai bugi kirji ya ce wai ‘A ware’? Kai gaskiya madallah da yunkurin matasan Arewa, madallah da tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Yin hakan da suka yi (matasanArewa), ya bayyanar da abubuwa kala-kala a kan wannan gadon burgar da aka dauki tsawon shekaru 50 ana yi mana ita.
Kun ga dai yanzu mun gane ashe ma abin duk fafalolo ne’kunburi ba karfi. Domin da ba haka ba ne da yanzu sun yi nisa akan shirye-shiryen warewar tunda sun samu amincewar da ‘A waren’din. Sai ga shi su yanzu yadda za a samu sulhu da matasan Arewa kafin cikar kayyadajjiyar ranar da aka ba su kawai suke nema.
Mun kuma gane ashe ma abun hadda kasuwanci a cikinsa, domin suma su tallata hajar ‘A ware’ashe ana ba su damman kudi ne a duk lokacin da suka yi yunkurin turza waccan manufar ta su, saboda sun gane da cewar kowace gwamnatin lokacin ba ta son a a ce a lokacinta ne aka tarwatsa kasa, aka ware yankunanta, shi ne sai suka mayar da shi dabi’a, da zarar sun ga an kafasabuwargwamnati, sai su yi wuf su bijiro da barazanar ta su don a kwashi makudan kudi a ba su san nan suyishuru.
D a zuwan siyasa sai aka surka manufofin kungiyyar Biyafara da tafiyar siyasa, ta yadda duk gwamnatin da aka kafa da ba ta ‘yan yankinsu ba, sai su yi kokarin ganin sun zame mata karfen kafa, duk su bi ta su sassake da matsalolinsu da sunan kafa yankin Biyafara, dole idan gwamnatin na so a sakar mata mara ta yi azamar ba su manyan mukamai har da wadanda ba su kamace su ba.
Yanzu an yi walkiya duhu ya yaye, in dai a waren suke so na gaskiya to mun yarda da ‘A waren’, domin mu ma yanzu ba ma shakkun komai a kan hakan, raja’ar da muka yi a kan arzikin man fetur dinsu a can shekarun baya; mun gane kuskure ne, kuma mun dauko hanyoyin gyara gadan-gadan. Idan kuma arzikin man fetur din ne ake yi muna gadara da kurin da shi, har ake hasadar a ci tare da mu, to muma ashe Allah ya bamu, rashin dubawa ne kawai da ba a yi tun a farko ba.
Idan kuwa dama can ba da gaske suke yi ba, kawai dai sun rike shi wani salon ba da tsoro da samun kudi ta kafar kangin siyasa ne, to muna ba su shawara da su bari, domin yanzu kowa a kasar nan ya gano su. Don haka ‘A ware’ ba zai sake yin tasiri a kasar nan ba, balle ya tada kura. Don haka ba abin da ya fiye musu illa su saki waccan akidar ta su, su fara tattalin sake kafa wata sabuwa ta kishin kasa, tun kafin su fadi ba nauyi daga bisani a zo a ji kunya.
Ku kuwa kungiyar matasan Arewa muna gode muku da kuka yi nasarar tsunka zaren wannan gadajjiyar barazanar, don haka mun a rokon kutunda sun karaya,susaduda sun tuba, to kuma ku yi hakuri ku yafe musu, ku janye waccan kayyadajjiyar ranar da kuka saka musu, ku fara shirye-shiryen shinfida yarjeniyoyi masu kyau da amfani da su ,don shimfida hadin kai da ci gaban kasarmu. Ya Allah ka dauwamar da kasar mu Najeriya a dunkulalliyar kasa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali amin.
A’isha Usman Liman, 09093467171