Gagdi ya gwangwaje ’yarsa da mota bayan ta kammala sakandare

Ɗan majalisar ya bai wa ‘yar tasa mamaki bayan gwangwaje ta da danƙareriyar mota.

Gagdi ya gwangwaje ’yarsa da mota bayan ta kammala sakandare

Ɗan Majalisar Tarayya daga Jihar Filato, Yusuf Gagdi ya gwangwaje ‘yarsa, Aisha Yusuf Gagdi da danƙareriyar motar ƙirar SUV a matsayin tukuici bayan ta kammala makarantar sakandare ta Lead British International a Abuja.

An ruwaito cewar Aisha, ta samu kyakkyawan sakamako a Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a (JAMB), wanda hakan ya sanya mahaifin nata yi mata bazata da kyautar mota.

Ɗan majalisar ya wallafa hotunan bikin kammala makarantar ’yar tasa a shafinsa na Instagram a ranar Asabar.

“Yau, na halarci bikin kammala makarantar ’yata. Kallonki ’yata kina tafiya kan dandali ya cike zuciyata da farin ciki da soyayya.

“Na yi farin ciki da nasararki da kuma ƙwazon da kika nuna. Ina fatan ki ƙare hakan a gaba da farin ciki.

“Ina taya ki murna, tauraruwata mai haske!”

Sai dai kyautar motar da Gagdi ya bai wa ’yarsa ya bar baya da ƙura a kafafen sada zumunta.

Wasu na ganin bai kamata a ce an bai wa yarinya kyautar mota saboda ta kammala makarantar sakandare ba.

Wasu na ganin bai kamata ya bayyana kyautar ba duba da halin ƙunci da ake fama da shi a ƙasar nan.