Gaggauta sa yara a makaranta

Kamar yadda Sarki yake neman Yarima, haka iyaye suka mayar da ’ya’yansu. Ta fuskar sai sun gaje su, ko ma su fi su samun daukaka a duniya! Bayan a zahiri kowa musamman yara suna da shirin da Ubangiji Ya yi musu, ba wai tsarin iyaye suke bi ba. Su iyaye aikinsu bai wuce su dora […]

Gaggauta sa yara a makaranta
Gaggauta sa yara a makaranta

Kamar yadda Sarki yake neman Yarima, haka iyaye suka mayar da ’ya’yansu. Ta fuskar sai sun gaje su, ko ma su fi su samun daukaka a duniya! Bayan a zahiri kowa musamman yara suna da shirin da Ubangiji Ya yi musu, ba wai tsarin iyaye suke bi ba. Su iyaye aikinsu bai wuce su dora su a hanya ba.

Idan muka lura a yau iyaye na  matsa wa ’ya’yansu kan sai sun zama mafarkin da suke gani, a gaggauta sa yara a  makarantun naziri. Su zarce firamare da sakandare har jami’a duk don iyaye su ga sun samu magada sun tabbatar da burin da suka yi ya zama zahiri.

Shekarun farko na yara suna da muhimmanci ga rayuwa baki daya. Idan aka bayar da yaro ga wanda bai san haka ba, yaro kan kangare, a kan haka ne wadansu iyaye kan ba kakanni raino, ko kula da ’ya’ya na tsawon wani lokaci, inda yara kan koyi hikimomi a kauyuka.

Manufar bayar da yaran kan zama a koya musu fahimta da aiki da basira, su koyi hadin kai da aiki tare, inda hakan zai kwantar wa iyaye hankali, yayin da suke wajen aiki ko wata hidima ta daban ko irin iyayen da suke saurin haihuwa. A irin wannan lokaci ana shirya yara don karatun firamare, su san launuka su haddace wasu kalamai da iya rubutu, fenti da karatu. Su koyi wakoki da wasanni daban-daban.

Tsarin kai yara makaranta da wuri kan zama wani matakin koyon barin iyaye a gida tare da tafiya makaranta. Hakan ci gaba ne domin a rayuwa sai an kai matsayar da yara za su rabu da iyaye, duk daren dadewa. Amma abin tambaya shi ne a wane lokaci za su rabu, kuma hannun wa za su fada?

Duk da wahalar da yara kan fuskanta wajen tabbatar da burinsu wajen ayyukan je ka ka dawo, (na aikin gida da aikin gwaji), tare da yin zuku don a gama karatun cikin gaggawa, a wani lokacin sai ka iske dan shekara tara ko goma a sakandare, dan shekara 15 a jami’a. Ko a kwanan nan an samu wani yaro dan shekara 12 da ya kamalla sakandare ya shiga jami’a a kasar Ghana.

Wadansu irin wadannan yara kan fada hadarin zama shagwababbu, ko ’yan daba ko su hadu da malalata ta yadda za a lalata musu tarbiyya baki daya. Domin a shekarun farkon na balaga ko gab da balaga yara na son ’yanci da yin duk abin da suka ga dama. Idan an matsa musu sai su bi duk hanyar da za su bi wajen ganin sun ji dadin kuruciyarsu.

Iyaye na ganin su dai burinsu ya cika, tun farko a shekara ta uku dansu yana zuwa makaranta. A kwanan nan har an bude ajin jarirai, inda ake koya musu gane mutane, wadansu yaran ma a keji ake jefa su! Su saba da wasu bakin al’adu dama mafi yawan malaman da suke tafiyar da irin wadannan makarantu ko gidaje, baki ne, suna da irin tasu manufar da akidu.

Kuma har malamai kan sa ’ya’yansu cikin irin wannan tarko, malamai da ya kamata a ce sun san matakin da ya kamata a sa yara a makaranta, su ma sun tafi da zamani, suna biye abin da suka ga ana yi. Wannan tsarin kan rage soyayya da shakuwa a tsakanin mahaifa da ’ya’ya, inda wadansu yara a makarantun suke yin karin kumallo, kafin iyayensu su dawo sun yi barci, sun fi sabawa da masu aiki a kan mahaifansu.

Akan samu iyayen da suke kai ’ya’yansu makarantu bisa dalilin zuwa wajen aiki, wadansu tunda sanyin safiya suke barin gida sai da almuru za su dawo! Wai ma’aikaci ne zai kula da yaransu, don haka a irin wannan tsarin dole su kai su gidan raino ko makarantun da za a aje ’ya’yan, wadansu har makarantun kara karatu bayan an dawo daga makaranta suke sa yara.

A tsarin irin wadannan makarantu ba a kai ziyarar ba-zata, bisa haka sai ma’aikatan sun san da zuwan iyayen yara kafin su zo. Don haka sai a tsabtace su in ana tsammanin zuwan iyayen. Bayan a da an bar su a cinkushe cikin kazanta, ba isasshiyar iska, wanda hakan yana sa kara yiwuwar su rika dauko cuttutuka kamar tari da kuraje.

Saboda tsadar makaranta da jin an bude wata sabuwa sai iyaye sun dunguma can, bayan ba a san abin da ke ciki ba. Sau da yawa abu mai tsada kan zama fitina ko sabon abu na yayi kan zo da wani nau’in sharrinsa. Kuma ta wani babin, hakan na jawo rikici a tsakanin ma’aurata, inda mata kan matsa wa maza sai an kai ’ya’yansu makarantu masu tsada, bayan a zahiri ba tsadar ke nuna inganci ba.

Mace tagari ita ce wadda ta damu da duniya da Lahirar mijinta. Sannan sau da yawa tarbiyya daga gida ake koyonta ba makaranta ba. Makaranta kan gina tarbiyya a kan tarbiyyar iyaye ne, musamman idan ’yan jeka ka dawo ne.

Wani abin takaici game da iyaye shi ne, sai ka iske ba su iya daukar nauyin ’yan uwansu marayu amma za su iya kashe wa ’ya’yansu kudi ko nawa ne, ta hanyoyin da ma ba fa’ida, duk da cewa sun san rashin yin sadaka da taimakon marayu kan zo da matsaloli a duniya da Lahira.

Kowace makaranta na da irin tsarinta, yayin da a wasu makarantu akan shirya a rika bada abincin rana, wato a dafa a makarantar a ba yaran sabanin yadda aka saba a kai wa yaron daga gida. Wadansu yaran ka taso da son barci da an shiga aji, a haka sun saba da zarar an shiga aji sai barci, musamman wadanda ba su  yin barci da wuri, kuma hana su barcin da rana a makaranta na iya haifar da wata illar ta daban. Idan aka bi tsarin koyarwa da kyau yakan koya wa yara wayewa da wuri, su yi abokai, su koyi sakin jiki da mu’amala da baki, amma ba nan gizo yake sakar ba.

Domin yawan irin wadannan makarantu matsala ne, a yau ga irin wadannan makarantun nan birjik a jami’o’i, makarantun gaba da sakandare a kasuwanni da shaguna. Da sunaye daban-daban, har da sunayen addini, duk don jawo hankalin iyaye, musamman iyaye mata, amma duk da haka ba a ba yaran irin kulawar da ta kamata.

Babu shiri ko yanayin koyarwa, wato hotuna da launukan da za su ja hankalin yara. Kalli yadda malaman suke, wadansu rashin abin yi ya sa suke koyarwa ko aiki a irin wadannan makarantu. Ba a biyan malamai albashi a kan lokaci, ko a samu ana ba su kudi kadan wanda hakan kan sa a dauki malaman da ba su da kwarewa don aiki a irin wadannan makarantu, wanda hakan illa ne ga yara a dogon zango na tafiyar rayuwarsu.

Saboda rashin kula daga gwamnati ko iyaye, akan bar irin wadannan makarantun na koyar da yara, su koyar ba tare da sa ido ba daga iyaye ko hukuma. Hakan hadari ne musamman ga iyaye domin ba ka san a wurin wa ka bar danka ba, ba ka san yanayin tsabta ko yadda ake yi idan ba ka nan, domin akan yi ganin ido a harkoki da dama. Akan cinkushe yara a irin wadannan makarantu ta yadda yara kan rasa iskar da a za su shaka, kuma ko koyarwar ce sai dai a ce an kai su riko a makaranta.

Yara su ne manyan gobe, a dalilin haka ya kamata kada a yi wasa da iliminsu, a tashin farko a tabbatar da yara sun hau hanyar zama nagari masu ingantacciyar rayuwa. Duk abin da mutum zai yi ba zai iya sauya kaddara ba. Duk abin da Ubangiji Ya yi nufi, sai ya tabbata, kuma abin da ba a kaddara ba ba zai taba yiwuwa ba har abada. Idan mutum ya dace da mata tagari wadda za ta koya wa yaran gaisuwa, sallama da godiya, wato gode Allah da kuma gode wa mutane, mutum ya samu komai.

A kyautata wa yara idan sun yi abin kirki, haka a hukunta su idan sun saba, a bi su a hankali ta yadda za su iya gane bacin ran iyaye, ko idon mahaifiya suka gani su san abin da take nufi, kuma idan sun yi kuskure a nuna musu sun yi ba daidai ba, ta hanyar hana su wata kyauta da aka saba, tare da yi musu magana cikin murya mai taushi ko a kwadaita su ko tsoratar da su gwargwadon abin da ake so su gane.

Kokarin ganin yara sun tarbiyyantu ya sa aka samar da wadansu mutane da kan bude gidajen raino da karbar yara, har zuwa lokacin da iyayen suka dawo daga wajen aiki, koda ba za a koya musu  karantu ba, amma tsarin na kama da makaranta ko wani gidan kwana, inda ake koya wa yaran wakoki ko a kunna kallo, ta yadda za a kore kewa, daga nan barci ya sace su. Ilimin da suka sani shi ne a ci abinci, a yi wasa, a yi barci! Domin masana tarbiyya sun tabbatar da cewa shekarun ilimi sukan kama daga shekara biyar ne. A nan an maganar tarbiyya ba karatu ba, ko zuwa makaranta.

A irin kasashenmu wadanda kowa na yin abin da ya ga dama, ba a sa ido ko kula a haka sai a rika cin mutunci da lalata yara, iyaye ba su sani ba, sai ranar da ta baci. Ya kamata jama’a su sani kula da ’ya’yan da ka haifa tare da watsar da ’ya’yan ’yan uwa, makwabta da marayu na haifar da fitina a al’umma.

Ita tarbiyya akan gina ta don mai ita ya more ta, ba wai don mai bada ta ya fi wanda yake da ita morarta ba. Idan muka bata rayuwar ’ya’yanmu, mun kashe al’ummarmu. Yara su ne manyan gobe.

 

Buhari Daure Kofar Kaura, Katsina

imel:[email protected]