Gaidam ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam, ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa da na duk mukaman da za a tsaya takara a jihar mai wakilai 98 a karkashin jagorancin Alhaji Yakubu Sidi Karasuwa da ganin jam’iyyarsu ta APC ta samu nasara a zaben watan gobe. Da yake jawabi a yayin kaddamar da kwamitin a […]

Gaidam ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa
Gaidam ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam, ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa da na duk mukaman da za a tsaya takara a jihar mai wakilai 98 a karkashin jagorancin Alhaji Yakubu Sidi Karasuwa da ganin jam’iyyarsu ta APC ta samu nasara a zaben watan gobe.

Da yake jawabi a yayin kaddamar da kwamitin a Damaturu, Gwamna Gaidam ya ce babban nauyin da ke kan ’yan kwamitin shi ne yin hobbasa don ganin duk mukaman da za a yi takara a kansu tun daga kujerun ’yan majalisun jihohi da na Gwamna da na majalisun tarayya da na Shugaban kasa Jam’iyyar APC ce ta lashe su.
Ya ce, akwai aiki a gaban ’yan kwamitin da ke bukatar sadaukarwa, kuma ya ce cancantarsu ta sa aka nada su a wannan kwamiti, kuma ya ba su tabbacin samun cikakken goyon bayansa da na duk masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC don ganin a kai ga nasara.
Ya ce sun cika kusan kashi 90 cikin 100 na alkawarin da suka dauka wa jama’ar jihar a yakin neman zaben da suka yi a shekarar 2011, musamman a fannin samar da ruwan sha da gina
hanyoyin mota da samar wa matasa akalla dubu 20 aiki da kuma yadda gwamnatin ta ba da muhimmanci kan harkokin tsaro inda ta kashe kusan Naira biliyan 10 a wadannan fannoni da sauran ayyukan raya kasa.
Ya yi kira ga magoya bayan Jam’iyyar APC a matakin kasa da jiha da kananan hukumomi su ba da cikakken goyon bayansu ga’yan kwamitin don ganin an ka jam’iyyar ga nasara.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista