Gaishe ka Bayajidda na biyu!

Muna godiya ga Maimartaba Sarkin Daura game da karrama Malam Muhammadu Buhari, Shugaban Tarayyar Najeriya da ya yi da lakabin Bayajida na biyu a ranar Juma’ar da ta gabata. Wannan abu ya zo a kan gaba ganin cewa Malam Muhamadu Buhari fitaccen dan Daura ne wanda ya daga martabar masarautar, da kuma Najeriya baki daya. […]

Gaishe ka Bayajidda na biyu!
Gaishe ka Bayajidda na biyu!

Muna godiya ga Maimartaba Sarkin Daura game da karrama Malam Muhammadu Buhari, Shugaban Tarayyar Najeriya da ya yi da lakabin Bayajida na biyu a ranar Juma’ar da ta gabata. Wannan abu ya zo a kan gaba ganin cewa Malam Muhamadu Buhari fitaccen dan Daura ne wanda ya daga martabar masarautar, da kuma Najeriya baki daya. Ya zamanto matakin da za a iya bi a kai ga biyan bukatar ciyar da kasa gaba da kuma kyautata matsayin talakawan cikinta ta hanyar kawar masu da dukkan matsalolin da ke addabar su a halin yanzu, da kuma dora su bisa tafarkin dogaro da kai don kai wa ga wadata da karuwar arziki.

Hakika tarihin Bayajida da kuma Sarauniyarsa Daurama, ya gauraye ko ina a fadin duniyar nan.Kamar yadda nasabar Muhammadu Buhari ta isa kowace nahiya, gida da waje, saboda tsananin sanin-ya-kamatansa da gaskiyarsa da rikon amanarsa da jajircewa wajen kyautata wa jama’arsa. Wanan lakabi da aka yi masa na Bayajidda na biyu zai kara karfafa masa gwiwa wajen turzawa da ci gaba da ayyukan alheri domin amfanin daukacin jama’ar Najeriya daidai da yadda Bayajidda ya kawar wa al’ummar garin Daura masifar da ta hana su more gardin rayuwa fiye da shekaru dubu da suka wuce. Haka nan kuma a matsayin abin alherin da Bayajida na farko ya yi a Daura, har hakan ya wanzar da zuriyasa wacce ta zame sanadiyyar kafuwar kasashen Hausa, sai ga shi nan kuma kyawawan ayyukan da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi suna inganta halayyar rayuwar jama’a da kuma share masu hanyar kai wa ga biyan dukkan bukatunsu.
A yanzu dai an tabbatar cewa jama’ar Najeriya kafatan dinsu na bayan Malam Muhammadu Buhari, sun kuma amince masa saboda sun gwada shi, sun kuma same shi sahihin mutum, managarci, mai tantance bambancin karya da gaskiya da nufin bin gaskiyar don neman tsira daga sharrin rayuwa da kuma hassadar magabta. Dangane da haka ne jama’a suka sanya shi a gaba, suka mika masa akalar rayuwarsu, domin sun san ba zai ja su, ya kai su wurin da za su tagayyara ko shan bakar wahala ba. Shi kuma a matsayinsa na shugaban kasarsu ya dauki alkawarin kaucewa biye son zuciya.Babu kuma wani abin da zai aikata sai wanda zai kasance mai tsananin amfani ga daukacin ‘yan Najeriya wadanda ya yi rantsuwar kare hakkinsu da rayukansu da kuma dukiyoyinsu ala kulli-halin.
Malam Muhammadu Buhari ya danki ragamar mulki a karo na biyu, amma a matsayin tsari irin na tafarkin dimokradiyya. Ya rigaya ya amince da irin wannan tsarin, ya kuma nakalci yadda ake gudanar da shi bisa la’akari da ra’ayin jama’a yana kuma kokartawa wajen aikata haka. Shi ya sa cikin ‘yan kwanaki kalilan da hawansa mulki, aka fahimci irin kamun ludayinsa, aka kuma fara ganin haske kan dukkan matakan da yake dauka a fafutukarsa na kyautata wa jama’a. Cikin ‘yan kwanaki masu zuwa za a fahimci cikakkiyar alkiblar da gwamnatinsa za ta kalla sa’ilin da ya kammala nade-naden manyan jami’an da za su kasance na hannun damansa da kuma ministocin da za su gudanar da harkokin ma’ikatun gwamnatinsa.
Wani hanzari ba gudu ba, jama’a sun tabbatar da cewa Shugaba Buhari ba zai yi zaben tumun dare ba idan ya tashi fitar da sunayen manyan jami’ansa.Ba kuma zai dauko wanda ke da wani makeken tabo a bayansa ba, ko wani mai guntun kashi a gindi. Zai darje zaratan ‘yan Najeriya ne, wadanda ya san ba za su ba shi kunya ba, za su yunkura yadda ya kamata don sauke nauyin da zai dora masu. To, amma duk da haka nan akwai mutanen da ke korafi, suna ganin kamar ana jan kafa ne wajen bayyana sunayen wadanda za a nada. Ta haka ne suke azzalawa, suna uzzura masa don ya yi abu cikin hanzari daga bisani kuma ya zo a rufe kofa da barawo ko ya yi kitso da kwarkwata, a yi ta gamadidi da batun, ana ta tujara da kwarmato.
Shugaba Buhari dai bai ce uffan ba game da hanzarin masu ganin bai yi gaggawa ba wajen nada sababbin jami’an da za su dafa masa, ya kuma kasance tamkar gwankin da bai dimuwa domin mai harbi.Sai kawai ya mayar da hankalinsa kan gagarumin aikin da ke gabansa na kawar da matsalolin da suka addabi kasarsa. Bisa ga dukkan alamu Shugaba Buhari ba zai ga ta zama ba sai ya shawo kan wadancan matsalolin daidai da yadda Bayajiddan farko ya yi, jama’ar kasar Hausa duk suke amfana da haka.
A Arewa akwai ‘ya’yan kwarai, wadanda suka taimaka wajen daukaka matsayin yankin a duniya baki daya, Shugaba Buhari ya kasance daya daga cikinsu wadanda suka bayar da gagarumar gudumawa wajen farfado da mutuncin Arewa sa’ilin da ‘yan Kudu suka far mata, suka karkashe shugabanninta. Ya kuma nuna tsananin bajinta a yakin Basasar da hakan ya janyo har aka samu nasarar tserar da Najeriya daga masifar da ‘yan tawaye suka nemi wurga ta ciki. Ashe ke nan ta kowace hanya aka dubi irin fafutuka da gudumawar da Shugaba Buhari ya bayar ga gina wannan gagarumar kasa za a tabbatar cewa ya cika dan halas daga Arewa, kuma mai kishinta da daukacin al’ummomin cikinta. La budda, Shugaba Buhari mutum ne da ya jajirce wajen ganin duk mutumin Arewa ya zama wata tsiya a harkokin rayuwa, ana kuma yi da shi a dukkan fannoni. Jama’a sun yi murna da lakabin da aka ba shi na Bayajidda na biyu, yana kuma kamanta ayyukan alherin da wancan Bayajiddan ya yi sa’ilin da ya kashe macijiyar rijiyar Kusugu a Birnin Daura mai cike da tarihi. Kuma idan har Bayajidda na biyu ya kintsa ina neman alfarmarsa wajen nada ni Majidadin Bayajidda don in taya shi yaki da zalunci da ha’inci da kuma cin hanci a Najeriya.