Gaisuwar mutuwa

Wani Bafulatani ne aka yi masa rasuwa sai wasu abokansa su uku suka je yi masa ta’aziyya. Na farko ya ce: “Ashe Baffa Allah Ya yi masa rasuwa? Allah Ya jikansa.” Na biyu ya ce: “Ashe Baffa Allah Ya yi masa mutuwa? Allah Ya gafarta masa.” Na ukun kuma ya ce: “Ashe Baffa kwana ya […]

Gaisuwar mutuwa
Gaisuwar mutuwa

Wani Bafulatani ne aka yi masa rasuwa sai wasu abokansa su uku suka je yi masa ta’aziyya. Na farko ya ce: “Ashe Baffa Allah Ya yi masa rasuwa? Allah Ya jikansa.” Na biyu ya ce: “Ashe Baffa Allah Ya yi masa mutuwa? Allah Ya gafarta masa.” Na ukun kuma ya ce: “Ashe Baffa kwana ya kare? Allah Ya rahamshe shi.” Bayan sun tafi sai ya fashe da kuka yana cewa: “Baffa abin ya yi masa yawa, ga mutuwa ga rasuwa ga karar kwana duk shi kadai. Allah Ya sa su tambaye shi daya kawai!” (Shi a zatonsa, wadannan abubuwa uku zunubbai ne ya aikata).

Daga Alhaji danladi China, Kano, 08034463170