Galibin cututtukan da suke addabar mutane daga dabbobi ake daukarsu – Likita
Wani likitan dabbobi kuma Shugaban kungiyar Ma’aikatan Kula da Lafiyar Dabbobi ta kasa reshen Jihar Yobe, Dokta Ahmed Ba’aba ya bayyana cewa kashi 70 cikin 100 na cututtukan da ke addabar dan Adam dabbobi ne ke yada su ta hanyoyi daban-daban musamman ta hanyar cin namansu. Dokta Ahmed Ba’aba ya bayyana haka ne a jawabinsa […]
Wani likitan dabbobi kuma Shugaban kungiyar Ma’aikatan Kula da Lafiyar Dabbobi ta kasa reshen Jihar Yobe, Dokta Ahmed Ba’aba ya bayyana cewa kashi 70 cikin 100 na cututtukan da ke addabar dan Adam dabbobi ne ke yada su ta hanyoyi daban-daban musamman ta hanyar cin namansu.
Dokta Ahmed Ba’aba ya bayyana haka ne a jawabinsa wajen bikin makon allurar rigakafin cututtukan dabbobi ta duniya, shiyyar Afirka ta bana da aka gudanar a garin Damaturu.
Shugaban ya ce, makasudin bikin shi ne a fadakar da jama’a kan hadarin cin naman dabbobi ba tare da jami’in kula da lafiyar dabbobi ya duba lafiyarsa kamar yadda ka’ida ta nuna ba.
Ya kara da cewa saboda muhimmancin kula da lafiyar dabbobi da ake yankawa a ci ne ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a taronta na cikarta shekara 60 da aka gudanar a birnin Malabo hedikwatar kasar Ekuatorial Guinea a shekarar 2010 ta amince a gudanar da bikin na mako duk shekara wanda aka fara a shekarar 2011 a Nahiyar Afirka.
Ya yi kira ga iyaye su rika yi wa ’ya’yansu allurar rigakafin cututtukan tarin fuka da cutar shan inna da kyanda da sankarau da sauransu.