Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo

Obasanjo ya bayyana hakan ne a cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’ inda ya zayyana halayen manyan shugabanni a matakin tarayya da na jihohi.

Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo

Cif Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce galibin ’yan Najeriya suna sha’awar yin amfani da muƙaman gwamnati ne kawai don arzuta kansu da abokan hulɗarsu su durƙusar da ƙasar fiye da yadda suka same ta.

Tsohon Shugaban ƙasar ya ce waɗannan mutane suna karɓar rancen biliyoyin Nairori, suna ganin cewa biyan kuɗaɗen gwamnati bayan an zaɓe su ba zai zama matsala ba.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’ inda ya zayyana halayen manyan shugabanni a matakin tarayya da na jihohi.

Littafin na ɗaya daga cikin sabbin littattafai guda biyu da aka ƙaddamar domin murnar cikar Obasanjo shekara 88 a makon jiya.

Tsohon Shugaban ƙasar ya ce akasarin waɗanda aka bai wa damar riƙe muƙaman shugabanci a ƙasar nan kamar Gwamnoni, shugabannin ƙasa, Ministoci, Kwamishinoni da shugabannin Ƙananan hukumomi, wasu nada mummunan shiri na son kai, kuma suna da yi niyyar azurta kansu ne yayin da al’ummar ƙasar ke ci gaba da durƙushewa cikin matsanancin talauci da rashin ci gaba.

Obasanjo ya ce, da yawa daga cikin waɗannan suna son zama gwamnoni ko kuma su jagoranci ƙasar nan ta wata hanya ko kuma wasu suna sha’awar yin amfani da ofisoshinsu ne kawai su arzuta kansu da abokan hulɗarsu sannan su bar ƙasar nan fiye da yadda suka same ta.