Gamayyar al’ummar garin Kundulum za su kashe miliyan biyar wajen gina gada

Al’ummar garin Kundulum a mazabar Garko da ke yankin karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe da tallafin hukumar CSDP za su gina Gada da Kwalbati na fiye da naira miliyan biyar. Tun farko al’ummar garin Kundulum sun fara Ginar ne ta hanyar taimakon kai da kai, daga bisani suka hada kai da hukumar nan ta […]

Gamayyar al’ummar garin Kundulum za su kashe miliyan biyar wajen gina gada

Al’ummar garin Kundulum a mazabar Garko da ke yankin karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe da tallafin hukumar CSDP za su gina Gada da Kwalbati na fiye da naira miliyan biyar.

Tun farko al’ummar garin Kundulum sun fara Ginar ne ta hanyar taimakon kai da kai, daga bisani suka hada kai da hukumar nan ta Gombe State Agency for Community and Social Debelopment Project CSDP.

Bayan al’ummar sun fara aikin, sai suka nemi hadin kan hukumar inda ta shigo ta ba su tallafi na kashi 90 na kudin da za a kashe su kuma suka bada kashi 10.

Da yake jawabi a wajen bikin bada tallafin, Janaral Manajan hukumar ta CSDP, Abubakar Ardo Kumo, cewa ya yi sun gudanar da irin wannan ayyuka sosai a garuruwa da dama ba Kundulum ne farko ba.

Abubakar Ardo Kumo, ya ce abin da al’ummar garin Kundulum za su yi shi ne su kara bai wa shugabaninsu goyon baya a gama wannan aiki a sake nemo musu wasu.

Ya kuma jawo hankalin shugabanin da cewa su rike amanar da aka dora musu na hakkin al’umma.

Daga nan sai Ardo Kumo, ya ce aikin da za ayi na gina gada da kwalbati zai lashe naira miliyan biyar, amma yanzu za su basu kashi 30 na soma aiki da ya kama naira miliyan  daya da dubu dari hudu da dari bakwai da arba’in da bakwai.

A nasa jawabin, wakilin Sarkin Gona Alhaji Usman Danburam, godiya ya yi wa wannan hukuma ta CSDP bisa yadda da suka bada tallafi don yin wannan gadar da za a ceto al’ummar Kundulum.

Sannan sai ya ce garin Kundulum Gari ne mai tsohon tarihi amma bai da kasuwa, inda ya ce kamar yadda aka kaddamar da wannan aiki, yana fata wata rana a bude kasuwar Kundulum.

Shi ma manajan ayyuka na hukumar mista Labilwa Isma’il, kiran al’ummar ya yi da kada su yi aiki mara kyau, domin idan suka yi aiki mara kyau sun yi wa kansu ne.

Shi ma manajan sa ido da tantancewa na hukumar, Muhammad Sani Adamu, kira ya yi da idan aka gama wannan aiki, kar su bari a rika zuba shara a kwalbatin don gudun cushewa, har ya jawo ambaliyar ruwa.

Shugaban kungiyar al’ummar Kundulum Ibrahim Sgu’aibu, ya yi alkawarin cewa za su rike amana kuma in sha Allah za su yi amfani da kudin yadda ya dace.