Gamayyar kungiyar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu ta koka a kan harin ta’addaci
Gamayyar kungiyar kwallon kafa ta mata da maza a Afirka ta Kudu da aka fi sani da (SAFPU) ta yi Allah-wadai da yadda wadansu bata gari a kasar suke kai wa bakin haure hari na babu gaira-babu-dalili al’amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan kasar waje da dama musamman wadanda ke yin kasuwanci a sassan […]
Gamayyar kungiyar kwallon kafa ta mata da maza a Afirka ta Kudu da aka fi sani da (SAFPU) ta yi Allah-wadai da yadda wadansu bata gari a kasar suke kai wa bakin haure hari na babu gaira-babu-dalili al’amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan kasar waje da dama musamman wadanda ke yin kasuwanci a sassan kasar.
Bakin hauren da al’amarin ya fi shafa sun fito ne daga kasashen Dimokuradiyyar Kongo da Etofiya da Malawi da Mozambik da Somaliya da Zimbabwe da kuma Najeriya.
Dubban jama’a daga cikin bakin hauren tuni suka yi gudun hijira zuwa wasu sassan kasar don neman dauki.
A wata takardar nuna bakin ciki da ta fitar a ranar Talatar da ta wuce mai dauke da sanya hannun daukacin ’yan kwallon kafa na maza (Bafana-Bafana) da kuma na mata (Bayana-Bayana) ta nemi a gaggauta tsayar da kisan gillars da ake yi wa bakin ba tare da wani bata lokaci ba.
“kungiyoyin kwallon kafa na Afirka ta Kudu suna bakin cikin abin da ke faruwa na kashe baki babu-gaira babu-dalili don haka muna kiran gwamnati da ta gaggauta shawo kan al’amarin”, inji sanarwar.
Kimanin makonni biyu kenan da wadansu bata gari a Afirka ta Kudu suke farwa bakin haure mazauna kasar wadanda ke kasuwanci a fannoni daban-daban da kisa da kuma kona musu dukiyoyi al’amurin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama yayin da wadansu kuma suka yi gudun hijira. Makisan sun yi zargin bakin hauren sun yi katutu a Afirka ta Kudu a fannonin kasuwanci al’amarin da ya jefa ’yan kasar cikin yanayin rashin aikin yi.