Gamayyar kungiyoyin Farar Hula ta yi taro a kan halin kasa a Kano 1

Wata sabuwar kungiya ta Gamayyar kungiyoyin Farar Hula ta yi taron gangami a Kano, inda aka tattauna muhimman al’amuran da suka shafi kasa da suka hada da tattalin arziki da rashin tsaro da kuma tabarbarewar sauran abubuwa na rayuwa.A jawabin maraba, wanda sakataren kungiyar Muryar Talaka, Malam Bishir Dauda Sabuwar Unguwa ya yi,  ya bayyana […]

Gamayyar kungiyoyin Farar Hula ta yi taro a kan halin kasa a Kano 1
Gamayyar kungiyoyin Farar Hula ta yi taro a kan halin kasa a Kano 1

Wata sabuwar kungiya ta Gamayyar kungiyoyin Farar Hula ta yi taron gangami a Kano, inda aka tattauna muhimman al’amuran da suka shafi kasa da suka hada da tattalin arziki da rashin tsaro da kuma tabarbarewar sauran abubuwa na rayuwa.
A jawabin maraba, wanda sakataren kungiyar Muryar Talaka, Malam Bishir Dauda Sabuwar Unguwa ya yi,  ya bayyana takaicinsa da al’amarin tsaro ya tabarbare kuma gwamnati ta gaza yin komai a kan hare-hare da kisan dimbin ’yan Najeriya da ake yi a kullum.
Haka nan Malam Bishir ya yi tir da lalacewar tattalin arzikin Najeriya, inda ya nuna mutanen kasa na cikin kunci da takuara kuma suna rayuwa ta kaka-naka-yi da tsananin talauci. Ya kuma zargi gwamnatin tarayya da laifin jawo lalacewar harkar ilimi. Ya bayar da misalin yajin aikin malama kwalejojin gwamnatin tarayya da ya jawo rufe kwalejojin har tsawon watanni bakwai.
A jawabin da shugaban Rundunar Adalci, Alhaji Abdulkarim dayyabu ya gabatar, ya yi suka ne ga ’yan yankin Naija-Delta da suke goranta wa ’yan Arewa cewa mai nasu ne.
Ya ce doka ta nuna cewa duk wata dukiya ta karkashin kasa mallakar dukkanin ’yan kasa ce. Ya kuma shawarta cewa kamata ya yi a debe ’yan Naija-Delta daga kasar da suke, wacce suke cewa mai ya gurbata ta, a mayar da su wani wajen kuma a gyara musu wajen don su ci gaba da rayuwa.
Alhaji Abdulkarimu, wanda kuma ya gargadi shugabanni su ji tsoron Allah wajen baiwa talakawa hakkinsu, ya ce ya kamata su san cewa talakawa fa amana ce a gare su. Ya kuma bayyana cewa halin da ake ciki na lalacewar abubuwa da zubar da jinni duk sun faru ne a saboda yawan saba wa Allah da ake yi. Don haka ya yi kira ga dukkanin jama’a da su koma ga Allah.
Shi kuwa Dokta Aliyu Muhammad Muri ya dora alhakin ayyukan ta da kayar-baya da kashe-kashen da ke faruwa kan makircin Amurka ne da kungiyar kasashen Turai, don a yi ta kashe musulmi tare da raunana tattalin arzikin Najeriya.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno