Gamayyar kungiyoyin kwadago ta nemi a kulle Jami’ar Tarayya ta Kashere
Hadaddiyar kungiyar Ma’aikatan Jami’ar Tarayya ta Kashere a Jihar Gombe sun kira taron gaggawa kan cewa sai an sallami Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Alhassan Muhammad Gani saboda rashin iya shugabanci. kungiyoyi uku ne suka yin hadin gwiwa, SSNU da NAAT a safiyar Litinin da ta gabata suka taru a babban dakin taro na jami’ar, inda […]

Hadaddiyar kungiyar Ma’aikatan Jami’ar Tarayya ta Kashere a Jihar Gombe sun kira taron gaggawa kan cewa sai an sallami Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Alhassan Muhammad Gani saboda rashin iya shugabanci. kungiyoyi uku ne suka yin hadin gwiwa, SSNU da NAAT a safiyar Litinin da ta gabata suka taru a babban dakin taro na jami’ar, inda suka tattauna yadda za a shawo kan matsalolinsu.
Hakan kuwa ya biyo bayan rashin biyan su albashinsu ne na watannin Augusta da Oktoba da suka gabata, sannan kuma an biya su albashin watan Mayu sau biyu bisa kuskure, wanda sun bincika ba daga jami’ar ba ne aka biya kudin kuma sun ce za su biya amma ba a lokaci daya ba.
Shugaban gamayyar kungiyar, Kwamred Mukthar Muhammad ya ce mataimakin shugaban jami’ar ya tabbatar musu da cewa sai sun biya wannan kudin a lokaci daya, shi ya sa babu wani ma’aikaci da zai samu albashin watan Oktoba.
Ya bai wa taron mambobin nasu na ma’aikatan jami’ar dama su bayyana ra’ayoyinsu kan matakin da ya dace su dauka, inda nan take suka dinga ihun cewa ‘Gani Must’ (Dole Gani Ya Sauka).
Matsayar da suka dauka, ita ce sun nuna cewa sai an kori mataimakin shugaban jami’ar sannan kuma za a kulle jami’ar da dukkan azuzuwan karatu da asibitin jami’ar, har sai gwamnati ta dauki matakin da ya dace, na biyansu albashinsu sannan a bude ita. Haka kuma za su tafi yajin aiki na makonni uku, domin gargadi.
Da yake mayar da martani kan zargin da kungiyoyin ma’aikatan jami’ar suke masa, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Alhassan Muhammed Gani cewa ya yi shi bai karbi kowanne irin koke daga wajensu ba, yanzu yake samun labarin daga ’yan jarida. Ya ce abin da ya sani kawai shi ne, jami’a tana biyan albashi yadda ya kamata.
Ya ce suna samun karancin kudi na biyan albashi, wanda sai an nemi ciko sannan a biya albashin. Ya kara da cewa kamar yadda suke kukan rashin biyan albashin watan Oktoba, wannan kam ba a biya ba kuma ba jami’ar Kashere ce kadai ba ta biya ba; sauran jami’o’i ma ba su biya ba saboda an dan samu canji ne daga Gwamnatin Tarayya wajen tsarin biyan kudin kuma duk lokacin da aka saki kudin za a biya.
Ya ce kuma albashin watan Mayu da aka biya sau biyu ake neman su dawo da shi, an biya ne a watan Agusta. Ya ce ya yi magana da shugabannin kungiyoyin ta bakin Magatakardar jami’ar kan cewa kar su taba, an biya ne da kuskure, za su dawo da su amma suka kashe.
Daga nan sai y ace shi bai kulle jami’a ba kamar yadda suke cewa za su je yajin aiki na makonni uku, shi ba ruwansa; duk wanda yake ganin zai je ya je ya bar masu son su yi karatu su yi karatunsu, shi bai kulle makaranta ba.
kungiyoyin dai sun kirayi mambobinsu kan cewa su tafi yajin aiki na makonni uku tare da kulle ko’ina a jami’ar, har ofishin Mataimakin shugaban jami’ar.