Gambo Mohammed ya koma Tunisiya

dan kwallon Kano Pillars Gambo Mohammed ya canza sheka zuwa kulob din Club Africain da ke Tunisiya a kwantaragin shekara uku.Mai magana da yawun kulob din Idris Malikawa ya tabbatar da wannan bayani ga manema labarai a shekaranjiya Laraba.Malikawa ya ce, Gambo ya samu zawarcin kungiyoyin kwallon kafa gudu uku da suka hada da kasar […]

Gambo Mohammed ya koma Tunisiya

Gambo Mohammed dan kwallon Kano Pillars Gambo Mohammed ya canza sheka zuwa kulob din Club Africain da ke Tunisiya a kwantaragin shekara uku.
Mai magana da yawun kulob din Idris Malikawa ya tabbatar da wannan bayani ga manema labarai a shekaranjiya Laraba.
Malikawa ya ce, Gambo ya samu zawarcin kungiyoyin kwallon kafa gudu uku da suka hada da kasar Sin watau Chaina da Saudi Arebiya da kuma Tunisiya amma bayan sun yi nazari sai suka shawarce shi ya koma Tunisiya.
Ya ce ana sa ran kafin karshen makon nan dan kwallon zai bar kasar nan don komawa sabon kulob dinsa a Tunisiya.
Gambo Mohammed yana daga cikin ’yan kwallon Najeriya Super Eagles da suka fafata a gasar cin kofin Nahiyoyi (Confederations Cup) da aka yi a Brazil a watan jiya.  Yana daga cikin zaratan ’yan kwallon da kulob din Kano Pillars ke ji da su a gasar rukuni-rukuni ta Najeriya.