Gambu mai wakar barayi ya rasu

A jiya Laraba ne Allah Ya yi wa Alhaji Muhammadu Gambo Fagada wanda aka fi sani da Gambu mai waƙar ɓarayi rasuwa, bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu ne a garin Maiyama na Jihar Kebbi, yayin da ake kan hanyar kai shi asibiti. An yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada yau Alhamis. […]

Gambu mai wakar barayi ya rasu
Gambu mai wakar barayi ya rasu

Marigayi Alhaji Muhammadu Gambo Fagada A jiya Laraba ne Allah Ya yi wa Alhaji Muhammadu Gambo Fagada wanda aka fi sani da Gambu mai waƙar ɓarayi rasuwa, bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya.

Ya rasu ne a garin Maiyama na Jihar Kebbi, yayin da ake kan hanyar kai shi asibiti. An yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada yau Alhamis.


Marigayin wanda ya shahara a waƙoƙin ɓarayi da ta ’yan tauri, ya rasu yana da shekara  67 a duniya, ya bar mata hudu da ‘ya’ya da jikoki da dama.

A shekarar 2009 ne Muhammadu Gambo ya yi ritaya daga yin waƙoƙin ɓarayi yayin da aka yi wani gagarumin bikin cikarsa shekara 60 a duniya, a Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato.