Game da hadin kan Musulmi
Allah Ta’ala Yana cewa “Ku yi riko da igiyar Allah (addinin Allah da LittafinSa) gaba daya, kada ku rarraba (kamar yadda na gabaninku suka rarraba), ku tuna ni’imar Allah a gare ku, yayin da kuka kasance makiyan juna (kafin Musulunci), sai Ya hada zukatanku (da Musulunci) kuka zamo ’yan uwa da ni’imarSa, kun zamo a […]
Allah Ta’ala Yana cewa “Ku yi riko da igiyar Allah (addinin Allah da LittafinSa) gaba daya, kada ku rarraba (kamar yadda na gabaninku suka rarraba), ku tuna ni’imar Allah a gare ku, yayin da kuka kasance makiyan juna (kafin Musulunci), sai Ya hada zukatanku (da Musulunci) kuka zamo ’yan uwa da ni’imarSa, kun zamo a gefen wuta, sai Ya tserar da ku daga ita. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyinSa don ku shiryu.” (Suratul Al- Imrana).
Hasbunallahu wa ni’imal wakil, rudi da dimauta da rikicewar da duniyar Musulunci ke ciki ya sa wannan ayar ta zamo tamkar shafaffiya, ko (kamar) ba a ma saukar da ita ba, in ka riski ki da kiyayya da kulli da kullaci da shagala da juna da saki reshe-kama-ganye da zagi da cin mutunci da bidi’antawa da kafirtawa a tsakanin Musulmi, sai ka zaci hakan cika umarnin ayoyi da Hadisan Annabin Rahama (SAW) ne, alhali hakan hannun-riga yake da su.
Makiya Musulunci, safe da rana a tafe ko a zaune da karfi da karfensu da tunani da iliminsu, sun kafu ne ba-ji-ba-gani kan kokarin kawar da Musulunci daga doron kasa.
Duk da sabanin da ke tsakanin Yahudu da Nasara, sukan dunkule don musguna wa Musulmi.
Bincike na dada fito da hanyoyin da suke bi wajen murkushe addinin Musulunci. Misali a 1978, sama da shugabannin addinin Kirista 150 ne suka hadu a birnin Fulorida don tattaunawa kan yadda za a Kiristantar da duniyar Musulmi. An gabatar da makala 40 a kan yanayin Musulmi a duniya da yadda za a juyar da su, tare da samar da gidauniyar gudanar da aikin. Ta irin wannan gidauniyar ce, suke samun damar kafa makarantu da asibitoci da coci-coci da daukar nauyin malamansu da suka sadaukar da kansu kan irin wannan aiki.
A nan Najeriya, Kungiyar Kiristoci (CAN), tana kokarin hade kalmar Kiristoci da game kungiyoyinsu, suna buga miliyoyin littattafan batanci ga Musulunci da kira zuwa ga Kiristanci da mabambantan harsuna kamar Larabci da Hausa da Ingilishi da Fulatanci (baya ga kananan harsuna, kuma wannan shi ne babban aikinsu a duniya kaf). Kuma kullum za ka samu aikinsu a duk kafar yada sadarwa: shafin yanar gizo(an samu wani shafi da wani Ba’amurke da ya kira kansa da Christian ya kirkiro sunan sura Like It, wai sura kamarsa, yana martani ga kalubalen da Allah Ya ba kafirai kan su zo da sura kamar irin ta Alkur’ani. Ya yi soki-burutsunsa, wanda dan-dagaji a Larabci zai kyalkyala wa dariya ko ya fashe da kuka, don irin yadda ya ci mutuncin Larabci. Amma wai Kur’ani aka kwaikwaya.
Ga jaridu kamar abin da aka samu a kasar Denmark wata jarida mai suna Jyllands-posten ta yi wani zane da nufin wai Annabi (SAW) ta zana (Allah Ya la’ance su). Kuma kwanakin baya ma mujallar Charlie Hebdo ta Faransa ta kwatanta makamancin haka da aka samu masu kishin Musulunci suka yi rugu-rugu da ofishinta.
Gidajen rediyo kuwa (ko a nan Kano, akwai kafar da suke yada addininsu). Ga jibintar marayu inda sukan je gidajen marayu su debe su koda irin ’ya’yan da muke cewa shegu ne tun suna yara kanana, su tarbiyyantar da su kan kafirci, mu kuwa ba mu gano hakan ba. Ga ziyartar marasa lafiya ta bin asibitoci don daukar nauyin marasa lafiya da zuwa gidajen yari don fansar fursunoni da tallafa musu), amma mu kungiyoyinmu ba ruwansu da wannan sai fada a tsakanin juna.
Muna fada a tsakaninmu abokan gabanmu na fada da mu a ciki da wajen kasa.
Misali a kasar Switzerland ta kada kuri’ar hana gina husumiya a masallatai, kasar Faransa kuma ta hana sanya nikabi (duk don musguna wa Musulmi).
Ba mamaki a samu wani ya ce mu ma Musulmi ai muna irin wadannan ayyuka, to sai mu ce: su Kiristoci in suna yada addininsu ba ka iya gane dan wace mazhaba ne ke da’awar, tare da yawaitar mazhabobinsu, mu yau an wayi gari, mutum ne zai musulunta, amma babban kokarin malamin shi ne ya yi saurin lakkana masa Musulunci tare da bangarensa na addini, don kada ya yi sake ya zama ba nasa ba. Ko ka samu Musulmi ba ya farin ciki da musuluntar kafiri, don ya musulunta a hannun bangaren da ba nasa ba.
Wakilansu a siyasance, suna kyakkyawan wakilci ga addininsu, hakan yake ba su damar zuwa da batutuwa don musguna wa dokokin Musulunci, kamar hana aurar da kananan yara ta fakewa da dokar ’yancin yara da kokarin tabbatar da ilimin koyar da jima’i (sed education) da yunkurin tabbatar da halaccin auren jinsi daya (namiji ya auri namiji ko mace ta auri mace) da ta halatta karuwanci.
Abu mafi ban haushi da bayyanar da rashin ba addini muhimmanci a tsakanin Musulmi, shi ne yadda Hukumar WAEC a jarrabawar Hausa ta wasu shekaru da suka wuce, ta siffanta Musulunci da kauyanci.
Shi ya sa sai kafiri ya fitsare kafarsa ya gaya wa Ma’aiki (SAW) mummunar magana, a yiwo ca! A kansa don neman a yi masa hukuncin gobe-a-kuma, sai hukuma ta shiga tsakani, ya aminta, gobe wani ya kara, an yi barkatai, (a da ko carbi ka ce ya zaga, ba zai iya ba).
Abul-Warakat Ayagi
Raudhatur-Rasul, Ayagi Kano
07082460196