Game da jadawalin sunayen barayin Gwamnati

Ministan Yada Labarai, Alhaji Lai Mohammed ya saki wata nakiya mai dauke da bomaboman siyasa a makon jiya, a yayin da ya bayyana jadawalin dake dauke da sunayen wasu manyan ‘yan siyasa a karkashin gwamnatin da ta shude ta PDP su shida a ranar 30 ga Watan Maris. Jadawalin ya bayyana sunaye da lokaci da […]

Game da jadawalin sunayen barayin Gwamnati
Game da jadawalin sunayen barayin Gwamnati

Ministan Yada Labarai, Alhaji Lai Mohammed ya saki wata nakiya mai dauke da bomaboman siyasa a makon jiya, a yayin da ya bayyana jadawalin dake dauke da sunayen wasu manyan ‘yan siyasa a karkashin gwamnatin da ta shude ta PDP su shida a ranar 30 ga Watan Maris. Jadawalin ya bayyana sunaye da lokaci da kuma adadin kudaden da suka sace, sannan da inda aka karkatar da kudaden. 

Inda Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, wanda ya kasance a jerin sunayen ya baiwa ministan awowi 48 ya janye sunayen sannan kuma ya nemi afuwar wadanda abin ya shafa. Amma a maimakon haka, sai Alhaji Lai Mohammed ya ce, wadannan sunaye da aka saki din somin tabi ne daga cikin daruruwan sunayen da suke da su a jadawalin gwamnatin tarayya. 

Sannan ya sake sakin sunaye a karo na biyu a ranar Lahadi 1 ga Watan Afirilu, wadda ya kunshi jerin sunaye 23 wanda ya hado da sunan Tsohon Ministan Jiragen Sama, Femi Fani Kayode; tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetir, Diezani Alison Madueke da kuma tsohon Mai Bada Shawara kan Harkokin Tsaro, Kanal Sambo Dasuki. 

Haka kuma a cikin sunayen har da sanatoci uku masu ci, Sanata Stella Oduah da Sanata Jonah Jang  da kuma Sanata Peter Nwaboishi. Sauran sun hada da tsofaffin hafsoshin soja biyu, Laftanar Janar Kenneth Minimah da Laftanar Janar Azubuike Ihejirika; akwai kuma tsohon Hafsan Tsaro, Aled Badeh; da Adesola Amosun; da tsohon Ministan Abuja, Bala Mohammed; da tsohon gwamnan Jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu; da tsohon Ministan Kudi, Bashir Yuguda da tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Rasheed Ladoja. 

Sai kuma Cif Tom Ikimi; da tsohuwar Ministar Kudi, Nenadi Usman; da tsohon Magatakardan Shugaba Jonathan, Alhaji Hassan Tukur; da tsohon Sakataren Dindindin, Godknows Igali; da Aliyu Usman da tsohon mai taimakawa Kanal Sambo Dasuki, Ahmad Idris; da Benedict Iroha da wani makusancin Sambo Dasuki, Aliyu Usman Jawaz duk sun fado cikin jadawalin. 

Alhaji Lai Mohammed ya ce, “Me PDP ta yi zato bayan da ta kalubalanci gwamnatin tarayya da cewa idan ta isa ta bayyana sunayen barayin gwamnati? Suna zaton cewa batun barayin wasan yara ne? Ko kuwa suna zaton cewa ‘April fool ne’?” Ya kuma kara da cewa martanin da PDP ta yi game da sakin sunayen barayin cin karo ne da batun neman afuwar ‘yan Najeriya da ta yi gabanin hakan. Ko kuwa suna tsammanin za su ci gaba da wautar da ‘yan Najeriya ne don su sake dawowa kan mulki 2019 a bagas?. 

To sai ita ma PDP ta hamzarta sakin sunayen wadanda ta ce sun wawashe baitil malin kasar har mutum 50 cikin Jam’iyyar APC mai mulkin. Sunayen sun hada da Rotimi Amaechi da Timipre Sylba da Bukola Saraki da Sulliban Chime da Orji Kalu da Chris Ngige da Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Adamu da Abubakar Mohammed da Gwamna Simon Lalong da Sanata. Andy Ubah da Sanata Magnus Abe da Injiniya Dakuku Peterside da Malam Nuhu Ribadu da Murtala Nyako da kuma George Akume da sauransu. 

Wannan musayar abin da suka kira sunayen barayin gwamnati bai burge ba ko kadan, sai ma kara daga hankulan al’ummar Najeriya da lamarin ya yi a makon jiya. Duka da cewa PDP ta gudanar da gwamanti mai cike da ayoyin tambaya, bai ma dace wannan batun ya taso ba. Baya ga haka ma ayyana sunan mutumin da yake gaban kuto yana fuskantar shari’a a matsayin barawo saba wa doka ne. Muna kira ga Alhaji Lai Mohammed da ya yi kokarin mallakar zuciyarsa a koda yaushe, sannan ya rika bambance matsayinsa a jiya da kuma a yau. 

Ya kamata aikace-aikacen gwamnati su zama abubuwan da zai maida hankali akansu, saura kuma ya kyale wa Kakakin APC ya rika maida martani. Dukkan batutuwan da suka shafi ayyana sunayen barayin gwamnati da bayyana sunayensu abar wa masu magana da yawun jam’iyyun siyasa, yayin da shi kuma minista zai kasance a bisa kololuwar aiki bisa doka tare da dabbaka muhimman kudurorin da gwamnati ta sanya gaba wadanda za su amfani al’ummar kasa baki daya.

Idan har ta tabbata cewa wadannan mutane da aka bayyana sunayen nasu na gaban kotuna, ba a kai ga yanke mu su hukunci game da abinda ake tuhumarsu akansa ba, to fa za su iya amfani da wannan wallafa da Alhaji Lai Mohammed ya yi su kalubalanci kotuna a matsayin ba a yi musu adalci a shari’un da suke fuskanta ba. Sannan ba a abin burgewa ba ne ayi rika yin musayar sunayen barayi a gidajen jaridu. Abinda ake fatan gani daga gwamnati a lokacin yaki da rashawa shi ne ta nemi shaidu da kwararan hujjoji sannan ta gurfanar da su gaban kuliya cikin tsanaki har ta kai ga nasara. Bayan haka kuma babu wata jayayya da a samu game da wane barawo ne ko kuwa a’a.