Game da kalaman T.Y Ɗanjuma
Salam Edita, da fatan kana nan lafiya. Na shigo wannan fili ne domin yin Allah wadai da kalaman tsohon Ministan Tsaron Najeriya, Janar T.Y Ɗanjuma a kan Rundunar Sojan Najeriya. Babu shakka waɗannan kalaman nasa sun nuna ƙarara cewa yana ɗaya daga cikin dubban mutanen da ke yi wa zaman lafiyan Jihar Taraba da Arewacin […]
Salam Edita, da fatan kana nan lafiya. Na shigo wannan fili ne domin yin Allah wadai da kalaman tsohon Ministan Tsaron Najeriya, Janar T.Y Ɗanjuma a kan Rundunar Sojan Najeriya. Babu shakka waɗannan kalaman nasa sun nuna ƙarara cewa yana ɗaya daga cikin dubban mutanen da ke yi wa zaman lafiyan Jihar Taraba da Arewacin Najeriya baki ɗaya kutunguila. Don haka muna kira da babbar murya ga Shugaba Buhari ya ba da umarnin tuhumarsa bisa waɗannan miyagun kalamai da ya yi! Sa’annan idan har aka same shi da laifi to a yanke masa hukunci mai tsananin gaske. A ƙarshe muna addu’ar Ubangiji Allah Ya kawo mana zaman lafiya mai ɗorewa a Arewacin Najeriya Ya kuma tona asirin duk wadanda ke da hannu wajen ta da zaune tsaye komai matsayinsu a Najeriya.
Daga Ashiru Lawal Nagoma Ruwan Ɓaure (Ɗan kishin talaka) karamar Hukumar Gusau, Jihar Zamfara. 08139177665.