Game da kisan dalibai a Uturu
A kwanaki ne wasu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne suka yi wa dalibai biyu da ke karatu a Jami’ar Jihar Abiya kisan gilla. Bayan kisan kuma, sai marasa tausayin suka yi amfani da kawunan daliban a matsayin turakun golar kwallon kafa. Mamatan dai sunayensu Ebuka Nwaigbo da Samuel Ethelbert kuma kafin mutuwarsu, suna […]
A kwanaki ne wasu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne suka yi wa dalibai biyu da ke karatu a Jami’ar Jihar Abiya kisan gilla. Bayan kisan kuma, sai marasa tausayin suka yi amfani da kawunan daliban a matsayin turakun golar kwallon kafa. Mamatan dai sunayensu Ebuka Nwaigbo da Samuel Ethelbert kuma kafin mutuwarsu, suna zaune ne a rukunin gidajen Chi-Doo da ke kan titin Uturu zuwa Afikpo.
Bincike dai ya nuna cewa wannan ta’addanci ya biyo bayan wata rashin jutuwa ce da ta faru tsakanin kungiyoyin asiri biyu, kungiyar Burkina Faso da kuma kungiyar da aka fi sani da sunan Maafia. Kamar yadda rahotanni suka nuna, wani dan kungiyar asiri ta Burkina Faso ne mai suna Collins Agwu aka kashe a watan da ya gabata, shi ne su kuma suka sha alwashin daukar fansa kan ’yan kungiyar asiri ta Maafia, inda suka kashe masu membobi biyu a wannan lokaci. Su dai makasan, an ce sun je gidan ne a kan babura guda hudu, inda suka kutsa kai ciki da karfin tsiya, suka kashe daliban biyu, sannan suka yi awon gaba da gangunan jikinsu cikin buhuna, inda suka nufi filin wasan da ke kusa da kofar makaranta, inda suka yi amfani da su a matsayin turakun golar kwallon kafa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Abiya, Ezekiel Onyeke Udebiotu ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, Joshiak Habila ya ba sashn binciken laifuffuka na rundunar umurni da su shiga binciken al’amarin kai tsaye. Irin yadda aka wulakanta gawar mamatan nan biyu, wani bakin abin takaici ne da ba a taba ganin irinsa ba, tun da aka fara jin labarin ala’muran kungiyoyin asiri a kasar nan. Wannan kuma yana nuni ne da yadda daliban jami’a matasa suka kasance marasa tausayi a jami’o’in kasar nan. Musamman aika-aikarsu ta nuna yadda suka maida ran dan Adam ba a bakin komai ba. Don haka, ya kamata a yi duk abin da ya kamata domin yin hukunci ga wadanda suka aikata wannan gillanci, ta yadda abin zai zama darasi ga kininsu masu irin wannan tunani, wadanda suka dauki aikin kungiyar asiri wani abu a makarantun kasar nan.
Aika-aikar da kungiyoyin asiri ke gudanarwa a makarantu suna cutar da al’ummar da ke makwabtaka da manyan makarantun kasar nan. Manyan makarantun da ya kamata su kasance wurin koyo da koyarwa, wurin koya da’a da ilimi, amma wasu karkatattu sun mayar da su wajen da suke gudanar da karkatattun ayyukansu na assha. Baya ga kisan gilla, irin wadannan ’ya’yan kungiyoyi na asiri suna aikata fashi da makami, fyade, fasa gidaje da barazana ga al’umma da tsoratarwa ga malamai da takwarorinsu dalibai. Mafi yawan lokaci, ba su tashi aiwatar da ta’addancinsu, sai sun yi mankas da abubuwan maye da jirkitar da hankali. Suna amfani da muggan makamai da suka hada da wukake, adduna da bindigogi da sauran makamantansu.
Wasu dalilai da ke haifar da irin wadannan bara-gurbi sun hada da rabuwar auren iyaye, rashin kyakkyawar tarbiyya ko kuma shagwaba yara da wasu iyaye ke wa ’ya’yansu. Wani lokacin kuma dalibai maza da mata kan shiga aikin kungiyar asiri a sakamakon bacin rai na rashin cin jarabawa. Haka kuma, yadda jami’o’i a wani lokaci suke daukar daliban da ba su cancanta ba. Irin wadannan dalibai gami da rashin ingantattar hanyar tafiyar da makarantu, suke haddasa ka ga daliban da aka kora daga makarantun amma sun ci gaba da zama ba tare da an bibiyi abin da suke yi ba.
Ganin cewa wannan aika-aika na kungiyoyin asiri a makarantu, al’amari ne da ya shafi al’umma gaba daya, don haka magance su na bukatar hada hannu tsakanin al’umma, hukumomin makarantu, iyayen yara, kungiyoyin al’umma da ba na gwamnati ba, ’yan sanda da sauran dukkan hukumomin tsaro. Iyayen yara suna da gagarumar rawar takawa, wajen taka wa wannan mummunar dabi’a ta kungiyar asiri birki. Iyayen yara su rika bibiyar yaransu domin su gane abubuwan da suke aikatawa, ta yadda za su dawo da su hanya, da zarar sun ga sun fandare daga hanyar kwarai. Iyayen su daina yi wa ’ya’yansu rikon sakainar kashi, su rika kula da bukatunsu daidai gwargwado, kuma su rika tattaunawa da su domin fahimtarsu da kwantar masu da hankali yadda ya kamata, tare da ba su shawarwari nagari da suka dace da rayuwa.
Ya kamata hukumomin makaranta su karfafa samar da kayayyakin wasanni domin shakatawar dalibai da hana su shiga ayyukan da ba su dace ba. kungiyoyin dalibai da sauran kininsu, lallai ne su tsaro da gangami da hanyoyin fadakarwa, yadda za a rika yaki da kungiyoyin asiri a makarantu. Lallai ne a rika ilimantarwa da fadakarwa ga dalibai, ta yadda za su gane illolin da ke tattare da kungiyoyin asiri a makarantu. Haka kuma, a fadakar da dalibai da malamai da sauran dukkan masu zama a makarantu, su rika fallasa wadanda suka fahimta da cewa suna gudanar da irin wannan kungiya ga jami’an tsaro. Ta haka za a rage ko ma a maganace irin wadannan munanan kungiyoyi da ke yi wa rayuwar matasa karan-tsaye a manyan makarantun kasar nan.