Game da sabon kudin wutar lantarki da cire tallafi kan lantarki
Ministan Makamashi, Alhaji Saleh Mamman, ya sake bayyana niyyar Gwamnatin Tarayya ta amincewa da sabon kudin wutar lantarki da zai fara aiki a ranar 1 ga Afrilun bana. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin za ta tsayar da bada tallafin da take ba bangaren lantarkin, saboda gazawar da kamfanonin rarraba wutar lantarkin (DISCOs) suke nunawa ta […]
Ministan Makamashi, Alhaji Saleh Mamman, ya sake bayyana niyyar Gwamnatin Tarayya ta amincewa da sabon kudin wutar lantarki da zai fara aiki a ranar 1 ga Afrilun bana. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin za ta tsayar da bada tallafin da take ba bangaren lantarkin, saboda gazawar da kamfanonin rarraba wutar lantarkin (DISCOs) suke nunawa ta bangaren yin amfani da kudaden da ke ba su.
Mamman ya ce ya riga ya gabatar wa Majalisar Zartaswa ta Kasa bayanan yadda DISCos suka kasa amfani da tallafin da ake ba su wajen sayen wutar lantarki tare da raba ta ga jama’a daga kamfanonin samar da wutar lantarkin GenCos.
A halin yanzu, DISCOs sun kasa sarrafa kusan megawatt 13,000 da GenCos suka tanadar musu, ko da cewa megawat 7,000 ne ake turowa daga wancan adadi, DISCos sun biya kashi 15 ne kawai cikin 100 na megawat 3,000 da suke rabawa.
Wannan ke nan yana nuna irin asarar da GenCos ke yi domin ba sa samun komai daga wutar da suke samarwa. Sannan kuma jama’a ba sa samun isasshiyar wutar lantarki da ya kamata su samu duk kda kokarin da GenCos suke yi.
Da yake tsokaci kan irin kokarin da gwamnati ta yi don tallafa wa wannan bangare ya tsaya da gindinsa, Ministan cewa ya yi “Gwamnati ba za ta kara bada tallafi ba,saboda abin da suke yi, za su karbi megawat 3,000 sai su biya na megawat 1,000 kawai. Wanda yake kashi 15 ke nan cikin 100 suke biya na abin da suka karba, gwamnati ce kuma za ta biya musu sauran, ba za mu sake lamuntar wannan ba.
Yanzu mun fito da wani sabon salon na maganar masu bukatar saye da kuma masu son sayarwa. Ka san akwai samar da wutar da ba za mu iya ma dauka ba sam. Yanzu mun ce wa GenCos, misali muna biyan kashi 15 cikin100 na lantarkin da suka samar; to ina za mu kai sauran kashi 85 cikin 100? Ko da Kamfanin Kula da Harkokin Wutar Lantarki (Nigeria Bulk Electricity Trading (NBET PLC) yana karbar kashi 100 cikin 100, bangaren iskar gas kawai yana daukar kashi 60 cikin 100, yayin da kashi 15 cikin 100 ke tafiya wajen gudanar da harkokinsu. NBET na sayen lantarki daga DISCos , sannan ya ba GenCos sannan ya karbi kudi daga DISCos kuma ya biya GenCos. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka samu gibi kuma shi ne dalilin da ya sanya dole mu yi wani abu a kai,” inji shi.
Daga wadannan bayanai da Ministan ya yi ya tabbatar da cewa har yanzu da sauran rina a kaba a kan tsarin da suka yi wanda dan Najeriya zai samu wadatacciyar wutar lantarki. Bayaninsa yana nuna dole sai an dauki wani mataki don gwamnati ta tsayar da tallafin da take bayarwa nan da 1 ga watan Afrilu 2020 in har ana son ta daidaita lamuran. Kuma wannan matsayi da Ministan ya dauka yana nuna ’yan Najeriya na dab da fadawa cikin duhu.
Abin da Najeriya ke bukata a yanzu a bangaren wutar lantarki shi ne, daukar wani mataki mai tsanani kuma cikin lokaci. Ko da wannan na nufin gwamnati ta san yadda za ta yi da lasisin da ta ba DISCos tunda ana zaton an sayar da su ga ’yan siyasa kuma ’yan Jari-Hujja.
Amma wani abin da gwamnati ta yi shiru a kansa shi ne na fayyace cewa mazauna birane ana cajinsu kudin lantarki mai yawa yayin da su kuma mazauna karkara suke biyan kudi kalilan. Don haka a yanzu da ake kokarin cire tallafin, wannan na nufin za a azabtar da ’yan Najeriya a kan laifin da ba nasu ba na kasawar kamfanonin da ke samarwa da raba wutar ce wato DISCos da GenCos.
Kuma kowa ya san wannan matsala ta wutar lantarki ita ce ta yi wa tattalin arzikin Najeriya tarnaki kuma ta hana ’yan Najeriya masu basira baje kolinsu.
Don haka kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta shafa wa fuskarta toka ta zakulo hanyar da za ta ba ’yan Najeriya isasshiya kuma dawwamammiyar wutar lantarki. Wannan lokaci ne da ya kamata a tsaya a gyara irin kuskuren da aka yi a baya musamman na sayar wa abokai da ’yan uwa kadarorin gwamnati.