Game da zaben gwamnoni da wakilan majalisun jihohi

Gobe Asabar, 9 ga Maris, 2019, miliyoyin ’yan Najeriya za mu kara fita domin sauke nauyin da ke kanmu na zaben gwamnoni da wakilan majalisun jihohi wadanda za su mulke mu tsawon shekara hudu. Wadansu za su je su yi zaben tumun dare, wadansu kuma za su dace. Sai dai a ra’ayina, zaben gobe sauki […]

Game da zaben gwamnoni da wakilan majalisun jihohi
Game da zaben gwamnoni da wakilan majalisun jihohi

Gobe Asabar, 9 ga Maris, 2019, miliyoyin ’yan Najeriya za mu kara fita domin sauke nauyin da ke kanmu na zaben gwamnoni da wakilan majalisun jihohi wadanda za su mulke mu tsawon shekara hudu.

Wadansu za su je su yi zaben tumun dare, wadansu kuma za su dace. Sai dai a ra’ayina, zaben gobe sauki gare shi, domin kusan an riga an ga kamun ludayin akasarin gwamnonin, saboda haka duk wanda ya yi zaben tumun dare, shi ya so .

A 2015, an yaudari mutane da yawa, amma ban da ni ciki, domin a koyaushe ina kokari in yi taka- tsantsan in ga wani dan siyasa bai yaudare ni ba.

Sai dai ga dukan alamu, ire-irenmu ba su da yawa. Wadansu ba sa koyon darasi, yanzu haka gobe a rude, ido rufe za su je su dangwala wa wanda ya share shekara hudu yana wasa da hankalinsu.

Ba zan ce ga wanda za ku zaba gobe in kun je akwatunanku ba, tunda ni ba dan siyasa ba ne, sai dai zan yi kira kamar haka:

MATA: Don Allah don son Annabi, kakanninmu, iyayenmu, yayyenmu, kannenmu da ’yan uwanmu mata, ku daina sayar da ’yancinku.

Mun sani yadda ake bi gida- gida ana raba muku kayayyakin da ba su taka kara sun karya ba kamar sabulun wanka, sukari, abinci, gidan sauro da ’yan kudade, don Allah ku daina yin zabe bisa wannan dalili. Hakan ba kawai kuna zubar da darajar da Allah Ya yi muku ta mata ba ce, sai ma sayar da ’yancinku, da ba da hadin kai wajen zaben shugabannin da ba su da kirki, wadanda za su cutar da al’umma ne kawai.

Ku tuna duk inda ake gudun hijira ku ne, kun fi kowa tagayyara lokacin rikicin siyasa, addini ko kabilanci, ku ne ake tauye wa hakki a kasashe masu tausowa kamar Najeriya.

Ba zan manta ba, a 1990, an yi babban taron matan duniya, a Beijing kasar Sin, inda aka amince cewa kasashen duniya za su rika ware wa mata kashi talatin na mukaman siyasa da na aikin gwamnati. To amma abin bakin ciki, ba a ba ku wannan ba, kun ki hada kanku, ku tabbatar ana ba ku wannan kaso, maimakon haka, kun biye wa ’yan siyasa suna wasa da hankalinku, suna ba ku dan abin da bai kashe babun yini guda. Don Allah ku farka, ku zabo nagartattun wakilai gobe, wadanda za su kare martabarku.

Muna da ’yan takara mata, me zai hana ku jaraba su? Ai ciwon ’ya mace na ’ya mace ce.

MATASA: Ga dukan alamu har yanzu da sauran rina a kaba dangane da siyasar matasa duk da dokar NOT TOO YOUNG TO RUN, sai ga shi muna ganin ana amfani da matasa ana ta da tarzoma wurin kamfen, ana kone-kone da kashe-kashe .

Dubi ta’addancin da ya faru a Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano, inda wani dan siyasa ya ingiza matasa suka kashe bayin Allah da kone motoci da yawa. Dubi a Gombe yadda matasa ke kone-kone da kashe-kashe. Kazalika Jihar Ribas, Ebonyi, Abiya da Akwa-Ibom. To wallahi in dai haka matasa za su ci gaba da yi a siyasar Najeriya, gaskiya babu ranar da za su zama shugabannin gobe. Yaya za ku bari, miyagun mutane suna ba ku makamai da miyagun kwayoyi, kuna ta’addanci wai da sunan siyasa? Wannan wace irin siyasa ce haka? Hatta kasashen kafirai da Yahudawa ba su irin wannan bakar siyasa mai hura wutar kiyayya da gaba a tsakanin al’umma.

Gobe in Allah Ya kai mu, akwai gwamnonin  da zan so a ce sun fadi warwas, saboda yadda suka cuci jama’a, suka wulakanta ma’aikatan gwamnati tare da barnata kudaden tallafi da Gwamnatin Tarayya ta ba su. Suka wulakanta malaman makaranta da ma’aikatan kananan hukumomi da sarakuna, tare da raba kan al’umma da yadda suka yi kama-karya inda suka ci zarafin dimokuradiyya, tare da rikita siyasar jihohinsu. zan so a kawo karshen siyasar daula da ubangida.

Ya Allah duk mai niyyar wulakanta bayinKa in ya ci zabe, Allah Ka fara wulakanta shi.

Mu yi hattara gobe kada mu zabi ’yan amshin shata a majalisun dokokin jihohi.

Daga karshe muna fatan Allah Ya sa a yi zabe lafiya, a kuma mutunta dimokuradiyya da kuru’un jama’a.

 

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar  Unguwa Katsina

Babban Sakataren Kungiyar Muryar Talaka na Kasa 08165270879.