Game da zaben Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya!
Bayan gaisuwa da fatan alheri ga ma’aikatan wannan jarida mai albarka. A yau ina son tofa albarkacin bakina ne game da zabar Sanata Ahmad Ibrahim Lawal a matsayin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, ba bu shakka yanzu kam burin shugaba Buhari da jam’iyyarsa ta APC ya cika, duba da cewa jam’iyyar ta APC ta yi wa […]
Bayan gaisuwa da fatan alheri ga ma’aikatan wannan jarida mai albarka. A yau ina son tofa albarkacin bakina ne game da zabar Sanata Ahmad Ibrahim Lawal a matsayin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, ba bu shakka yanzu kam burin shugaba Buhari da jam’iyyarsa ta APC ya cika, duba da cewa jam’iyyar ta APC ta yi wa majalisar dattawan zawarcin Sanata Ahmad Lawal a matsayin wanda zai shugabanci majalisar a shekarar 2015, amma kasancewar wa’adinsa bai yi ba ya kasa samun goyon bayan sauran ‘yan majalisar, wannan ne ya baiwa Sanata Bukola Saraki, nasarar zama shugaban majalisar, a karshe kuma aka ci gaba da samun rashin fahimtar juna tsakanin majalisar zartaswa da ta dokokin, a karshe hakan ya haifar da tsaikon gaske dama koma baya a Najeriya.
To a yanzu burin APC dama shugaba Buhari ya cika, dan haka babu wani zancen baiwa mu ‘yan Najeriya hakuri illa mu gani a kasa kawai, duba da yanzu majalisar zartaswa da ta dokokin dan Juma ne da dan Jummai.
A karshe ina addu’ar Allah madaukakin Sarki ya kara kawo ci gaba da zaman lafiya ga kasarmu Najeriya ameen.
Daga Ashiru Lawal Nagoma Ruwan ‘Baure (Dan kishin talaka) jahar Zamfara a tarayyar Najeriya. 07086868025.
Barka da Sallah Aminiya
Assalamu alaikum ina amfani da wannan damar domin taya dukkanin ma’aikatan jaridar AMINIYA, hadi da dukkanin makaranta da masoyan jaridar barka da Sallah, da fatan Allah ya karbi ibadunmu, Yasa muna ganin wasu shekaru masu albarka, Allah Ya maimaita mana, ya yi wa rayuwarmu Albarka.
Daga Nura M. Mai Apple Gusau 08133376020.
Sakon taya murna ga Ahmad da Gbajabiamila
Salam Edita, don Allah ka bani dama in mika sakon taya murna na ga sabbin shugabannin majalisar Dattawa da na Wakilai, wato Ahmed Lawan, da Femi Gbajamiamila, da fatan zasu baiwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, goyon baya don ciyar da kasar mu gaba.
Daga Sani Mohammed Chindo. Unguwar karofin madaki a Bauchi 08030918913
Sabbin Shugabannin Majalisun Tarayya
Ya Allah muna rokon Ka da Ka dafawa sabbin shugabannin majalissun tarayya, Ya Allah Ka sa musu kishin Malam talaka a zukatansu, Ya Allah Ka basu damar aiki da Baba Buhari cikin aminci domin gina kasar mu ta gado. Masu fadin munanan kalamai ya kamata ku fadi alheri ko ku yi shiru.
Daga Nasiru K. Hadejia 08100229688.
Kira ga uwar Jam’iyyar PDP ta kasa
Ina kira ga uwar Jam’iyyar PDP ta Kasa da ta gaggauta kawo dauki ga Jam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa tun kafin masu takamar tasu ce su rusa ta ta hanyar korar wasu.
Daga Haruna Shuaibu Danzomo 08068704909.
Goron Sallah ga Aminiya
Barka da Sallah Editan Aminya da ma’aikatanku baki daya, ina muku fatan alheri Allah ya maimaita mana yasa mu a cikin bayinsa ’yantattu, ku huta lafiya. 08108003333
Kira ga Buhari a hada hannu da ’yan Majalisa
To shugaba Buhari, yanzu dai wadanda kake marawa baya ne suka samu nasarar zama shugabannin majalisar dokokin Najeriya, don haka bamu bukatar jin korafin ka na cewa ‘yan majalisa ne ke yi wa gwamnatin ka zagon kasa. Muna fatan zaka hada hannu dasu wajen kirkiro da muhimman ayyukan ci gaba ga ’yan Najeriya.
Daga Mahmud Salihu Kaura Namoda, Zamfara. [email protected]
Kira ga Gwamnati: A tallafa wa manoma da taki
Salam ina kira ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya don Allah ta yi kokarin baiwa manoma taki da iri akan lokaci ba sai lokaci ya kure ba, domin kara inganta harkar noma a kasa.
Daga A.U Shuwaki Jihar Kano 08063511575.
Muna goyon bayan kirkiro da Masarautun Kano
Salam, Edita muna goyon bayan wannan nadin Sarakunan Bichi, Karaye, Gaya, Rano Allah Ya taya su rike amanar talakawansu, kuma wannan ci gaba ne ga Kano, dan haka muna farin ciki Allah Ka shiryi masu mulki akan daidai.
Daga 08167481684.
Kira ga shugaban Najeriya da Gwamnan Kano
Assalam Edita da daukacin masoyan wannan Jarida mai albarka dan Allah ina san in yi amfani da wannan damar in yi kira ga shugaban kasa da Gwamnan Kano ganin yadda suka fi maida hankali wajan ramuwar gayya na lura ba talaka ne a gaban su ba.
Daga Barau Liman 08062862191.
Jinjina ga el-Rufa’i
Salam Edita, ina rokonka isar mani da jinjina ta ban girma ga mai girma Gwamna da rabin wani Gwamnan. Malam da rabin wani malam. Muna bayanka sai ka gaji Baba Buhari da Yardar Allah. M. A. El Rufa’i sai kayi.
Daga Ibrahim Malami Katsina 07062903579.
Kira ga Ganduje talakawa na cikin kuncin rayuwa
Edita ka bani dama in isar da sakona zuwa ga mai girma Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje wallahi talakawa suna cikin hali na kuncin rayuwa rashin aikin yi, ba a yin kokarin nemo mafita ba sai muji an kara masarautar jahar Kano kaso biyar Ya Allah Ka karemu daga azzaluman shugabanni ka taimaki al’ummar jahar Kano dama kasa baki daya naku Auwal Yunusa Sauna jihar Legas 08168238423.
Sakon Barka da Sallah
Salam Edita, dan Allah ka bani dama in yi mika sakon Barka da Sallah ga illahirin musulman Duniya da fatan an yi bukukuwan Sallah lafiya Allah Ya amshi ibadun mu da muka gudanar a watan Azumin Ramadan Allah Ya sa muna daga cikin ‘yantantun bayi salihai.
Daga Sani Mohammed Chindo. Unguwar karofin madaki a Bauchi tarayyar Najeriya 08030918913.
Kira ga Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Igabi
Assalam Edita ya ibada da fatan Allah Ya kabamana amin ina fatan za ka bani fili in yi kira ga Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Igabi a jihar Kaduna da ya yi wa Allah ya tashi a majalisa ya kawo kuduri a kan yawan buge mutane da motoci ke yi akan hanyar Kaduna zuwa Zariya domin manyan garuruwa takwas da ke kan hanyar duk a mazabarka suke sai ka nemo masu gadojin sama domin jama’arka su samu saukin wannan annoba ta yawan kashe mutane da motoci ke yi akan wannan hanya Kaduna zuwa Zariya Allah Ya baka ikon tashi ka gabatar da wannan kuduri amin.
Daga Sabo Kima Maraban Jos Kaduna 07031102553.
Kira ga gwamnati a kan samar da takin zamani
Salam! Edita ka bani dama in yi kira ga hukumomin kasar nan musamman ma jahohi da kuma gwamnatin tarayya akan lamari noman damina dangane da farashin takin zamani mai rahusa da kuma inganci akan lokacin da manoma ke bukatar shi. Noma yana daya daga cikin hanyoyin da mutane ke dogara da kawunansu domin samun ingantattar rayuwa, muna kira ga gwamnati da ta kawo wa manoma daukin taki akan lokaci.
Daga Auwal Abubakar Dandagoro, 08039254822.
Allah Ya dada tsare mana Baba Buhari
Asalam Aminiya ina muku fatan alheri, rokona shi ne Allah Ya dada tsare mana Baba Buhari da mukan mu baki daya.
Daga 08108406818.
Kira ga Gwamnatin Bauchi
Tuni kan koken dana yi batun gyaren hanyar Ningi zuwa Burra, wallahi, akwai wata gada idan ba’ayi gyara ba, sai in mun koma ta jihar Kano da Jigawa kenan kafin mu shiga Karamar hukumar wato Ningi jihar Bauchi kenan!.
Daga Hassan Ibrahim Warji 08121899959
Sarakuna ku nisanci siyasa
Assalam, Aminiya, don Allah ku sanarwa iyayen mu Sarakuna su nesanta kansu da siyasa, idan har suna son su tsira da mutuncinsu. Ina goyon bayan karin masarautun jahar Kano, amma ban goyi bayan rashin baiwa masarautar Kano shugabancin majalisar Sarakunan jahar Kano ba.
Daga M. Mohammed, Abuja 07062337888.
Fatan alheri ga sabon Sarkin Karaye
Assalamu alaikum Edita AMINIYA dan Allah ku bani dama na mika wa Mai martaba Sarkin Karaye sakon fatan alheri da murna Allah Ya taya ka riko amen.
Daga Nazifi Hassan Sani Gwarzo 08066926647.
Sakon gaisuwa ga Sarkin Kano
Salam Editan Aminiya, Don Allah a mika min sakon gaisuwata zuwa ga Sarki Mai Adalci, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na 11 ya daure ya ci gaba da rikon sarautar shi kuma zalunci baya dorewa kaikum mulki lokaci gareshi yaugareka gobe gawa ne .
Daga Mai A.C Kogo Kofar Kudu 09030466517.
Jinjina ga Dakta Suleiman Mudi
Salam Edita ka ba ni dama in mika godiya da jinjina ga Dakta Mudi Daraktan Gwarzo Zone 4. bisa sahalewarsa na gyaran asibitin Kabo da ake yi, sakamakon barnar iska da aka samu. Allah Ya sa ka fi haka.
Daga Isah Mato Bichi. 08062212290.