Gamin Gambizar Halayya
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan sinadaran sarkakkiyar soyayya da kuma yadda za a warware sarkewar da suka haifar cikin auratayya. Allah Ya sa wannan bayani […]
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan sinadaran sarkakkiyar soyayya da kuma yadda za a warware sarkewar da suka haifar cikin auratayya. Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Sinadari na 2: Gamin Gambizar Halayya
Gamin gambizar halayya na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da sarkewar soyayya tsakanin ma’aurata, komai irin yadda ma’aurata suke son junansu, idan hali bai zo daya ba, ko aka samu bambanci mai fadin gaske a cikin gundarin halayyarsu, to kullum za su kasance ko dai cikin yawan gardandami da jayayya, ko kuma su zauna cikin tsami da yawan share juna.
Ma’anar Halayya
Halayyar mutum ta kunshi gaba dayan dabi’unsa, yanayin tunaninsa da kuma shau’ukansa da yadda yake bayyanar da su a wurare da kuma lokuta daban-daban. Duk wata dabi’a da mutum yake yawan maimaitawa to a hankali za ta zama halinsa, dunkulewar halayen mutum ke zama halayyarsa. Kamar yadda Hausawa kan fada wai hali zanen dutse (mai wuyar kankarewa), to haka abin yake a kimiyyance, domin binciken masana kimiyyar halayya ya tabbatar da cewa duk wani hali da mutum ya yi shekaru ashirin a cikinsa, to zai yi tsananin wuya a iya raba mutum da wannan halin. Babu mutane biyu da ke da halayya iri daya cif-da-cif komai irin kusancinsu ko kamanceceniyar dabi’unsu kuwa. Kowane mutum yana da dimbin dabi’u da halaye daban-daban, amma akwai wata dab’i, wani hali da ke jan kowane dan Adam da suka sa ya fita daban da sauran mutane kuma da wannan hali ne mutane suka san shi.
Tasirin Halayya Cikin Soyayyar Ma’aurata
Idan aka sami akasi halayen ma’aurata suka sha bamban sosai da juna, ko suka yi kusa sosai da juna, nan da nan wannan matsala ke fitar da wutar soyayyar ma’aurata daga cikin zuciyarsu. Kamar yadda Hausawa ke fadin cewa ‘wai sai hali ya zo daya ake abota,’ wannan haka yake musamman a abota irin ta rayuwar aure, amma zuwan dayan ba kodayaushe ne yake haifar da abota ba, kamar yadda sha bamban mai yawa kan iya haifar da matsala, to haka ma idan hali ya zo daya sosai gab-da-gab zai haifar da matsala; Misali: ‘Idan aka sami maigida da uwargida dukansu masu nisan hakuri ne, halinsu ya zo daya zuwan da zai haifar da alfanu cikin soyayyarsu; amma kuma in ya kasance dukkansu masu gajen hakuri ne, halinsu ya zo daya zuwan da zai haifar da matsala cikin soyayyarsu.
Kamar sauran muhimman abubuwan cikin rayuwar aure, bambancin halayya kadai ba ya haifar da matsala ga soyayya, amma irin yadda ma’aurata suka mu’amalance shi ne ke zama matsala. Bayan zaman aure ya fara nisa, ma’aurata za su ga wasu halaye ko dabi’un da ba su yi masu ba game da junansu; maimakon su yi hakuri da wadannan halaye kamar yadda suka aminta da sauran halaye ko dabi’un da suka yi musu din, da yawan ma’aurata na yin kuskuren daukar matakin da bai kamata ba, wanda wannan shi ke haifar da sarkewar soyayya cikin rayuwar aurensu. Wasu ma’aurata sai su fara jin haushin juna a dalilin wannan, ko su ji sun tsani juna, wasu kuma sai su rika kokarin son canza junansu daga wannan dabi’a da ba ta yi masu ba, wadanda duk ba su kai su ga warware matsalar sai dai su kara haifar musu da wasu matsalolin.
Yadda Za a Warware Wannan Matsala
Ma’auratan da suka fahimci cewa bambancin halayya ne ke kawo matsala cikin mu’amalar soyayyarsu, sai su bi wadannan hanyoyin don warware matsalolinsu:
1. Ma’aurata su sani cewa dole halayensu da bukatunsu da sha’awowinsu su sha bamban da juna, don haka ba ya yiwuwa miji ya ce dole sai matarsa ta canza daga halin da ta girma a kai ta koma yadda yake so, haka ma mata bai kamata ta bukaci wannan daga maigidanta ba, ko sun yi kokarin canzawa, ba za su iya ba, kuma takurawa ga juna da cewa dole sai mutum ya canza halayyarsa ba abin da yake yi sai haifar da sarkewar soyayya tsakanin ma’aurata. Hali zanen dutse bai goguwa take yanke, in kuwa aka ce za a kankare shi da tsiya, to tabbas sai an kankaro har da jikin dutsen, don haka hakuri, kyautatawa da kwatantawa cikin siga mai kyau za su fi alfanu a kan duka wani mataki da ma’aurata za su dauka. Mummunan dabi’a da ta saba shari’a da hankali kadai ce za a dauki zazzafan mataki a kan ta.
2. Sannan Ma’aurata su tuna cewa aure ya fi muhimmanci sama da komai a rayuwarsu; domin yawancin ma’auratan da suka sami kansu a cikin irin wannan matsala ta bambancin halayya, sukan ba wannan hali ko dabi’a da ba su so muhimmanci sama da dorewar zaman lafiyar aurensu; sai ya kasance abin da bai kai ya kawo ba yana yawan haddasa fitina a tsakninsu; da yawa abubuwan da ke haifar da fitina har su kai ga mutuwar aure in an duba za a ga ko kama kafar muhimmancin auren ba su yi ba. Ma’aurata su tuna da cewa zamantakewar auratayyarsu ta fi muhimmanci sama da komai a rayuwarsu, don haka duk wani abu da zai kawo barazana ga dorewar zaman lafiyarsu bai kamata su ba shi muhimmanci ba. Su tuna cewa auren nan fa ibada ce, kuma ibada ana yinta duka a cikin tsanani da cikin dadi.
3. Hakuri da Kyautatawa: Ma’aurata su sani duk irin yadda suka so da tafiyar ko canza wani hali da ba su so wa junansu, to yawan korafi, mita, jin haushi da nuna tsana a fili ba shi ne magani ba, kyakkyawan hakuri da kyautatawa su ne hanyoyin da za su iya magance wannan matsala. Amma yawan korafi da mita sai dai su kara dagula matsala tare da haifar da wasu ma, a hankali sai zama ya yi tsami sosai ta yadda duka ma’auratan ba za su rika jin dadinsa.
4. Koyi da Sunna: Daga cikin dimbin Hadisan Manzon Allah SAW da suke bayani kan kyautata zamantakewa, hadisi daya kadai idan ma’aurata suka rike shi ya isa ya kawar masu da wannan matsala ta bambancin halayya tsakaninsu. Misali:
• “Imanin dayanku ba ya cika sai ya so wa dan uwansa abin da yake so wa kansa.” Maimakon jin haushi da yawan korafi, sai ma’aurata kodayaushe su auna su ga idan su ne ke da irin wannan matsala ya suke son a yi musu? Na tabbata ba za su so a dame su da yawan korafi da jin haushi a kan wata halayyarsu ba, amma idan aka yi hakuri, ko da halayyar nan ba ta bace ba, to ba za a kasance cikin kuncin zuciya da bacin rai ba a dalilinta.
5. Haka kuma in kowannensu ya sauke nauyin auratayya da shari’a ta dora masa, to bambancin halayya ba zai iya haifar da baraka ba cikin auratayyarsu.
Sai sati na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.