Gamin Gambizar Halayya 1

Assalamu alaikum, a wannan mukalar in sha Allah zan yi tsokaci gwargwadon fahimtata a kan ’yancin mata ne, wanda a Yammacin Turai ake yawan kururuta cewa ana danne hakkin mata musamman a kasashen Musulmi. A tawa fahimtar ’yanci wata kalma ce wadda da zarar dan Adam ya ji ta, to hakika zai ji wani farin […]

Gamin Gambizar Halayya 1

Assalamu alaikum, a wannan mukalar in sha Allah zan yi tsokaci gwargwadon fahimtata a kan ’yancin mata ne, wanda a Yammacin Turai ake yawan kururuta cewa ana danne hakkin mata musamman a kasashen Musulmi.
A tawa fahimtar ’yanci wata kalma ce wadda da zarar dan Adam ya ji ta, to hakika zai ji wani farin ciki a birnin zuciyarsa, domin yana ganin zai samu adalci da walwala ba tare da an tsangwame shi ba.
An sha yin farfaganda a kan kalmar ’yanci musamman na mata tare da alakanta kalmar da tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewa, misali a Yammacin Turai an sha tafka muhawarori masu zafi a kan ’yancin mata tun kafin karni na ashirin 20, a lokacin ana matukar kuntata wa mata a Turai, domin ana hana su mallakar duk wata kadara; a hana su yin zabe a mulkin dimokardiya; a hana su mallakar kayan gado, sannan an dauke su tamkar wadansu halittu marasa daraja.
kungiyoyin masu fafutikar kwato ’yancin mata sun fara gwagwarmayar neman ’yanci tun a cikin karni na 19, a yayin da suka fara bayyana neman ’yancinsu a karo na farko a bayyanar jama’a a birnin Paris da ke kasar Faransa, wato a lokacin da ake taron duniya a kan hakkin bil Adama, sai dai duk da haka mata a Turai ba su samu ’yancin yin walwala daga mazajensu ba har sai lokacin da tattalin arzikin Turai ya fara tumbatsa, lokacin da kamfanoni suka fara yawaita sai suka karkata ga daukar mata aiki, domin samun sauki wajen biyan ma’aikata, inda mazaje suka dinga shan wahala wajen samun ayyukan yi a kamfanoni, musamman a Birtaniya, sai kuma duk jikinsu ya yi sanyi tare da fara sauraren koke-koken mata na samun ’yancin walwala, duk da haka ba su samu ’yanci ba sai a tsakiyar karni na 20. Bayan an gama yakin duniya na biyu  a 1948 ne sai majalisar dinkin duniya ta bayyana ’yancin mata  na ba su duk wata dama kama daga mallakar duk wata kadara da samun rabon gado da ’yancin warware  aurensu a duk lokacin da suka ga dama ko da ta hanyar shari’a ce.
Wannan ’yancin da mata suka samu a Turai a tsakiyar karni na 20 duk shi ya jawo tabarbarewar tarbiyyarsu, domin suna sanya sutura yadda suka ga dama, sukan yi yawo a gari daga su sai dan kamfai, sukan auri junansu ba tare da tsangwama ba, sukan zubar da ciki a duk lokacin da suke bukata. Ya ’yan uwana mata shin wannan ne ‘yancin kuke bukata? A halin yanzu mata sun kafa kungiyoyin fafutikar kwato ’yancinsu musamman a Arewacin Najeriya, to a tuna cewa wanne ’yanci ne Musulunci bai ba mata ba?
Matan Turai da kuke hankoron samun ’yanci irin nasu ba su san ’yancin walwala ba sai a tsakiyar karni na 20, ’yancin da nake ganin ya yi kama da ci gaban mai hakar rijiya; ’yancin da ya sa suke wahalar da kawunansu wajen yin gogayya da mazaje a wajen aikin ofis ko na karfi, kana su rika da’awar cewa duk abin da namiji ya yi to mace ma za ta iya wata kila fiye da na namiji.
Za mu ci gaba insha Allah.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi