Ganawa da mawakin zamani Hafizu C.K.

Hafizu Abdullahi Ibrahim wanda aka fi sani da ‘Cikar Kamala’ (CK), a hirar da ya yi da Aminiya ya bayyana al’amuran da suka shafi rayuwarsa da wakokinsa: Takaitaccen tarihinsa:An haife ni a Kurna cikin Jihar Kano a 1987. Na yi karatun firamarena a Makarantar Tudun Fulani Islamiyya. Bayan na kammala sai na samu shiga Makarantar […]

Ganawa da mawakin zamani Hafizu C.K.

Hafizu Abdullahi Ibrahim wanda aka fi sani da ‘Cikar Kamala’ (CK), a hirar da ya yi da Aminiya ya bayyana al’amuran da suka shafi rayuwarsa da wakokinsa:

Takaitaccen tarihinsa:
An haife ni a Kurna cikin Jihar Kano a 1987. Na yi karatun firamarena a Makarantar Tudun Fulani Islamiyya. Bayan na kammala sai na samu shiga Makarantar Sakandire ta Aliya. Na yi shekara biyu a wannan makaranta sai na samu sauyi zuwa G.S.S Gwammaja. Bayan na kammala aji uku na karamar sakandire sai na samu shiga Makarantar G.S.S Kurna, inda na kammala aji shida a wurin. Daga wannan lokaci sai na fara harkar waka a matsayin sana’a. Bayan wasu shekaru kuma sai na koma Makarantar Koyon Aikin Gona ta Audu Bako wacce ke danbatta, inda a halin yanzu a nan nake karatu, ban kammala ba.
Yadda aka yi ya fara waka:
Na fara waka ne a 2005, kodayake tun kafin wannan lokaci na dan jima da fara waka tun ina makarantar sakandiren Aliya. Zan iya tunawa, akwai wani malaminmu na Adabi, yana koya mana yadda ake rubuta waka da kuma ka’idojinta. Da farko da Larabci yake koya mana amma daga baya sai ya koma koya mana da Hausa don mu fi ganewa. A wannan lokaci har aiki yake ba mu, ya nemi mu je gida mu rubuto wakoki da kanmu. Da yake dama ina da sha’awar waka sai ya zama tun daga wanann lokaci na fara rubuta wakoki nawa na kaina har kuma na rera su yadda nake so.
bangarorin da yake wa waka:
Nakan yi wakokin yabon Annabi ko kuma wasu lamurra na rayuwa da sauransu. Ina taba kowane bangare da ya shafi fadakarwa da ilimintarwa da nishadantarwa. Haka kuma akan gayyace mu gidan biki inda mukan yi wakokinmu a wurin. Sai dai ni salon wakata yakan tafi ne.
A kan hawa da sauka abin da ake kira da Turanci ‘hippop’ wato yadda mawaki zai rika jero kalmomi yana fadar su da sauri kuma da karfi sosai.
Adadin wakokinsa:
Zan iya cewa a yanzu haka wakokin da na buga za su kai 56. Su kuwa wadanda na rubuta ban kai ga bugawa ba a gaskiya ban san yawansu ba. Tunda a koyaushe idan na sami sukuni nakan dauki takarda da biro na rubuta waka.