Ganawa da Ubangiji cikin raka’a biyu (1)

Yadda za ka yi sallah cikakkiya cikin tsoron Allah da kusanci a gare Shi.

Ganawa da Ubangiji cikin raka’a biyu (1)

Annobar coronavirus ta tilasta wa masallata bayar da tazara tsakaninsu a sahun Sallah.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai. Mai nuna mulki Ranar Sakamako.

Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa Ranar Hisabi.

Bayan haka, hakika malamanmu sun karantar da mu cewa Sallah ganawa ce a tsakanin bawa da Ubangijinsa, kuma mu yi tattalin yadda za mu gana da Shi.

Dan uwa ka dauka za ka je ganawa da sarkin garinku ko gwamnanku ko Shugaban Kasa, shin haka za ka tafi wannan ganawa ba tare da sanin abin da za ka fada masa ba?

Shin haka za ka je ganawar ba ka kintsa ka shirya wa ganawar ba?

Shin haka za ka je ganawar ba tare da ka tsara bukatun da za ka gabatar masa ba?

Idan haka ba zai yiwu ba, yaya za ka gana da Rabbil Izzati ba tare da ka kintsa ka tsara yadda za ka gana da Shi ba?

Shin ka taba tsayawa ka yi tunani kan yadda kake ganawa da Ubangijinka?

Shin kana ganawa da Shi ta yadda kake fahimtar abin da yake gudana a tsakaninka da Shi, ko kawai kana zuwa ne ka gana da Shi (SWT) ba tare da ka san abin da ka fada maSa ba?

A yau, za mu dauki raka’a biyu kacal daga cikin raka’o’i 17 da Allah Ya wajabta mana domin ganawa da Shi a kullum.

Za mu yi misali da Sallar Asuba mai raka’a biyu don ganin shin yaya ake ganawa da Ubangiji har a samu dacewa.

Idan har kana yin Sallah biyar din nan da aka wajabta maka, amma ba ka fahimtar cewa kana ganawa kai-tsaye ne da Ubangijinka, to lallai sallarka akwai tasgaro, ko kuma ma ba Sallah kake yi ba.

A matsayinmu na Musulmi duk wanda zai yi Sallah, abu na farko da ake bukata shi ne ya kasance mai tsarki, tsarkin jiki da tsarki daga masu bijirowa, ma’ana a tsarkaka daga janaba da haila da jinin biki ga mata, sannan a tsarkake jiki ta hanyar alwala da tufafi da wurin ibadar.

Mu dauka duk mun cika wadancan ka’idoji, wadanda hakika akasarinmu ba mu cika su din.

Mu dauka mun yi alwala yadda ta kamata, mu dauka mun kammala komai ga mu nan mun yi sahu za mu gana da Ubangijinmu.

Shin me kalmomin da muke fara furtawa suke nufi?

Mun ce Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Me wadannan kalmomi biyu na farkon Ikama suke nufi? Mun san ma’anarsu ko dai kawai muna fadi ne kamar yadda muka ji sauran mutane suna fadi?

Idan mun sani alhamdu lillah, kalmomin suna nufin Allah ne Mafi girma! Allah ne Mafi girma!!

Shi ke nan abin da ake so mu fahimta? Ina! Allah ne Mafi girma, kalma ce da take da nauyi. Kalma ce da take nufin Allah ne Mafi girma daga duk abin da yake cikin sammai da kasa.

Allah ne Mafi girma daga duk abin da na mallaka. Allah ne Mafi girma daga duk abin da nake nema a duniya. Allah ne Mafi girma daga iyayena da matana da ’ya’yana da duk abin da yake bayan kasa! Don haka na watsar da su na mayar da hankalina gare Shi!

Shin haka muke kaddarowa da hararowa a zukatanmu a lokacin da ladan yake Ikama yana cewa “Allahu Akbar! Allahu Akbar!!?” Ko kuwa muna jin kalmar ce kawai muna kuma tunanin mun bar shago ga abokan ciniki suna jiranmu, ko mun bar aiki kaza a kan teburi ko jirginmu yana daf da tashi ko ko ko… tambayoyi birjik a zukatanmu?

Shin mun yarda Allah ne Mafi girma daga duk abin da muke so a daidai lokacin da muka tsaya a gabanSa?

Bayan wannan sai kalma ta gaba “Asshhadu an la’ilah illallah, Asshhadu anna Muhammadar rasulullah.” Shin mun san ma’anar wannan kalma da muke fada ko dai kawai mun iya furta ta ce ba tare da sanin ma’anarta ba?

Idan ba mu sani ba, ba ma jin kunyar tsayawa a gaban Allah, mu fadi abu game da Shi ba tare da mun san ma’anar abin da muke fadi ba?

Wannan kalma nanata alkawari ne cewa “Mun tabbatar babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma mun tabbatar Annabi Muhammad Manzon Allah ne.”

Shin a yayin da muke fadin wannan kalma muna hararowa cewa a gaban Masanin boye da fili muke magana?

Muna tuno shin da gaske mun yarda kuma mun tabbatar babu abin bautawa da gaskiya sai Allah?

Shin mun yarda kuma mun amince Annabi Muhammad Manzon Allah ne?

Wadannan kalmomi biyu kalmomi ne masu nauyi domin a kansu addini ya ginu.

A koma gaban malamai a yi ta karatu don sanin su da aiki da abin da suke nufi.

Kalma ta gaba duk da cewa gamu a tsaye a sahu amma ana cewa “Hayya alas salah, hayya alal falah!” Ma’ana mu yi gaggawa zuwa ga Sallah, mu yi gaggawa zuwa ga babban rabo. Mene ne sirrin fadin haka bayan mun riga mun hau sahun Sallah?

Manufar ita ce mu tattaro hankalinmu mu yi watsi da duniya da abin da yake cikinta, mu mayar da hankalinmu wajen ganawa da Allah Ubangijinmu. Mu natsu mu tuna muna tsaye ne a gaban Masanin abin da zukata suke boyewa!

Don haka, idan har da sauran gafalalle da ya shiga sahu, ana tunatar da shi cewa ya mayar da hankali ga Sallah, ya mayar da hankali wajen samun babban rabo!

A karshe sai a sake tunatar da masallata cewa “Kad kamatis salatu.” Ma’ana “Sallah ta tsayu.” An fice daga wannan duniya da tarkacen da yake cikinta an yi watsi da komai nata na dukiya da mata da ’ya’ya da komai an koma wata duniya ta ganawa da Allah Madaukaki.

Don haka kafin kabbarar harama don fara Sallah sai a sake tunatar da mai Sallah cewa “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! La ilaha illallah.” Ma’ana: “Allah ne Mafi girma! Allah ne Mafi girma. Kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah!”

Da wadannan kalmomi ana fata duk wanda zai yi Sallah ya bar wannan duniya tamu ya koma duniyar mala’iku. Ba zai yi kowane abu da zai saba wa Ubangiji ba, ba zai kalli girman komai ba in ba na Allah ba.

Ba zai, ba zai…” Babu kowa a gabansa sai Allah Ubangijin bayi.

Daga nan sai ya kabbara ya ce “Allahu Akbar!” Allah ne Mafi girma! Cike da natsuwa da kankan da kai a gaban Masanin abin da yake boye a cikin zukata.