Ganawa ta musamman da Alhaji Aminu Dantata

Hira ta musamman da babban attajiri Alhaji Aminu Dantata game da rayuwarsa da wasu muhimman abubuwa

Ganawa ta musamman da Alhaji Aminu Dantata

Alhaji Aminu Alhassan Dantata

Aminiya ta yi tattaki zuwa gidan fitaccen attajirin nan na Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, a unguwarsu da ke Koki, a birnin Kanon Dabo.

Mai kimanim shekara 89, kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dantata, sanye da farar taguwa da babban riga a dakin tarbar baki a gidan ya karbi bakuncin ayarin jami’an Kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Daily Trust da Aminiya da suka hada da; Mukaddashin Babban Jami’in Gudanarwar  Kamfanin, Malam Nura Mamman Daura da Babban Edita, Naziru Mika’ilu, da Manajan Shiyyar Kano, Malam Yusha’u Ibrahim, wadanda suka je don neman izinin tattaunawa ta musamman da shi a matsayinsa na wanda ya ga jiya ya kuma ga yau.

Yana cike da kwarjini kuma yanayinsa ba ya nuna shekarunsa, kamar yadda tunaninsa na nan daram, ba tare da rudewa ba, domin yana tuna abubuwan da suka faru a shekarun 1950 da kafin nan cikin sauki da sauri.

Cikin hikima Alhaji Aminu Dantata ya bayyana cewa shi ba ya tattaunawa ta musamman da ’yan jarida domin a cewarsa, mahaifinsa da yayyensa duka babu wanda ya taba yin hira da ’yan jarida a rayuwarsu, don haka ba zai zama farau ba.

Sai dai ya ba da dama a yi hira irin ta yau da kullum, inda a ciki za a iya tsintar abin da za a iya bugawa a jarida, kuma hakan aka yi.

Ku biyo mu don jin yadda ta kaya.

 

Dantata matafiyi:

An fara tattaunawar ce kan tafiye-tafiyen Alhaji Aminu Dantata zuwa kasashen ketare.

Wasu daga cikin irin wadannan tafiye-tafiye na kasuwanci ne, wasu kuma ba haka ba.

Tun wajejen 1956, Alhaji Aminu Dantata ya karade kusan manyan kasashen duniya da suka hada da Austireliya da Indiya da China da Brazil da Yugoslabia da Rasha da sauran kasashe.

A wajajen 1961 kuma Alhaji Aminu Dantata ya kewaye kasashen Larabawa gaba dayansu da kuma kasar Isra’ila.

Alhaji Aminu Dantata ya bayyana cewa a lokacin ko kasashe irin su Saudiyya ba za su nuna wa Najeriya arziki ba.

Ya ce ko a lokacin gine-ginen nunawa a garuruwan Makka da Madina ’yan kadan ne.

“A duk lokacin da muka tafi Saudiyya don yin aikin Haji a farkon shekarun 1950 zuwa1960, mahukunta a kasar Saudiyya ba sa son mu dawo gida da wuri don burinsu a lokacin kawai shi ne mu tsaya mu yi ta kashe kudi a kasar”, inji shi

“Hikimarsu ta jinkirta dawowarmu ita ce iya tsawon dadewarmu a kasar iya kashe kudin da za mu yi kuma wannan a wurinsu yana kara musu kudin shiga.

“Sun saba sukan rike mana fasfo da sauran takardunmu da zarar an kammala aikin Haji”, inji shi.

Ga mutum mai yawan tafiye-tafiye irin Alhaji Aminu Dantata, ya ga sauye-sauye a tashoshin jirage dama da irin yadda suka canja.

Alal misali, a farkon shekarun 1950 ginin filin jirgin saman Sarkin Abdul’aziz da ke Jiddah an yi shi ne da itatuwa, ba ginin zamani ba, kuma ofisoshi kadan ne kawai suke ginannu.

A wancan lokaci filin jirgin saman duniya na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano na ganiyar shahararsa don a lokacin jirage na tashi a filin a-kai-a-kai zuwa kasashe irin su Ghana da Saliyo da sauran kasashen Nahiyar Afirka inda nan ne ’yan wadannan kasashe ke yada zango.

Sai dai babban abin takaici, kamar yadda ya bayyana, shi ne yadda al’amura suka tabarbare inda al’amuran cigaba a yankin Arewacin Najeriya suka fuskanci gagarumar koma-baya.

Ba wannan ba kawai, babban abin da ya fi bata wa Alhaji Aminu Dantata rai shi ne yadda kasashen Turai suka yi amfani da arzikin kasashen Afirka suka azurta tare da gina  kasashensu.

“Arzikinmu suka diba suka gina kasashensu da shi.

“Sun kwashi kayayyakin amfanin gonarmu da ma’adinanmu da sauran albarkatun kasa zuwa kasashensu.

“Ba su bar mu a yayin da suka mulke mu ba sai da suka tabbatar sun dora mana nasu a kanmu, suka daure mana hannayenmu don ganin mutanenmu ba su iya tabuka wa kansu komai da zai bunkasa mana kasashenmu ba.

“Kalli misalin Jihar Kano inda kafin zuwan Turawa, Kanawa ke gudanar da harkokin kasuwanci da na addini da kasashen Larabawa irin su Moroko da Tunisiya da Sudan.

“Amma lokacin da Turawa suka shigo mana suka ga yadda muke gudanar da addininmu na Musulunci da harkokinmu na kasuwanci da sana’o’inmu da muke dogaro da su, ba ina baki saboda kasancewata mutumin Kano ba ne, amma zan iya cewa a duk fadin Najeriya babu garin da ya kai Kano wayewa saboda mu’amala da Larabawa.”

Dangantaka tsakanin shugabanni da ’yan kasuwa

Alhaji Aminu Dantata na daya daga cikin kafaffun ’yan kasuwar da suka tsayu da kafafunsu wanda kuma duniya ke yi da shi. Ya kasance mutum mai nasibi da shugabanni ke damka masa amana. Sai dai alakar da ke tsakanin shugabanni da ’yan kasuwa ba kowane lokaci ne take zama da dadi ba musamman a mahaifarsa Jihar Kano, inda yake tunanin ya kamata alakarsu ta zamo mai karfi sosai. A irin gogayyarsa da kwarewarsa, Alhaji Aminu Dantata yana ganin dangantaka tsakanin ’yan kasuwa da shugabanni lamari ne da yake zama ginshiki ga ci gaban kasa, kamar yadda ya ga haka a wasu kasashe.

“Kamfanoni da masana’antu na samuwa ne ta hanyar kasuwanci, wanda ta nan ne kuma sauran jama’a za su rika gudanar da harkokinsu na kasuwanci kuma ta nan shugabanni za su samu damar jan ragamar talakawansu tare da bunkasa al’umma ta fuskoki daban-daban,” inji shi.

Raguwar tasirin Jihar Kano, a ra’ayinsa, na daga sakamakon balbalcewar dangantaka a tsakanin shugabanni da ’yan kasuwa a jihar. “Ni ban san a ina matsalar take ba. Shin daga bangaren ’yan kasuwar ne ko daga shugabanni? Shugabanninmu ba sa lura da ’yan kasuwarmu sai dai a suna kawai. Shugabanni na tunawa da ’yan kasuwa ne idan suna bukatar wani abu daga gare mu kuma a batun gaskiya ba haka abin ya kamata ya zama ba idan har ana so komai ya tafi daidai,” inji shi.

Dalilin da na ki tsayawa takarar Shugaban Kasa

Harkokin siyasa da na kasuwanci sun kasance suna tafiya kafada-da-kafada da juna, ta yadda a karshe za ka ga dan kasuwa ya rikide zuwa cikakken dan siyasa kamar yadda Shugaban Amurka, Donald Trump da kuma tsohon dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar SDP a nan kasar, MKO Abiola suka yi.

Alhaji Aminu Dantata dai ba ya kallon kansa a matsayin dan siyasa duk da ya dan taba kadan.

Ya taba zama dan Majalisar Wakilai a Kaduna a Jamhuriya ta Farko.

Bayan kifar da gwamnatin da sojoji suka yi ne ya dawo Kano inda Gwamnan lokacin a zamanin mulkin Janar Yakubu Gowon, Alhaji Audu Bako ya ba shi mukamin kwamshina a gwamnatinsa.

Alhaji Aminu Dantata ya bayyana yadda wadansu fitattun mutane suka yi ta kawo masa tayin tsayawa takarar Shugaban Kasa a Jamhuriyya ta Biyu a zaben da Alhaji Shehu Shagari ya zama Shugaban Kasa, yayin da wadansu irin su marigayi Malam Aminu Kano suka shawarce shi ya fito takarar Gwamnan Jihar Kano a lokacin.

“Amma dalilina na kin amsa kiraye-kirayen da ake ta yi min a lokacin a fili yake.

“A matsayina na dan kasuwar da ke da tulin dawainiya a gabana, na gamsu cewa kasuwancin shi ne hanyar da Allah Ya zabar mini kuma zan yi iyakar kokarina wajen ganin na taka muhimmiyar rawa don ci gaban jihata da kasata da al’umma baki daya.

“Don haka na ga ba ni da wani dalilin shiga siyasa kuma”, inji shi

Alhaji Aminu Dantata, wanda a lokuta da dama yake kawo ayoyin Kur’ani da hadisai a cikin tattaunawar tare da wasu karantarwa na Musulunci don karfafa matsayarsa, ya kawo misalin Hadisin da ya yi bayanin wadansu mutane uku da suka hada da shugaba da malami da mai kudi idan daya daga cikinsu ya ki sauke nauyin da Allah Ya dora masa zai gamu da mummunar makoma a Ranar Kiyama, kamar yadda duk wanda ya sauke nauyin da Allah Ya dora masa a cikinsu zai gamu da kyakkyawan sakamako daga Ubangiji.

Koyar da jikansa yadda zai yi amfani da kwakwalwarsa

Alhaji Aminu Dantata yana da ’ya’ya da jikoki da yawa.

Ya bayar da labarin wata ganawarsa da daya daga cikin jikokinsa.

“Ina tattaunawa da daya daga cikin jikokina yayin da muke dawowa daga masallaci sai ya ce min Baba, lokaci ya yi da ku tsofaffin nan za ku kyale mu (yana nufin kansa da sauran sa’o’insa) don ci gaba da gudanar da abubuwa.

“Kwakwalwarku ta tsufa, ya kamata ku ba mu wuri mu dora.

“Gaskiya, na girgiza da maganarsa sai dai ban nuna masa hakan ba.

“Sai dai na yanke shawarar in yi masa gyara tare da canja shi daga wannan tunani da yake kai.

“Don haka lokacin da muka dawo gida sai na fada wa matata wato kakarsa abin da ya faru tsakaninmu.

“Na fada mata cewa zan nuna masa cewa kwakwalwata tana aiki.

“Sai muka yanke shawarar cewa duk lokacin da ya zo gare ta, to ta turo shi don ya gana da ni.

“Bayan mun yi wannan magana da kakarsa sai na daina yi masa wasa.

“Bayan kwana biyu sai ya lura cewa na canja masa fuska.

“Rana ta uku sai ya je wurin kakarsa ya sanar da ita cewa na yi fushi da shi, don haka yana neman ta shiga maganar, amma sai ta fada masa cewa ba za ta iya shiga maganar ba tunda tun farko babu ita a maganar.

“Wata rana muna zaune a dakin hutawa da sauran iyalaina sai ya tayar da maganar.

“Ya ce min Baba alamu sun nuna cewa ba ka ji dadin maganar da na fada maka ranar ba.

“Ina so in sanar da kai cewa maganar da na yi wasa nake yi, irin na kaka da jika, idan na bata maka rai ina neman afuwarka”.

“Sai na ce masa “Na taba yi maka wasa?

“Na kyale ka ne kai da kwakwalwarka mai aiki ce ka yi abin da ka ga dama a rayuwarka tunda dai tawa kwakwalwar ba ta aiki kamar yadda taka take yi. Don Allah kada ka sake tunanina.

“Abin mamaki, yaron da ni na tura shi kasar waje ya yi karatu, na gina masa gida na sama masa aikin yi na kuma yi masa aure shi ne zai fada min cewa kwakwalwata ba ta aiki.

“Abin da zai ba ka sha’awa shi ne ’ya’yan masu kudi a wannan zamani sun dauki dabi’ar danganta iyayensu da ma’ajiyarsu, ma’ana iyayen nasu suna ajiye wa ’ya’yansu dukiyarsu ce.

“Mu dawo ga maganarmu a kan jikana, sai na yi amfani da wannan damar da muke zaune da iyalina don in koya masa hankali a rayuwarsa don kuma ya canja tunaninsa.

“Wadannan ne matsalolin da suke damun al’ummarmu a yau. Yawancin matasa suna da wannan tunani”, inji shi.

A kan halaye marasa kyau a tsakanin matasa

A matsayinsa na wanda ya ga jiya ya ga yau, wanda ya ga al’ummomi daban-daban wadanda suka canja,  Alhaji Aminu Dantata ya damu da yadda tarbiyyar al’umma take a yau.

Manya da aka san kanana da su tana dusashewa, idan har ba a yi maganin abin ba, to za ta jefa al’ummarmu masu tasowa cikin matsala a nan gaba.

Ya bayyana cewa a lokacin da suke samari, suna girmama manya ba tare da la’akari da inda suka fito ba.

“Gaskiya abubuwa ba su tafiya yadda suka kamata a cikin al’ummarmu saboda dusashewar gaskiya da rikon amana a tsakanin matasan Najeriya, kuma idan abubuwa suka ci gaba a yadda suke, Allah ne kadai Ya san abin da zai faru ga wadanda ba a haifa ba, saboda lamarin yana kara baci a kullum,” inji shi.

Tabarbarewar rashin amana wani abu ne da ya dami Alhaji Aminu Dantata saboda yana da labarai game da tafiye-tafiyen da ya yi a shekaru masu yawa da suka gabata lokacin yana manaja a Sakkwato wanda kuma ya sanya dole ya rika yin tafiye-tafiye a garuruwan da ke yankin.

Yana iya tuna yadda gaskiya da rikon amana suka yi tasiri a lokacin da motarsa ta lalace a kan titti.

“A kowane lokaci idan na hadu da wata matsala irin wannan sai dai kawai in sanar da maigari cewa motata ta samu matsala kuma akwai kudi a ciki.

“Ina tabbatar maka mai garin zai sa wanda zai yi gadin motar har zuwa lokacin da makanike zai zo ya gyara motar koda kuwa za a dauki kwana uku ko kwabo ba zai bata ba a cikin kudin da ke motar. Sai dai abin ba haka yake ba yanzu,” inji shi.

Saboda yadda dabi’un kwarai suka lalace da suka sa Alhaji Aminu Dantata jin tsoro, lamarin ya kai yanayin da ya bar mutanen da suke son yin gyara cikin rudanin rashin sanin ta inda za su fara.

“A matsayin shugaba mutane za su tunkare shi da manufofi daban-daban. Wadansu da kyakkyawar niyya wadansu kuma da mummuna.

“Ko da shugaba yana da kirki yana kuma da kyakkyawar niyya ta yin abubuwa daidai, to, ina kuma bangaren mutanen da suke tare da shi? Su ma suna da kirki kamarsa? Wannan matsala ce,” inji shi.

A cewarsa ya tabbata neman hanyar warware wadannan matsaloli ya ta’allaka a kan mutanen da suke tunanin canja hanyoyin da za a gina Najeriya.

Amana da kishin kasa dole su ne abin da za su zama linzamin mutum.

Saboda damuwa da halin da Arewa ke ciki Alhaji Aminu Dantata ya ce dole a kula da sha’anin samun ilimin boko da na addini.

Yakar rashin da’a nauyi ne da ke kan kowa musamman gwamnati da malaman addini da masu rike da sarautun gargajiya da ’yan kasuwa da kuma shugabannin al’umma wadanda ya shawarce su da su zo su ceto kasar nan kafin a makara.

“Kamata ya yi a fara komai daga gidajenmu da makarantunmu da wuraren ayyukanmu da kasuwanni.

“Abin ba dadi ganin yadda dabi’u masu kyau suke bacewa musamman a tsakanin matasanmu kuma idan har ba mu yi maganin abin ba, ba za mu iya samar da shugabanni nagari a nan gaba ba.

“Ba za kuma mu samu abin da muke nema wajen gyara kura-kurenmu ba”, inji shi.

“Ku ma ’yan jarida kuna da rawar takawa.

“Ya kamata ku sake dagewa wajen ayyukanku wajen ilimintarwa da nishadantarwa da wayar da kan al’umma saboda kafafen watsa labarai suna da rawar takawa wajen dawo da kyawawan halaye a tsakanin ’ya’yanmu masu tasowa a kasar nan.

“Dole in yaba wa shugabannin Kamfanin Media Trust game da yadda suke yin gaskiya a rahotanninsu.

“Ina kuma kira ga shugabannin kamfanin su mayar da hankali wajen yin rahotanni kan yadda za a dawo da kyawawan dabi’u a tsakanin matasan kasar nan, saboda a matsayinsu na shugabannin gobe, ya kyautu a ce matasan suna da kyawawan halaye.

“Ya kamata mu yi wani abu don ciyar da harkar ilimi gaba.

“Idan ka auna irin daliban da jami’o’inmu suke kyankyashewa a yanzu za ka yarda cewa muna fitar da abin da bai nuna ba, saboda yawancin matasanmu suna da ilimi amma ba su da kyawawan dabi’u.

“Don haka me kake tsammani daga wurin irin wadannan yara? Yaya kake tunanin za su fitar da mu daga kangin da muke ciki?”

Yadda ya hadu da kura a wajen neman kudi

Alhaji Aminu Dantata na  daya daga cikin tsofaffin masu arzikin da ake maganarsu, har yau a Najeriya, kuma ya fara neman kudi ne tun yana matashi.

A lokacin da yake matashi, Alhaji Aminu Dantata bai taba jin kunyar yin duk wata sana’a da za ta kawo masa kudi ba.

Ya ce duk wani abu da mutumin da ke zaune a kauye yake yi, domin ya samu kudi, ya yi a lokacin da yake matashi.

Ya ce ya yi kananan sana’o’i da dama da ake yi a kauye, tun daga sayar da ruwa da sayen kayan amfanin gona duk ya yi.

Alhaji Aminu Dantata ya yi tafiye-tafiye zuwa garuruwa da kauyuka da dama a Arewacin Najeriya, don sayen gyada da sauran kayan amfanin gona.

Ya ce a wadannan tafiye-tafiye da ya yi, wata rana wani abu ya faru da shi, wanda ba zai taba mantawa  ba.

Wannan abu kuwa shi ne wata rana da daddare ya hadu da kura a lokacin da ya je Daura, don sayen  kayan amfanin gona.

Ya ce yana kwance a dakin da ya kama na jinka, bayan ya gama sayen kayan gona, yana kwance a dakin da daddare, sai yaji motsin dabbobi, a bayan dakin.

Da ya leka waje sai ya ga ashe kura ce, take kokarin shigowa dakin.

A lokacin ya firgita, amma Allah cikin ikonSa kurar ba ta samu damar shiga dakin ba, balle ta ji masa ciwo.

Har ila yau ya ce lokacin da yake matashi ya taba fuskantar matsala da ’yan siyasa, lokacin da ya je kauyen Rogogo da ke Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano.

“Yadda abin ya faru shi ne a lokacin da na je kasuwar wannan kauye ina sayen kaya, akwai wani dan tsohuwar Jam’iyyar NPC da ya je kauyen, don yakin neman zabe.

“Sai ya je kasuwar  garin ya kafa tutar jam’iyyar a shiye-shiryensa na yakin neman zabe.

“Amma sai mutanen kauyen suka mayar da hankalinsu, ga harkokin kasuwancin da ake yi a kasuwar, maimakon su mayar da hankalinsu ga gangamin yakin neman zabe da ake shiryawa.

“Sai wannan dan siyasa ya yi tsammanin ni na shirya yadda mutanen kauyen suka ki kula su.

“Don haka sai ya je ya yi kara ta wajen mahaifina, cewa na dauki hayar wadansu matasan kauye sun kai musu hari lokacin da suke yakin neman zabe.

“Nan take mahaifina ya aiko mini, cewa in tafi fadar Hakimin Bichi in roki gafara, kan abin da na yi.

“Nan take na bi wannan umarni na mahaifina.”

Alhaji Aminu Dantata ya yi bayanin cewa daga nan, maimakon direban motar da ya kai shi Bichi, ya dawo da shi kauyen na Rogogo ya sauke shi, sai ya ga ya kama hanyar zuwa Kano da shi.

Sai ya tambayi direban dalili, sai direban ya shaida masa cewa umarnin da mahaifinsa ya ba shi ke nan.

Ya ce lokacin da suka isa Kano, sai mahaifinsa ya tambaye shi dalilin da ya sanya wadansu matasa suka kai wa ’ya’yan Jam’iyyar NPC hari.

Nan take ya shaida wa mahaifin cewa shi bai aikata haka ba. Daga nan sai mahaifinsa ya yi masa gargadi, kan ya guji tsoma kansa cikin harkokin Jam’iyyar NPC.

Ya ce mahaifin nasa ya yi masa bayanai da dama kan siyasa da al’amuran ’yan siyasa da shugabanni da rayuwa baki daya.

Ya ce babu shakka ya karu da abubuwa da dama, kan bayanan da mahaifin nasa ya yi masa.

Alhaji Aminu Dantata ya nuna takaicinsa, kan yadda aka rufe masana’antu da dama a jihohin Kano da Kaduna, wanda hakan ya yi sanadin rasa aikin dubban matasa.

Ya ce babban dalilin da ya kawo rufe wadannan masana’antu, shi ne rashin kula da mayar da hankali daga masu masana’antun.

Alhaji Aminu Dantata ya tabbatar da cewa yana da hannayen jari a kusan dukkan masana’antun da suke aiki a kasar nan.

Ya ce yana da hannayen jari, a dukkan kamfanonin da suke aiki a Kano da Kaduna sama da shekara 20.

A yayin da masu kudi da shekaru irin na Alhaji Aminu Dantata suke tunanin su je su huta.

Shi kuwa a halin da ake ciki yanzu yana nan yana shirye-shiryen sake bude Masakar Fine Ted Tedtile da ke Kaduna, wadda yake da kashi 87, na hannun jarin masakar.

Har ila yau a matsayin Alhaji Aminu Dantata na mai shekara 89 a duniya, a yanzu ya shirya sanya jari a harkokin noma, inda ya shirya noma babbar gonarsa da ke garin Kura a Jihar Kano, mai fadin eka 5,000.

Ya ce ya shirya zai noma shinkafa da masara don bunkasa samar da abinci a kasa da samar da ayyukan yi, ga al’umma.