Ganawar Jonathan da iyayen ’yan matan Chibok

Bayan wata uku da sace ’yan mata ’yan makaranta a Chibok ganawar da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi da iyayensu kwanakin baya tamkar ihun ne bayan hari inda ya haifar da shakku kan manufa da martabar ganawar Shugaban kasar da bakinsa.Jim kadan da sace ’yan matan a watan Afrilu ’yan Najeriya da suka damu […]

Ganawar Jonathan da iyayen ’yan matan Chibok
Ganawar Jonathan da iyayen ’yan matan Chibok

Bayan wata uku da sace ’yan mata ’yan makaranta a Chibok ganawar da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi da iyayensu kwanakin baya tamkar ihun ne bayan hari inda ya haifar da shakku kan manufa da martabar ganawar Shugaban kasar da bakinsa.
Jim kadan da sace ’yan matan a watan Afrilu ’yan Najeriya da suka damu wadanda suka lura da rashin katabus din Shugaban kasar na ya kai ziyara zuwa Chibok, sun bukace shi da ya yi haka cikin gaggawa a matsayin wata hanya ta tausar iyayen yaran tare da ba su tabbacin cewa gwamnatinsa ta tashi tsaye domin tabbatar da ta dawo musu da ’ya’yansu cikin koshin lafiya. Amma Shugaban kasar ya shashantar da bukatar, sai ya zabi zuwa kasar waje domin amsa gayyatar wasu abubuwa maimakon ziyartar Chibok, lamarin da ke nuna rashin muhimmanci da ya ba wa batun. Wannan ya nuna cewa kodai Shugaban kasar ya dauki batun a matsayin tatsunniya, ko kuma bai damu da gagarumar matsalar da ake ciki ba – cewa wasu miyagu sun sace dimbin ’yan mata domin nuna bakin halinsu da irin hadarin da suke da shi kuma suna shirye su yi komai a yakin da suke yi da al’umma.
Duk fadin haka, yanzu da Shugaban kasa ya gana da iyayen ’yan matan Chibok da dattawansu duk da dai ba a Abuja ne ba a Chibok ba, ya fara nuna nuna damuwa game da batun sace ’yan matan, musamman a matsayinsa na uba ya ji koke da damuwar das ace ’ya’yansu da karfin cin tuwo daga makaranta aka tsare su a wani wuri ba da son ransu ba suka jefa su a ciki.
Shugaba Jonathan ya yi amfani da wannan dama wajen musanta zargin da ake yi wa gwamnatinsa na kasa yin komai don ceto ’yan matan kamar yadda jama’a suke gani. Game da wannan ya kamata ya zargin kansa kan yadda tun farko ya rika nuna halayen ko in kula kan lamarin.
’Yan Najeriya sun yi farin ciki kan alkawuran da ya rika yi wa iyayen a lokacin ganawar cewa nan ba da jimawa ba kowa zai yi murna saboda ana aiki don ganin an sako dukkan ’yan matan kuma yana bukatar su ci gaba yin “hakuri da nuna fahimta da ba da hadin kai.”
Sakamakon bayyana damuwarsu da halin da suka shiga a wata uku da suka gabata kai-tsaye ga Shugaban kasar, ba dukkan iyayen yaran ne za su jure wa wannan bukata ta kara hakuri ba. Kuma yadda ake ta kiraye-kirayen nemo a sako ’yan matan kiran iyayen su ci gaba da nuna hakuri ba wani abu ne da za a ce bai dace ba.
Game da jan kafar da ake yi wajen ceto ’yan matan Shugaban kasar ya ce gwamnati na daukar matakan kwato ’yan matan, kuma ana taka-tsantsan domin dawo da su “da ransu cikin koshin lafiya.” Wannan dan bayani ya nuna ana jan kafa ne a aikin ceton saboda bukatar da ke akwai ta kauce wa halaka rayuka, hujjar da aka bayar don wanke sojoji da ake zargi da gaza ceto ’yan matan.
Shugaba Jonathan yana iya nuni da hakan cewa kada ’yan Najeriya su tsammaci wani yunkurin soja da sakamakonsa zai iya shafe maharan amma ya gaza kwato ’yan matan da rayukansu. A hakika, wannan hange ne na gaskiya da tausaya wa ran dan Adam – gaba daya dai, abin da ake son nunawa kada a auka wa inda ake garkuwa da ’yan matan da bindigogi a dawo hannu rabbana. Har yanzu dai a yayin da za a yi aikin cikin taka-tsantsan, kada a manta dogon jan kafa kansa kan iya jawo asara, musamman ga rayuwar dan Adam.
  Shugaban kasar ya kuma shaida wa iyayen cewa lura da halin da Arewa maso Gabas ta shiga an bullo da wasu hanyoyin farfado da tattalin arziki da inganta rayuwa, kamar shirin tallafa wa wadanda hare-hare suka shafa (bSF) da shirin kula da makarantu (SSI) da sauransu, inda za su fara aiki cikin sauri da zarar an ceto ’yan matan kuma an samu nasara kan Boko Haram.  
Lura da wahalhalun da ake fuskanta wajen magance matsalar, akwai yiwuwar a dauki dogon lokaci. Don haka aiwatar da shirye-shiryen ya kamata ya fara ne nan take, kafada da kafada da yaki da maharan. Kuma idan aka aiwatar da su cikin gaskiya da rikon amana da sadaukar da kai, akwai fatar amfaninsu ga al’umma zai kawo karshen ta’addan da matasan da suke cikin matsala kuma suke yakar jama’a.
Ko ma menen ne ta kowace hanya, ’yan Najeriya za su kama Shugaba Jonathan kan alkawarinsa ga iyayen Chibok cewa kwanan nan za a ’yanto ’ya’yansu.