Ganawar Marubuci Farfesa Yusuf Adamu da daliban Kwalejin Sa’adatu Rimi
A Ranar Lahadi (12-7-2015), daliban Sashen Hausa na Kwalejin Sa’adatu Rimi suka karbi bakuncin Farfesa Yusuf M. Adamu, tsohon shugaban kungiyar Marubuta ta kasa (ANA) reshe Jihar Kano. Taron ya gudana ne bayan daliban da ke (part time) na kwalejin sun yi nazari a kan littattafin Farfesan mai suna Idan So Cuta Ne, wanda aka […]
A Ranar Lahadi (12-7-2015), daliban Sashen Hausa na Kwalejin Sa’adatu Rimi suka karbi bakuncin Farfesa Yusuf M. Adamu, tsohon shugaban kungiyar Marubuta ta kasa (ANA) reshe Jihar Kano. Taron ya gudana ne bayan daliban da ke (part time) na kwalejin sun yi nazari a kan littattafin Farfesan mai suna Idan So Cuta Ne, wanda aka rubuta tun a shekara ta 1989.
Farfesa Yusuf Adamu na rubutu cikin harshen Hausa da Turanci, ya fitar da littattafai masu yawa wadanda suka hada da Ummul-Khairi da Maza Gumbar Dutse da Gumakan Zamani. A littattafansa na Turanci akwai Butterfly and Other Poems da Animal in the Neighbourhood da Landscapes of Poetry da They Can Speak English da A flat World da sauransu.
Taron ya kayatar matuka, domin ba ya ga marubucin, wasu daga cikin marubuta sun halarta wadanda suka hada da Zaharaddeen I. Kallah da Dokta Faruk Sarkin Fada da Kabiru Yusuf Anka. Sannan akwai da yawa daga cikin malaman Sashin Hausa na kwalejin, karkashin jagorancin Shugabar Sashin, Dokta Bilkisu Yusuf, wadda Dokta Mahe Isa Ahmed ya wakilta.
A yayin jawabin maraba, Dokta Mukhtar Sadauki ya sanar da cewa wannan rana ita ce rana ta karshe da daliban suka gama daukar darasi a kan wannan fanni, hakan yasa suka gayyaci marubucin littafin da aka nazarta wato Farfesa Yusuf M. Adamu don ya amsa tambayoyi daga daliban.
Farfesa Yusuf Adamu ba boyayye ba ne a bangaren rubuce-rubuce, domin yana daga cikin jiga-jigan da suka haifar da Adabin Hausa na zamani. Tun bayan da kamfanin wallafa littattafai na NNPC ya dakatar da buga littattafan Hausa, marubuta na wannan zamani suka shiga mawuyacin hali na rashin samun kafar da za su isar da sakonninsu. A cikin wannan hali ne marubuta irin su Talatu Wada da Farfesa Yusuf Adamu da Ado Ahmad Gidan Dabino da Sunusi Shehu Daneji da dan’Azimi Baba da su Balaraba Ramat da su Adamu Muhammad da Alkhamees D. Bature da Bala Anas Babinlata da sauransu suka jagoranci nakudar Adabin Hausa na zamani. Hakika zan iya cewa gudunmawarsu ta taka rawa wajen dawwamar da Adabin Hausa har ya zama a raye zuwa wannan lokaci. A yau idan ana maganar marubutan da suke rubutu cikin harshen uwa, yana cikin wadanda suka yi fice. Wannan abin alfahari ne ga duk mai kishin yare da al’ada ta Hausa.
Farfesa Yusuf, yayin gabatar da tarihinsa da tarihin fara rubuce-rubucensa, ya gabatar da yadda ya fara sha’awar sauraron labarai da tatsuniyoyi, wadanda sun taimaka wajen zamansa marubuci. A cewarsa, mahaifinsu kan dauke su lokacin hutu zuwa wasu garuruwa, inda bayan sun dawo yakan ummarce su da su rubuta abin da suka gani. Da haka ya fara rubutu, inda ya rubuta littafinsa na farko Maza Gumbar Dutse, sai kuma Idan So Cuta Ne… da ya rubuta shi a cikin mako guda. A cewarsa, har yakan zana yadda yake son wani abu daga cikin bayaninsa ya kasance ya yi rubutu.
Hakika wannan dan gajeran tarihi zai haska wa wadanda suke da sha’awar zama marubuta da su yi koyi da shi, su fahimci suna da baiwar rubutu. Na san da yawa daga cikin mutane suna da wannan baiwa amma ba su sani ba. Misali, akwai mutane da idan suna ba ka labari sai ka rantse suna nan aka yi abu, ko kuma ka ga wadanda ke da sha’awar sauraron tatsuniyoyi da labarai, babu shakka hakan na nuna cewa za su iya zama kwararrun marubuta.
Kamar yadda na ce a baya, taron ganawa da daliban ya yi armashi kwarai, domin ya ba su dama sun yi tambayoyi ga Farfesa sannan sun gana da wasu daga cikin marubutan Hausa. Hakan ya sa an yi musayar ra’ayi da fito da wasu muhimman bayanai a kan adabi. Daga cikin abubuwan da aka duba sun hada da alakar marubuci da labarin da ya rubuta. Wasu daga cikin mahalarta taron sun yi duba ga wannan bangare. Misali, marubucin Idan So Cuta Ne… dan boko ne wanda ya kai matsayin Farfesa, hakan ya yi tasiri a cikin littafinsa na amfani da ’yan boko a cikin taurarin labarinsa. Kusan kowa yana yin boko, illa wasu kalilan da ba ’yan boko ba wadanda su ma sun taka rawa wajen fito da jigon labarin.
An kawo misalai na Abdulmalik da Salisu da Zairo a wasu daga cikin ’yan book, sai kuma Hajiya Bilkisu a matsayin wadda ba ta yi boko ba, kuma hakan ya kawo matsala ga Abdulmalik da Farida a kan soyayyarsu.
Daga cikin abubuwan da daliban suka tambaya, har da abin da ya ja hankalin marubucin ya yi wannan littafin. Yayin ba da amsa, marubucin ya ce ya jima yana jin ana maganar duk wata soyayya da aka jima ana yi a karshe zai yi wuya a yi aure. Kasancewar yana da wacce yake so kuma sun jima tare sai ya fara tunanin abin da zai faru idan haka ta faru, wannan ne ya sa ya fara tunanin yadda zai ba kansa hakuri. Wannan ne ya sa ya rubuta littafin Idan So Cuta Ne…
daliban sun yaba wa marubucin a kan cewa an rubuta littafin tun 1989 amma sai a dauka a wannan lokaci aka rubuta shi. An kuma yaba masa yadda littafin ya kasance tsaftatacce da al’umma za su amfana da shi.
Sauran baki su ma sun tofa albarkacin bakinsu a kan taron. A nasa bangaren, Zaharaddeen Kallah ya nuna farin cikin kasancewa a wurin taron, musamman saboda sha’awa da daliban suka nuna na nazarin Adabin Hausa. Ya kuma ba su shawara da su yi alfahari da harshen Hausa wanda a halin yanzu ya dauki hanyar shahara sosai a fadin duniya. Ya nemi daliban su kasance masu dabi’ar karance-karance da nazarin littattafai, wanda hakan zai taimaka musu matuka, musamman ga wadanda ke da sha’awar zama marubuta.
Dokta Faruk Sarkin Fada kuma ya yaba wa Sashen Hausa na kwalejin saboda wannan abu da suka shirya wanda zai taimaka wa daliban a cikin karatunsu. Ya yi kokarin fahimtar da daliban tasirin rubutu, musamman da aka samu wata daga cikin daliban marubuciya ce. A cewarsa yana da kyau mutum ya yi rubutu ba kawai don abin da zai samu ba, sai don manufarsa a rubutu wanda ilmantarwa da gyara al’umma ke ciki. Ya ce da yawa daga cikin marubuta sai sun bar duniya sannan rubutunsu ke shahara. Ya ba da misali da Muhammad Ikbal daga tsohuwar kasar Indiya da Pakistan wanda rubutunsa ya yi tasiri wajen kawo juyin juya hali a kasar Iran, bayan tsawon lokaci da rasuwarsa. Duk da cewa Ikbal bai taba zuwa Iran ba, rubutunsa da aka fassara ya yi tasiri sosai a can. Wannan ya sa a yanzu har maulidinsa suke gudanarwa saboda jin dadin abin da rubutunsa ya yi. Daga karshe sai Dokta Faruk ya ba da gudunmowar littattafansa guda uku da ya buga da Hausa ga Sashen Hausa na kwalejin.
Taron ya zo karshe da jawabin godiya daga bakin Dokta Mahe Isa Ahmed, wanda ya gode wa Farfesa Yusuf Adamu saboda lokacinsa da ya ba da na amsa gayyatarsu. Ya kuma gode wa sauran marubuta da suka halarci taron, a inda ya nuna aniyar sashen na kulla alaka da kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) reshen Jihar Kano don ciyar da adabi gaba.
Hakika wannan alaka da kwalejin marubuta za su yi farin ciki da ita, musamman don za ta kasance hanya da za a taimaki juna. A bangaren dalibai zai kasance hanyar nazari da horar da su a harkar nazari tare da ganawa da marubuta. A bangaren marubuta da suke bukatar manazarta don rubutunsu ya ci gaba da rayuwa, su ma abin alfahari ne. Tabbas wannan yunkuri abin maraba ne musamman a wannan lokaci da ake neman yin wancakali da koyar da harshen Hausa a makaratun sakandire na kasar nan, wanda haka kan iya kawo barazana ga harshen gaba daya.
Zaharaddeen Ibrahim Kallah, tsohon sakataren kungiyar Marubutan ta Najeriya ne reshen jihar Kano, sannan ma’aikaci a Jami’ar Bayero, Kano. [email protected] <mailto:[email protected]>;