Ganawarmu ta karshe da ‘yata mai tuka jirgin yaki

Mahaifin mace ta farko mai tuka jirgin yaki a Najeriya wacce ta mutu a hatsarin mota a barikin sojin sama da ke Kaduna, Tolulope Arotile ya ce sai da suka yi waya da ita kafin ta rasu. A ranar Laraba, Mista Akintunde Arotile tsohon ma’aikacin Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ya shaida […]

Ganawarmu ta karshe da ‘yata mai tuka jirgin yaki

Marigayiya Tolulope Arotile

Mahaifin mace ta farko mai tuka jirgin yaki a Najeriya wacce ta mutu a hatsarin mota a barikin sojin sama da ke Kaduna, Tolulope Arotile ya ce sai da suka yi waya da ita kafin ta rasu.

A ranar Laraba, Mista Akintunde Arotile tsohon ma’aikacin Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ya shaida wa ‘yan jarida a Lokoja cikin kaduwa cewa ya kira ‘yar tasa a waya sa’o’i hudu kafin rasuwarta.

Ya kuma ce dama tun tana ‘yar karama “ta bambanta da sauran yara. A lokacin ina Kaduna, ta fara karatu tun daga matakin nozire, firamare har zuwa sakandire a makarantar ‘ya’yan sojojin sama na Kaduna kafin ta wuce zuwa Makarantar Horar da Kananan Hafsoshin Soji ta NDA.

‘Babban burinta tun tana karama shi ne tuka jirgin yaki’

“Zan iya wata rana tana aji shida na firamare ta ga wani jirgin sama zai wuce ta ce baba, ka ga wancan jirgin, wata rana zan tuka shi.

“A lokacin ina ganin kuruciya ke damun ta saboda haka sai na ce mata ba komai na kuma yi mata fatan alheri.

“Ta samu gurbin karatu a NDA inda ta karanci Lissafi a matakin Digiri, ko da yake a lokacin ta mayar da hankali wajen tuka jirgin yaki, kafin daga bisani a zabe ta cikin matuka.

“Bayan kammala NDA ne aka tura ta Inugu, kuma ta je kwasa-kwasan karo ilimi kasashe da dama. Babban abin alfaharina shi ne Tolulope ta cimma burinta kafin ta rasu”, inji Mista Akintunde.

‘Maganarmu da ita ta karshe’

Mista Akintunde ya ce ana saura kwana daya da rasuwar Tolulope sun yi waya da misalin 9.00 na dare.

“Ranar Talata na sake kiran ta da misalin 1.00 na rana inda ta ce min za ta shiga cikin sansaninsu don yi fotokofi, sai na ce mata ta yi kokari ta koma gida da wuri saboda tana zaune ne tare da babbar diyata a Kaduna.

“Da misalin karfe 5.30 wani ya kira ni yana tambaya ta ko mun yi waya da Tolu, sai na ce masa ai tana Kaduna.

“Mutumin dai ya dage cewa lallai in kira wayarta, da na kira sai ba a daga ba. Daga baya na kira abokan aikinta sai na ji suna ta kuka.

“Na tambayi daya daga cikinsu me ya same ta, sai aka shaida min cewa an shigar da gawarta dakin ajiyar gawa.

“Na yi matukar mamaki cewa wadda muka yi waya da ita kasa da sa’o’i biyar da suka gabata yanzu a shaida min cewa an kai gawarta dakin ajiyar gawa”, inji mahaifin nata.

Ya kuma ce Rundunar Sojin Saman Najeriya ce za ta sanar da ranar da za a yi bikin binne ta nan gaba.

A ranar Laraba ne dai rundunar ta bakin daraktanta na yada labarai, Ibikunle Daramola ta sanar da rasuwar Tolulope ‘yar kimanin shekaru 23 bayan mota ta take ta a Kaduna.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos