Ganduje ya yi ta’aziyyar mahaifiyar Sheikh Kabiru Gombe
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya yi wa fitaccen mai wa’azin Islama, Sheikh Kabiru Gombe, ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa, Fatima Abdullahi Haruna. Ganduje ya bayyana rasuwar mahaifiyar fitaccen malamin a matsayin babban rashi ga al’uma da jama’ar Jihar Gombe da ma kasa baki daya. #EndSARS: Filato ta yi asarar N75bn a kwana biyu Satar #EndSARS: Dalilin adanar kayan […]
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya yi wa fitaccen mai wa’azin Islama, Sheikh Kabiru Gombe, ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa, Fatima Abdullahi Haruna.
Ganduje ya bayyana rasuwar mahaifiyar fitaccen malamin a matsayin babban rashi ga al’uma da jama’ar Jihar Gombe da ma kasa baki daya.
- #EndSARS: Filato ta yi asarar N75bn a kwana biyu
- Satar #EndSARS: Dalilin adanar kayan abincin gwamnati
- Ganduje ne jagoran yaki da cin hanci a Najeriya —Salihu Tanko Yakasai
Sakon ta’aziyyar da ya aike a ranar Juma’a, ta hannun kakakinsa Abba Anwar, ya bayyana marigayiyar a matsayin uwar al’uma ba iya dan da ta haifa a cikinta ba.
Gwamnan ya ce tarbiyyar da Hajiya Fatima ta ba wa Sheikh Kabiru Gombe tamkar ta ba wa al’uma ne baki daya.
A karshe ya mika ta’aziyyarsa a madadin Gwamnatin Jihar Kano ga Sheikh Kabiru Gombe da Gwamnatin Jihar Gombe da Masarautar Gombe da jama’ar jihar da kasa baki daya.
Ya yi wa marigayiyar addu’ar samun gafara da haske a sabon masaukinta da dukkan Musulman da suka rasa rayukansu.