Ganduje ya bar mana bashin sama da biliyan 500 – Gwamnatin Kano

Gwamnatin ta ce har yanzu tana ci gaba da aikin tattara basukan

Ganduje ya bar mana bashin sama da biliyan 500 – Gwamnatin Kano

Ganduje

Gwamnatin Jihar Kano ta yi zargin cewa tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya bar mata gadon bashi na sama da Naira biliyan 500.

Mataimakin Gwamnan Jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana hakan yayin taron shiyyar Arewa maso Yamma na jam’iyyar NNPP a Kaduna, ranar Juma’a.

Ya ce suna hasashen idan suka kammala tantance yawan bashin, zai iya haura biliyan 500 din, kuma hakan na kawo wa tafiyar da gwamnatin jam’iyyarsu tsaiko a Jihar.

Bayan zayyano tarin ayyukan alherin da ya ce gwamnatinsu ta yi a Jihar a cikin kankanin lokacin da ta yi a kan karagar mulki, ya ba da tabbacin cewa za su ba mara da kunya.

Mataimakin Gwamnan ya kuma ce, “Mun karbi mulkin Kano ba mu tarar da komai ba sai bashi. Da farko bashin biliyan 300 ne, amma yanzu ya fara dosar biliyan 500, kuma har yanzu muna ci gaba da tattarawa. Da zarar mun kammala aikin tattarawar, za mu sanar da ’yan Najeriya, musamman Kanawa ainihin yawan bashin domin su san halin da ake ciki,” in ji shi.

Aminu Abdussalam ya kuma ce duk da tarin kalubalen da suka gada, yanzu haka suna aiki tukuru wajen ganin sun fita kunya ta hanyar tasarrafi da ɗan abin da yake a lalitar gwamnati wajen ayyukan raya kasa.