Ganduje Ya Biya Muhuyi Hakkokinsa Lakadan A Kotu

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya biya tsohon ٍhugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Karbar Korafe-korafe ta jihar, Muhuyi Rimin Gado, hakkokinsa na fiye da Naira miliyan biyar a kotu. Tun da fari dai Muhuyi Rimin Gado ne ya maka gwamnatin Kanon a gaban kotu, yana neman ta biya shi hakkokinsa bayan tube shi […]

Ganduje Ya Biya Muhuyi Hakkokinsa Lakadan A Kotu

Ganduje da Muhuyi

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya biya tsohon ٍhugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Karbar Korafe-korafe ta jihar, Muhuyi Rimin Gado, hakkokinsa na fiye da Naira miliyan biyar a kotu.
Tun da fari dai Muhuyi Rimin Gado ne ya maka gwamnatin Kanon a gaban kotu, yana neman ta biya shi hakkokinsa bayan tube shi da ta yi daga matsayinsa ba bisa ka’ida ba.
A karshe dai kotun ta bai wa gwamnatin umarnin biyan sa hakkokin nasa, tare da tabbatar da shi a matsayin halastaccen shugaban hukumar.

Freedom Radio ta rawaito cewa, gwamnatin lakadan ta biya Muhuyin, kuma har ya fara amfani da su ba tare da bata lokaci ba.

A nasa banagren, Rimin Gado ya ce ba don kudin ya kai gwamnatin kotu ba, sai don tabbatar da doka da oda na aiki a jihar Kano.

“Ni dama ba wai maganar kudin ce matsala ba, a’a an karbi kudi ne daga wajen wadanda ba sa son bayar da hakki.

“Yanzu abubuwan da muke yi da kudin shi ne sayen magunguna da tukwane da za a saya na makabartu, da taimakawa marasa lafiya da ke asibiti,” in ji shi.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan