Ganduje ya bukaci gwamnati ta hana fasa-kwauri

Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kawar da ayyukan fasa-kwauri domin masana’antun kasar nan sun farfado ta yadda tattalin arzikin Najeriya zai inganta.Gwamnan ya yi wannan kira ne a wajen liyafar da gwamnatin jihar ta shirya wa Kakakin Shugaban kasa Malam Garba Shehu a Kano a karshen mako.Dokta Ganduje […]

Ganduje ya bukaci gwamnati ta hana fasa-kwauri
Ganduje ya bukaci gwamnati ta hana fasa-kwauri

Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kawar da ayyukan fasa-kwauri domin masana’antun kasar nan sun farfado ta yadda tattalin arzikin Najeriya zai inganta.
Gwamnan ya yi wannan kira ne a wajen liyafar da gwamnatin jihar ta shirya wa Kakakin Shugaban kasa Malam Garba Shehu a Kano a karshen mako.
Dokta Ganduje ya ce idan aka magance fasa-kwauri a kasar nan, kamfanonin za su farfado tare da samun damar ci gaba da samar da kayayyakin da ake bukata cikin nasara sabanin yadda abin yake a yanzu.
Ya kuma bukaci a inganta samar da wutar lantarki a kasar nan, inda ya ce sai da wadatacciyar wutar lantarki ne kamfanoni za su iya samar da kayan da ake bukata.
 Ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaron iyakokin kasar nan domin dakile ayyukan ’yan fasa-kwauri tare da inganta wutar lantarki idan aka dubi kyawawan manufofinta.
Gwamna Ganduje ya ce gwamnatin jihar tana kokarin samar da wutar lantarki mai karfin megawat 35 ta amfani da madatsun ruwa na Tiga da Chalawa domin wadata jihar da wutar lantarki da bukasa masana’antu da tattalin arzikin al’umma.
Ya ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai yi cikakkiyar kididdiga kan ayyukan Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin baya suka watsar domin gabatar da su kamar aikin fadada noman rani da tituna da hanyoyin zagaye na birnin Kano da tagwayen hanyar Kano zuwa Katsina.
Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne babban bako a wajen liyafar.