Ganduje ya gabatar da N147.9bn a matsayin kasafin kudin 2021
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya gabatarwa da zauren Majalisar Dokokin Jihar da kasafin kudin 2021 da ya kai N147,935,302,948 a ranar talata. Taken kasafin kudin na bana dai shine “Kasafin kudin farfado da tattalin arziki da ayyukan raya kasa”. Ganduje ya ce, “Kasafin kudin yana haska mana irin kudurin da muke da shi […]
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya gabatarwa da zauren Majalisar Dokokin Jihar da kasafin kudin 2021 da ya kai N147,935,302,948 a ranar talata.
Taken kasafin kudin na bana dai shine “Kasafin kudin farfado da tattalin arziki da ayyukan raya kasa”.
Ganduje ya ce, “Kasafin kudin yana haska mana irin kudurin da muke da shi na bullo da sabbin hanyoyin samun kudin shiga a jihar Kano tare da gina sabon harsashi mai karfin gaske da zai yi wa gwamnatinmu jagoranci ta fuskar ci gaba da daga kimar da jihar Kano ke da ita.”
- #EndSARS: Ganduje ya nemi taimakon Rarara da Ali Nuhu
- Diyar Ganduje ta caccaki gwamnati kan zanga-zangar #EndSARS
- An cafke boka zai kwakule idanun jariri a Kano
Gwamnan ya kara da ce wa, dukkan bangarorin da ke da ruwa-da- tsaki da al’amuran da suka shafi tattalin arziki, ilimi da samar da ruwan sha da lafiya da harkokin noma da manyan ayyukan bunkasa birane.
Ganduje ya ce jimullar kudaden shiga da aka samu a wannan shekarar ya yi kasa da wanda aka samu na kasafin kudin shekarar bara wanda ya kai kimanin N604,692,618.
A cikin kasafin dai, an warewa manyan ayyuka N74,661,312,950, wanda wanda ya zarta na shekara bara 2020, da muka ware naira N14,175,781,008.”
Gwamna Ganduje, ya bayar da tabbacin kirkiro sabbin ayyuka da shirye-shirye da zasu bunkasa ci gaban jihar a shekarar mai kamawa.