Ganduje ya sassauta ka’idojin ba da kwangila
Gwamnatin Jihar Kano ta sassauta ka’idojinta na ba da kwangiloli a kokarinta na farfado da matsakaita da kananan kamfanoni daga masassarar COVID-19 a jihar. Babban Sakatare a hukumar cika ka’idoji ta jihar, Adamu Musa ya ce COVID-19 ta illata matsakaita da kananan kamfanoni wadanda su ne kashin bayan bunkasar tattalin arzikin Najeriya. A taron da […]
Gwamnatin Jihar Kano ta sassauta ka’idojinta na ba da kwangiloli a kokarinta na farfado da matsakaita da kananan kamfanoni daga masassarar COVID-19 a jihar.
Babban Sakatare a hukumar cika ka’idoji ta jihar, Adamu Musa ya ce COVID-19 ta illata matsakaita da kananan kamfanoni wadanda su ne kashin bayan bunkasar tattalin arzikin Najeriya.
A taron da aka shirya domin fahimtar da su hanyoyin samun ayyuka daga gwamnatin jihar, jami’in ya ce “Muna so ne su fahimci yadda za su samu kwangiloli shi ya sa aka sassauta ka’idojin.
“Horaswar za ta kara musu fahimta da kwarewa kan yadda za su ci moriyar sassaucin wajen samun kwangiloli”, inji shi, yana mai bayyana muhimmancin taimaka musu domin su farfado.
A jawabinsa, Kwamishinan Ciniki na jihar, Ibrahim Mukhtar, ya ce an shirya taron ne domin kara wa matsakaita da kananan ‘yan kwangila fahimtar komai kan yadda za su nemi kwangiloli su kuma samu daga gwamantin jihar ba tare da matsala ba.