Ganduje ya sauke kwamishinoninsa biyar
Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya sauke biyar daga cikin kwamishinoninsa a yayin da ya rantsar da shida sababbi. Kwamishonin da gwamnan ya sauke suna hada da Haruna Muhammad Falali, wanda ya rike ma’akatar sharia, da Ahmed Rabi’u wanda ya rike ma’aikatar ciniki da Hajiya Zubaida Damakka Abubakar da ta rike ma’aikatar tsari […]

Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya sauke biyar daga cikin kwamishinoninsa a yayin da ya rantsar da shida sababbi.
Kwamishonin da gwamnan ya sauke suna hada da Haruna Muhammad Falali, wanda ya rike ma’akatar sharia, da Ahmed Rabi’u wanda ya rike ma’aikatar ciniki da Hajiya Zubaida Damakka Abubakar da ta rike ma’aikatar tsari da kasafin kudi da Injiniya Shehu Haruna Lambu wanda ya rike ma’aikatar ayyuka da kuma Farfesa Kabiru Isa Dandago wanda ya rike ma’aikatar kudi.
Sababbin kwamishinonin da gwamnan ya nada sun hada da Bairsta Ibrahim Mukhtar wanda ake sa ran zai rike ma’aikatar shari’a da Injiniya Aminu Aliyu wanda ake sa ran zai jagoranci ma’aikatar ayyuka da gidaje da kuma sufuri, sai Alhaji Aminu Mukhtar Dan Amu wanda ake sa ran zai rike ma’aikatar kudi sai Ahmed Rabi’u na ma’aikatar ciniki da Musa Iliyasu Kwankwaso wanda ake sa ran zai rike mukamin mai taimakawa gwamnan na musamman sai Hajiya Aishatu Jafar Yusuf wacce ake sa ran za ta jagoranci ma’aikatar tsari da kasafin kudi.