Ganduje ya taya Tinubu murna

Tinubu zai yi aiki tukuru wajen ganin ya shawo kan matsaloli da kasar ke fuskanta.

Ganduje ya taya Tinubu murna

Tinubu da Ganduje

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kwatanta zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu a matsayin dan kishin dimokuradiyya.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne yayin taya Tinubu murnar lashe zaben Shugaban Kasa da ya yi a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

A cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaru ga gwamnan, Abba Anwar ya fitar, Ganduje ya yaba da irin jajircewar Tinubu da kuma na sauran mutane da suka tsaya wajen ganin sun cimma nasara.

“Bola Ahmed Tinubu jajirtaccen mutum ne da ke son ci gaban kasa da kuma al’umma saboda irin ayyuka da ya yi a fadin kasa,” in ji Gwamnan.

Ganduje ya ce jajircewar da Tinubu ya yi na tsawon shekaru wajen ganin tabbatuwar dimokuradiyya a Najeriya, shi ya sa suka ga ya dace ya mulki kasar nan.

Ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa zababben shugaban kasar zai yi aiki tukuru wajen ganin ya shawo kan matsaloli da kasar ke fuskanta.

Gwamna Ganduje ya gode wa mambobin jam’iyyarsu da kuma dukkan wadanda suka jajirce wajen samun nasararsu.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya